EPISODE THIRTY NINE&FOURTHY

211 22 2
                                    

EPISODE:39&40

"Waye ku kuma wa ya saka ku biyo mu a baya har inda muka zo"?tambayar da Agneta ta aikowa ɗaya daga cikin matan nan kenan wacce sanadiyar faɗuwar su ƙasa mayanin fuskar ta ya ɗaga..
  Kasa bata amsa suka yi sai suka yunƙura suka taso a take faɗa ya kaure wurin sai dambe ake ta yi wanda ya saka su yada makaman yaƙin ma gabaɗaya suka shiga yi da hannuwan su da jikin su,faɗa sosai suka yi kasamcewar four against two ne sai suka rinjayi mata biyun suka yi faɗa da su sosai sai da abin ya kai masu yadda suke so sannan suka tsagaita ba dan an kai matakin tsagaitawar ba..

  Cikin zafin nama Juda ta tambaye su babu alamar wasa ko shirme cikin batun ta
"Mun san juna yanzu kuma alamu sun nuna min da manufa kuka dumfari masarautar nan dan haka muna sauraron ku ku yj gaggawar fallasa dalilin ku tun kafin rai na bai ɓaci ba in kasa dakatar da kai na daga aiwatar da abin da zuciya ta ke kwaɗaiyin aikatawa"duk sun gaji tsabar ɗaukar abin da suka yi da zafi da yadda suka ci da zuci wun yaƙin.
  Kamar dai ba zasu furta kai ba sai daga baya suka amsa maganar wacce ɗaya daga cikin su ne ta bada amsar kamar haka
  "Ni sunana Callee kamar yadda kuka gan mu mu biyu ne tare da abokiyar tafiya ta kuma ba wani abin ya kawo mu nan ba sai son cikar burikan mu biyu wanda muka gano muna buƙatar wani littafi kafin komai ya wakana,ko da muka taho nan bamu da masaniya akan komai amma mun san ba zamu koma gida haka ba sai da wannan abin da muka fito nema".
Kallon ta suka yi sai suka kuma kallon ɗayar haɗe da yi mata alamar ke kuma fah dan haka itama ta gabatar da kan ta
"Sunana Fianna kuma aiko ni aka yi sakamakon kasa aiwatar da aikin da sarkin ƙasa ta ya sa ayi aka dawo mai da sakamako mararar gamsarwa dan haka aka buƙace ni da in cika wannan ragowar aikin kuma kamar yadda abokiyar tafiya ta ta faɗi,a hanya muka haɗu kuma bamu taɓa mafarkin zamu haɗu da ku ba hasalima abin da ya kawo mu nan muka zo aiwatarwa sai dai hakan bai samu ba,yau kimanin kwanakin mu huɗu kenan muna zuwa da komawa akan rashin nasarar da muke samu dan a duk lokacin da muka zo nan masarautar haka muke komawa babu nasara sakamakon mugun baƙin dafin asirin da mamallakin masarautar ya sa aka mai wanda in ba ƴan cikin masarautar bane toh babu mai shiga cikin dare wannan dalili ya sa muka daidaici lokacin da muka ga zuwan ku a tunanin mu ku ɗin ƴan cikin gidan ne dan muyi amfani da ku wurin shiga gidan sai dai muka ga akasin haka kuma da kuka gan mu muka yaƙe ku dan kar ku shaida mu amma bamu san abin zai zamo haka ba".
Kallon mamaki suka bi ta da shi kenan in nutshell suma dai mayaƙa ne kamar su sai dai kowa da abin da ya fitar da shi daga masarautar sa..
  Wani idea ne ya zo wa Berenice akan me zai hana su masu wayo exactly yadda suka wa Agneta a haɗuwar su ta fari in ya so bayan sun yi nasarar fiddo ƙanwae Juda sai su rabu da su ita a nata ganin hakan zai yi sosai..  
  Kafin wata ta furta wani abu cikin su Judan sai Berenice tayi karaf ta riƙo hannun Juda ta fara jan ta wanda abim ya zo mata cikin shammaci..
  Sai da auka yi ɗan nesa da su sannan ta rage muryar ta ƙasa ta fara magana
  "Juda ni gani nake kamar mutanin nan biyu Callee da Fianna wannan kundin suka fito nema kuma ko basu sanar da mu ƙasar su ba na san abin da ya kawo su kenan dan haka ni a tunani na me zai hana mu janyo su jiki tun kafin su gano cewa kundin nan na tare da mu su yaƙe mu ba tare da mun ribatu da komai ba mu nuna masu cewa muma abu ne ya fiddo mu daga ƙasashen mu daban daban kuma muna son komawa gida cikin farinciki da jin daɗi dan haka su haɗa hannu da mu mu taimaki junan mu dan samin komai cikin sauƙi kamar dai yadda muka wa Agneta a haɗuwar mu ta fari da ita,ya kika gani ke a naki tunanin"?tambayar tayi tana kallon idanun Juda dake rufe cikin mask ɗin nan..
  Sosai Juda tayi na'am da shawarar Berenice ko ba komai Berenice ta koyi dabarar ta dan haka sai kawai ta rungune Berenice tana ɗan bubbuga bayan ta tana faɗin
  "Kin kawo shawarar da na kasa kawowa kuma kin birge ni ba kaɗan ba  kuma hakan za'a yi amma Balik kaɗai za'a yi revealing ma sirrin banda Agneta ko"?da sigar zolaya tayi tambayar wanda ya saka Berenice darawa kaɗan dan ta san zolayar ta Juda ke yi..
  "Oh come on ai mun zamo ɗaya mu da Agneta komai ma ana iya sako ta ciki"!murmushi suka yi sannan suka koma can inda suka baro su Agneta da Balik haɗe da sauran mata biyun..
  Balik Berenice ta jawo yayin da Juda ta ja Agneta gefe suka mayar masu da shirin da suka yi dan ƙaruwa da su Callee da Fianna..
  Duk sun yi na'am da tsarin sai dai shakkar su kar su gano gaskiya su zo su guje su sai dai Juda da Berenice sun yi ƙoƙarin fahimtar da su..
Komawa suka yi Balik ya jagoranci zance ta hanyar yi masu bayanin abin dake tafe da su dan haɗa hannu su sami abin da suke so..
  Bayani sosai Balik ya ɗau lokaci yana masu amma sai da suka so janyewa kafin su yarda akan zasu haɗa kai da su.
  "Sharaɗin mu kar abin nan ya tafi ba bisa tsarin da kuka zo da shi ba dan in hakan ya faru toh ba zamu maku ƙarya ba sai mun raba ku da kawunan ku wannan ajiyayyen zance ne kun yarda"!!gyaɗa kai suka yi kafin duk su koma gefe dan sanin abin yi..
  Agneta ce ta fara magana dangane da shirin da ya kamata su fara yi akan tunkarar wannan masarauta
  "Ni a gani na me zai hana mu samo wanda ya san kan sihiri a cikin garin nan wanda zai iya bamu sirrin sihirin masarautar nan dan dai ba za'a ce babu wanda ya san sirrin masarautar nan ba dangane da irin tsaface sa da aka yi ba sai dai in bamu nema ba, dan haka ni a nawa tunanin kafin mu samowa kan mu mafita game da sihirin da aka wa masarautar nan dole sai mun samo wanda ya ƙware a fannin sihiri dan ya taimaka mana in ba haka ba bana jin abin nan zai mana sauƙi ya kuka gani"?ta juyo tana kallon su ɗaya bayan ɗaya sai Fianna ta karɓe zancen da
  "Ni tun kafin in zo sarkin da ya aiko ni ya shaida min cewa an tsaface masarautar kuma da mugun tsafi dan haka zai ba ni sirrin warware tsafin amma in tabbatar ni kaɗai nayi amfani da wannan sirrin dan in ba haka nayi ba toh lallai shirin mu da shi zai lalace toh ni dai ina da sirri ɗaya da zan iya shigar masarautar nan da shi sai dai ban sani ba ko zamu iya amfani da wata hanyar dan ganin dukkan mu mun shiga".
  Girgiza kai Juda tayi dan ta gama nazarin zantukar su kaf kuma ta gano kamar shawarar Agneta ne yafi dacewa da halin da suke ciki yanzu da haka dan  haka sai ta ɗan rage murya tana faɗin
  "Shawarar Agneta ya fi dacewa da yanayin nan da muke ciki dan samo mafi sanin kan sihiri shine zai kawo mana sauƙin lamarin nan amma me kuka gani"?amsa Balik ya bayar da
  "Eh mun amince sai dai shawarar Fianna ma na kan hanya me zai hana in mun samo mai sanin sirrin sihirin daga baya mu ɗabbaƙa shawarar Fianna duk da ma ita kaɗai ce ke da ikon amfana da sirrin amma dole za'a sami hanyar da zamu iya amfana da shi".jinjina kai suka yi baki ɗayan su cikin amincewa da shawarar ta Balik a ƙarshe dai sun yanke shawarar komawa masaukin su Juda na jiya dan su yada zango har zuwa washegari in yaso sai su bazama cikin gari dan nemar masanin wannan sihirin.

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now