5&6

90 8 0
                                    


*Gaskiya fans inajin Dadi comments din ko da kuma fatan alkairin na ku*

*Wannan shafin na kune masoya wannan littafin nawa inayinku over over*

Kokarin tashi Jummai take, sai kawai tayi an naushi bakinta dagefan baki da idanta, ihu tasa wayyo Allah takashe ni wlh. 
Indo da Ramatu najin uwarsu tayi wannna ihu sukayo kan Bakuwa, dan rufeta duka, ita dai Indo taga hannu ya gefta amma batasan ina yadaka ba ita dai kawai taga tafadi kuma taji naushi amma bata shaidaba. Itako Ramatu mari hudu tasha ta zube kasa tana ihu azaba,mlm da yaga bakuwa zatayi kisa yasa tashi dan raba fada, sai dai me Jummai ce ta dago inda yaga gefan ido ya kunbara kumatu yayi wani kullutu ga labba sun kunbara kamar ganda dariya ce taso subuce shi amma ya baze wani mugun muni tayi kamar goggon biri. Magana tafara Allah ya isa azzaluma aita na fadar haka akaga mlm na shika dariya harda rike ciki. Ramatu ta dago kanta hannu dafe da kumatu dan daga me  mijin babarta ke wa dariya. Ai ita ma tana gani tafara dariya harda tuntsurawa. Rai abaci Jummai tace ke uban mekikewa dariya?

Wlh Inna bakin ne ya koma kamar na agwagwa idan kina magana,wata dariya takara shekewa, shiko mlm cewa yayi ni naga kamar yafe kamada shantu ko,ai yana fada Ramatu tace wlh baba kamar gandar  Tanko, habawa sai wata dariya kamar sun zare.

Wani bakin ciki ne yadaki Jummai tare da mikewa amma ina takasa ashe bakuwa ce riketa.

A masiface ta kalleta, amma da tatuna da  koriyar sanbada da Ja tuni ja bakinta tayi gum. Karuwa dan sake ni inje bayan gida fitsari nakeji. Idanu bakuwa takara zuba mata irin zakici ubanki yau.

Hannu bakuwa zata zange Jummai, mlm ya maza yariko hannu ta yana rarrashinta, tuni bakuwa tasaki Jummai tare da rungume mlm tana wasa gefan rigarsa.

Ai Jummai na gani bakuwa tasaki ta tamaza ta tashi tashige daki a million tare da banke kofa. Allah ya isa na muguwa. Kai kuma zamu hadune in kazo rokan na baka . tsaki yaja tare da cewa bude kofa bakuwa tashigo ta kwanta. Wa wlh sai dai kasan yadda zakayi da ita amma ba dakin Jummai ba.

Rokanta yayi tayi amma taki dan haka yajata dakinsa.

Tom kwanciyar mlm da bakuwa.

Ai fa mlm ana kwanciya kan tabarma, Bakuwa ta kwanta gefan sa, jim kadan da addu'a  bacci ya tufa masu kawai yaji bakuwa ta haye jikinsa,mlm najin shock me kon yace Subahanalallah sai cewa yayi Masha Allah Masha Allah Masha Allah shi adole Subahanalallah yake cewa sai gumi yake yaji tattausar farar fata mai hade da kamshi ga gashi yarofe fuskarsa ga dukiyar fulani a tsaye suna be Taba kirjinsa ai mlm su Masha Allah ake fada kawai, karfin ahali akayi tare da janyeta daka jikinsa, inda ya dakko yar kanwa yajika saboda tsaro.

Da safe tana bacci ya tafi massalaci yake shadawa me gari akwai matsala nan fayyace masa komai. Me gari na zari aka hauyi sannan yace,ankya ba kuwa Auranta zakayi ba kuwa,sai dai ina kuma gudun samun matsala karko tana da miji azo dangi su zo nemanta, shiru duk akayi sannan daya daga mutanan sarki gaskiya ni banga alamar tana da miji ba saboda duk yadda akayi ko me kudi ce akesan kashe ta. Nan fa akafara bin zancen Hudu. Nan da nan aka daura be Auran mlm Kabeeru Dashe da kuma bakuwa wadda taci Suna Fateema   Bako wato me gari. Akan sadaki dubu 4500 .

Tom mutane sunyi Mamaki inda lbr ya shiga kunnen Jummai ina bazai Aure aljana karuwa ba sai zage zage take kamar mahaukaciya. Inda mutane ke shugowa kallon Amarya bakuwa sai dai kaji ana cewa babu me kyanta duk garin ba ataba ganin me kenta ba, sai da me gari yayi musu tatas sannan suka hakura aka daina maganar.

Mlm tunda akayi sabuwar Amarya ya tura yaro ayanka zabgegiyar tinkiya,  a garken sa dake gidan Goma.

Takaitattan lbr kan Mlm Kabeeru.

Mlm Kabeeru ba fulatani shi iyayan mulanin tashi ne inda suka zo garin dashe dake Zamfara State, sai basu dade anan ba wata Annoba ta barke agarin inda dangi sa duk suka mutu sai shi da kakansa yana yaro dan shekara goma.  Yasamu dukiya mai yawa sosai ta Dabbobi da kuma gonaki masuyawa. Hakane kakansa ya mutu yana shekara ashirin. Nan komai yayi masa zafi yafara rayuwar kadaici nan me gari ya bashi shawara yayi aure saboda me gari abokinsa ne kuma sa'a ni .

Babu musu yafara neman yari kaddara da tsautayi yasa Jummai ta kyalla idanta akansa nan fa tashiga tafita takaso Auranta tafito da yara mata Indo da Ramatu nan tashanye mlm Kabeeru ya aure ta. Nan kaddara tafara samunsa ,a  haka ne sukai tsawan shekara goma babu haihuwa ita Jummai bata da mu gashi taki vari yakara aure sai akan bakuwa.

Cigaban lbr

Tinkiya nan gegiya aka yanka a gidan Goma tare da farfesu, akayi tare da hado ruwan randa mai sanyi, aka kawo Jummai na daki yashige dasu sai ashar take ita kadai. Mlm Kabeeru aka zage ana lallaba Amarya ana bata abaki saboda kar asamu matsala sai da sukaci suka shi akayi alwala akayi sallah.

Tom mlm akabari dare yatsala kafara kwasar gara, wanda mlm ya kwana ya na sunbatu yana kyau tutuka da gunarsa   kamar bayaso, sai dai yayi Mamaki da yajita ba budurwar ba duk da cewa komai nata akame amma sai yayi tuanani ko bata dade da aure ba ya mutu mlm har makara akayi sallar asuba.

Da safe suna fitowa  Fateema na binsa rike da hannusa aka aiko da yaro da kaya wajan kala goma na Fateema wanda zata dinga sawa ana shan amarci. Da ashar Jummai ta fito yanzo mlm bako kunkya katoshe mu ya harda be sun batu kamar mahaukaci. Harara yazo ba mata anyi asara anawa mutane labe, kuma in anyi zuciya agyara makwanci aji sunbatu. Baki bude take kallonsa tab tayi sake mlm ko shakkarta baiyi ba dole boka na kwari sake sabon shiri.

Sati daya da shan Amarci  Fateema Shalele akafara aman huya alama an dauka, nan fa mlm yafara murna tare da kaita wajan abokinsa me magani dan kamar maye haka yake yana ksllon mutum zaice cikine wata kaza da kwana kaza. Haka kayi yana kallonta yace cikin wata biyu ne da ita da kwana biyu. mlm ne yazabura me kake cewa kara mai-maita masa yayi,kana nufin cikin bana wane ba kenan,? Tabbas hakane.

Ke nan mijinta ne yasaketa da ciki kenan ko kuma. Baikarasa ba abokinsa yace kaga daka ni sai kai muka sani dan haka kana cika magana za iya ballowa kawai kabarshi amatsayin danka karka gayawa kowa. Tom yace tare da dawo gida inda yatar da Jummai bata nan ,nan yayyi tatunani har  ya gamsu da maganar abokinsa..

Wajan Jummai ta na zaune gaban boka dan ko Marka bata biyawa ba tataho ya shida mata Fateema na da ciki. Nan fa ta dinga ihu harda birgima ita ina bazata yarda ba sai anzubar.

Ya gayamata abinda bazaiyuba dan yagani cewa   cikin alheri atare da cikin kuma yun kurin zubarwa tashin hankali ko Rasa rai nan ya fafataki Jummai ta na kawo masa hauka....

Tom fa

MOHANNAD MEHEKK Where stories live. Discover now