😭HINDU😭 page 14

6 0 0
                                    

😭
     HINDU
                 😭



      ✍🏻
            By
                *Tooraee*
                                  🥰🥰🥰.


          Page 14




"Hakane Kam,Allah yasa ta aure ka?"

"Ameen dai"


Hydar Hud na hango da Haris suna Hira....

"Hydar Hud kace Wai akwai ban bancin wayewa tsakanin Hauwa da Hibba?"

"Eh Akwai,Hauwa wayewar ta na ilimi da boko ne, ita Kuma sis Hibba waye watar na boko da iskanci ne"

"Eyyah Hibba na ban tausayi wlhy"

"Nima haka,Dan rayuwar da takeyi bana so,dama Hafeez ya aure ta"

"Cab,ai shi ba ita bace a gabanshi Hindu ce."

"Hindu fa,wacce Hindu?, badai Hindu takaba?"

"Ita"

"Cab,Bazai yuwuba,Basu San halinshi bane?"

"Sun sani"

"Toh Allah ya kyauta"

"Ameen dai"


Weshegari da sassafe taga Kiran Hafsat,Hindu jiki narawa ta daga,Dan tun jiya da bata ganta ba take kiranta Amma Bata daga ba,sai yanzu take kiranta.........

"Assalamualaikum"

"Wa'alaikumuslam"

"Hafsat lfy jiya Ina kiranki Baki dauka ba?"

"Jikin Umma ne ya tashi,sai da mukaje Asibiti,Ni Kuma na manta da wayana a gida,sai yanzu da aka sallamo mu tukunna,shine nazo Naga missed calls dayawa"

"Eh hakane,Dan saida nasa Haris yazo gidanku yaduba Koh lfy?,shine yace mun Wai gidan Ku a kulle yake,shine ya kamo hanya"

"Eyyah Allah sarki Dr. Haris,wlhy yanada kirki Hindu,Dan munyi waya dashi Dana dawo daga skull Akan zaizo ya daukeni mutaho"

"Ai shine yaketa kiranki,yace kun shiryane?,da Baki dauka bane shine ya Kira Ni"

"Eyyah,Ai hawan jininta ne yatashi,Kuma Alhamdulillah ta Samu sauki"

"Ok,Allah yabata lfy, insha'allah yau zamu dawo,Ina dawo zanzo"

"Ok,Allah ya tsare,ya taron?"

"Alhamdulillah"

"Masha Allah,sai kundawo din"

"Ok insha'allah"

Tana Gama waya,suka fara shiri Dan Hubby yace bazasuyi yamma ba,Kuma su kadai zasu koma shiya dawo Office bazai bisu ba.......

Haka suka Kama hanya Hauwa, Huzaifa da Hindu a mota daya,Habib ya tuk'a su Hajjo da Humaid,Dan Hubby yace baza'a tafin Mai  da driver ba,da yike Yana da wasu motocin acan.......

Tun suna hanya Hindu tabasu lbrn jikin Umma su Hafsat yatashi....

"Eyyah Allah sarki,kice abunda ya hanata zuwa kenan?"

"Eh wlhy"

"Allah yabata lfy?"

"Ameen"

"Ya Huzaifa mubiya Mana tuna akan hanya ne sai mu gaishe da Umma"

"Eh hakane Yana da kyau"

"Yauwa Aiko na gode"

"Haba Hindu,ai Koh aure kikayi Dole in Abu yasamu Hafsat muje mu dubata,ai an zama Daya"

Dadi ne yakama Hindu,Dan tana matuk'ar son Hafsat da iyalan gidansu......

Bayan sun shigo KADUNA nane suka wuce gidan su Hafsat suka duba jikin umman su,daganan suka wuce gida.....

Hafeez ba ranan yadawo ba Saida ana gobe Hauwa zata hada Dinner tukun na yadawo....

*Ranar Dinner*

Dakyar Hindu taje, Dan batasan abunda zai sa ta hadu da Hafeez,Shima Haris ne yace sai taje Dan Hydar Hud ma yabiyo Haris KADUNA........

Hindu ce taga abun mamaki,yadda taga course mates dinta sunzo,hadda wa yanda ba department dinsu Daya ba.....

*Ai kungane irin gayyan 😅😅😅gayata*

"Hafsat Wai waya Gaya ma Yan skull muna da taro"

"Waye Bai sani ba,Abu na social media yanzu,saidai kice waya gayyace su"

"Toh,Waya gayyace su?"

"Ni,Hauwa ce ta Kirani tace in Mata gayyan Yan Kasu"

"Na shiga uku da Hauwa"

"Bawani malama,mutun fa Rahma ne,kyaleta hafsat kunmun daidai"

"Ai Hauwa na burgeni"

"Ai Ni ban ganin laifin ta, Koh kadan"

"Amma kasan wani Abu Dr. Haris?,nifa da ban son hauwa, gani nake batada kunya"

"A'ah wlhy Baki fahimce tabane tana da fadan gaskiya ne kawai"

"Ai Nima Naga hakan"

Tunda a kafara dinner around 8:00pm,9:00pm nayi Yan Kasu sukace zasu tafi,Aiko sunga Abu buwa awurin Hauwa,sunci sunsha hadda takeaway ta Basu,ga gifts din data loda musu,sukoh Yan gida ba su sukabar wurin ba sai 10:00pm Daman Hubby bayanan,kunga Koh Sai abunda ya turewa buzu nadiiii......

*Bayan 1 week*

Kowa ya watse a gidan,Hauwa ta koma skull Ankara University *Turkey*,shi Kuma ya huzaifa ya koma U.S.A shida Hamma,Daman a wuri Daya suke aiki,shi Kuma Habib Yana yin 2nd degree dinshi a Standford University *U.S.A*.

So gida ya rage daga Hindu, Hajjo, Humaid sai Hafeez......

Hajjo Kuma shirye shirye take zata je wurin Hubby a Abuja,Daman ta kanje wurin shi,wani lokacin ma sai ta share wata uku zuwa hudu Bata dawo ba......

Bayan kowa ya watsene hadda Hajjo,Daga ita sai Humaid,Dan Haris ma yakoma......

Wani Abune Hindu tashiga tashin hankali dashi,yau watanta biyu kenan bataga Al'adan taba,Kuma gashi wani Abu da Bata dashi da, yanzun ya ziyarce ta....... *kwad'ayi*.

Hakalinta a tashe takira Hafsat  a waya,

"Hafsat pls muhadu a skull Dan Allah"

"Lfy?"

"Lfy kalau,Amma mu hadu yanzu"

"Ok,ganinan zuwa...."

Batare da Bata wani lokaci suka iso atare,

"Hafsat Ina cikin matsala"

"Wanne irin matsala....✍🏻✍🏻?"

*Wayyo ya k'are😥,Hindu Mai yasa kikayi shuru?*



    
       By *Tooaraee* 🥰🥰🥰.

😭 HINDU 😭Where stories live. Discover now