😭
HINDU
😭✍🏻
By
*Tooraee*
🥰🥰🥰.
Page 17Tashi yayi yatafi skull,Yana zuwa ya ganta ita kadai a karkashin biyashiya,Dan Hafsat tana fushi da ita.....
Saukowa yayi daga mota yazo inda take
"Hindu Zo muje mota zamuyi magana"
"Ok,jeka Ina zuwa"
Hafsat na tsaye a kofar class ta hangosu,gyara tsayuwa tayi Dan taga ikon Allah.....
Bayan Hafeez ya wucene da Yan mintuna sai Hindu ta bishi,tana shiga motar ya tada motar yabar makarantar.....
"Hindu za muje ne a zubar da cikinnan"
"Ni bazan zubar ba"
"Toh ya zakiyi dashi?"
"Duk yadda Allah yayi dashi"
"Kamarya😠?"
"Na dauki cikinnan kaddarata ce kamar yadda Haris yake Gaya mun kullun"
"Shi Haris dinne yace karki zubar da cikin?"
"A'ah Baima sani ba"
"Toh Hindu Bari kiji,Wlhy karya yake fada,bawanda zai aureki da Ciki,Koh Ni Dana Miki cikin wlhy bazan aureki da Ciki ba,in Kinga na aureki toh wlhy sai kin zubar da cikinnan"
Nikaf dinta tad'aga,sannan tace Mai
"Ya Hafeez Daman nace maka ka aureni ne😠?"
"Toh waye zai aureki bayan ke ba virgin bace?"
"Oh Daman kayi hakanne saboda bawanda zai dauki ragowan wani Koh?,Toh wlhy kayi kuskure Ya Hafeez,Toh Bari kaji......
Ni Hindu bazan zubar da ciki ba....
Kuma Wlhy bazan aure kaba..."
Dariyan takaici yayi, sannan yace
"Kina tunanin Haris zai aureki ne?,Toh wlhy Koh ya aureki ya tabbatar keh ba Virgin bace bazai zauna dake ba"
"Ai Ni bance maka Haris lallai zan aura ba,Amma wlhy bazan taba auranka ba,mugu kawai"
Bude motar tayi tafita abunta,tahau mota ta koma skull,Tana zuwa taga Hafsat tana zaune a inda ta Tashi,zuwa tayi tasame ta....
"Assalamualaikum"
"Wa'alaikumuslam"
"Hafsat fushi kike Dani?"
"A'ah,an zubar da cikinnan?"
"A'ah bazan zubar ba nace"
"Ok shikenan,Amma ki sani Wlhy Hindu, kinsan Hafeez Alkaline Koh?,zai iya karyatawa yace bashi ya Miki cikinnan bakoh?gawamma a je azubar sai ki auri Hafeez"
"Hafsat wlhy bazan auri ya Hafeez ba"
"Toh fa,in Baki aureshi ba, waye zai rufa Miki asiri?"
"Allah,Koh kin manta dashine?"
"A'ah,Amma ai bashi zai sauko daga samaba yazo ya rufa Miki asiri ba Koh?"
"Eh nasani,ai shine yace duk runtsi duk wahala Yana tare damu,Kuma yace idan ya jarabce mu bawai Dan Baya sanmu bane..."
"Eh hakane,Allah ya shige Mana gaba"
"Ameen,yauwa Hafsat Dan Allah kidaina fushi dani kinji?"
"Ok babu damuwa Hindu,bazan iya rabuwa dake ba......."
Wayan Hindu ne yadauki Kara
"Kinsan waye?"
"A'ah"
"Dr. Haris ne"
"Allah sarki, bawan Allah"
"Toh daga Mana"
"Ai ya tsinke Bari ya Kara Kira"
Sake Kira yayi,dagawa tayi cikin natsuwa
"Assalamualaikum"
"Wa'alaikumuslam"
"Ykk?"
"Lfy Lau"
"Hindu nakirane in Miki ALBISHIR"
"Ok inaji?"
"Yanzu muka rabu da Daddy na a Istanbul,yazo wani meeting shine muka had'u"
"Ok"
"Shine namai maganar ki,sai yace mun yaushe zan dawo Nigeria?"
"Oh,ka kusa dawowa ne?"
"A'ah Amma Nan da 4 months insha'allah"
"Ai Koh kakusa,"
"Ammafa Banda wannan month din Zaki kirga"
"Ah haba,sai kace mun 5 months kawai"
"Ok 5 months,shine yace za'a turo gidanku asa Mana Rana....."
Hawayene 😭😭suka zubo Mata daga idanuwan ta...
"Allah ya kaimu"
"Naga kamar bakya farinciki ne?"
"A'ah kunya ne yakama"
"Ok nagane,bye Bari zanshiga class,Daman nakirane Dan ingaya Miki ALBISHIR"
"Ok Thank nagode"
"Ok,Allah yamiki Albarka 🤲🏻"
"Ameen nagode"
Kashe wayar tayi tafashe dakuka😭,ta rungume Hafsat.
"Hafsat nashiga uku😭,kinsan sanda Haris zai dawo cikina Yana 7 months kenan"
"Hmmmmm,toh me kike son in Miki?"
"Addu'a"
"Ok, insha'allah"
"Amma Hafsat Ina son Haris"
"Toh ya kike son muyi?"
"Nasan na rasa Haris,Dan bazan iya cutar da Haris ba"
"Nima hakan nake gani,Dan Koh kin zubar da cikinnan bazaki auri Haris ba,Dan Haris mutumin kirkine Bai kamata a Mai hakan ba...."
"Gaskiya ne,bare ni Hafsat bak'aramin yarda Haris yayi Dani ba"
"Hakane Hindu,mutane dayawa sun yarda da,
natsuwar ki,
kimar ki,
hakalin ki,
tarbiyar ki,
hangan nesan ki,Amma keh Zaki rusashi da hannunki Kuma acikin mutuna kalilan"
"Mintuna fa kikace?"
"Eh,Dan har yanzu bawanda yasan kina da juna biyu"
"Eh nasani,Amma ai Allah ya yarda da Ibadata Koh?"
"Wannan ban sani ba,tunda bani ke amsa ba.....✍🏻✍🏻"
*Huuuu huuuu 💃🏼💃🏼💃🏼 yanzu aka fara Hindu my fans,kucigaba da su burbudo mun comments Dan shine ke karamin karfin gwuwan typing💕💞💕........✍🏻✍🏻*
By *Tooaraee* 🥰🥰🥰.
YOU ARE READING
😭 HINDU 😭
Contolabarin wata yarinya ce da tsautsayi ya abkamata,Kuma tadaukeshi a kaddaranta....