😭 HINDU 😭 page 25

7 0 0
                                    

😭
      HINDU
                  😭



    ✍🏻
         By
             *Tooraee*
                                🥰🥰🥰.




         Page  25




Hafsat ce tawuce da Hindu gidansu,kowa na gidan ya tausaya Mata,Kuma Umma ta dauki alkawarin riketa har lokacin dazata haihu,Dan umma tayi tayi da ita Amma Taki gayamata wayamata ciki🤰🏻...

Abun mamaki Ranan da Hindu tafara kwana agidansu Hafsat ranar ne barayi suka shiga gidan suka musu sata.....

Abunda Bai taba faruwa a Layinba bare Kuma gidansu,suka wayi gari da jimamin abunda barayin suka musu,Amma bawanda yace wani Abu....

"Hafsat Dan Allah Zaki rakani banki incire kudi....?"

"Ok Muje,Umma ma zasu Asibiti ita da Hassana zasu amso magani,"

"Ok mutafi da Hussaina Mana kawai"

"Toh badamuwa"

Haka Koh akayi suka fita suka kulle gidan babu kowa,suna zuwa Hindu ta cire kudi a account dinta Aiko nan take Hubby yaji Alert....

Murmushi😊 yayi yace

"Ai inkinsan wata bakisan wata ba......"

Kafin sudawone suka samu gidansu Hafsat ya k'one kurmus....

Ashe Hassana ce tabar cooker a kunne,Amma mak'ota suka zuga Umma,Wai tsinuwar Hindu ce da ubanta yamata yake binsu,saboda haka ta sallameta...

Aikoh haka akayi suna dawowa Umma tace tabar Mata gida....

"Umma ba laifinta bane,kaddaran muce hakan"

"Kimun shuru,nidai bazata bini ba"

"Umma kiyi Hakuri,nagode zantafi Allah yasaka da Alheri,ubana ma ya gujeni, Dan kin gujeni ai Babu wani matsala........"

"Umma Dan Allah karkiyi haka ba Hindu bace Dan Allah"

"Wlhy saidai kibita bazan zauna da itaba kwana Daya bala'i biyu, wlhy a'ah"

"Hafsat karki damu nagode Miki da duk irin kulawar da Kika nuna min,kin cika k'awa ta kwarai nagode........"

Tafiya tafarayi tana cewa....

"Alhamdulillah, Alhamdulillah🤲🏻🙏🏼🤲🏻🙏🏼"

"Hindu ga kudinki"

"A'ah Hafsat kurike kukama hayan gida,kafin wani lokaci"

"A'ah Hindu baza'ayi hakaba....."

"Karki damu zanje in Kara cire wani kudin......"

"Hafsat idan Kika k'ara Mata magana Wlhy sai kin bita....."

Hindu ce tadagama Hafsat hannu itama ta daga Mata🙋‍♀️🙋‍♀️.....

Hindu Bata dad'e da wucewa ba Hafeez yazo nemanta Amma Bai sameta ba....

Yasha yawo amma Bai ganataba,dawowa yayi gidansu Hafsat,yabasu kudi da zai ishesu su gyara gidansu da Kuma su sayi Kaya masu yawa.....

*Kudai kunyi gobaran titi a jos😉*

Hauwa take kallo a YouTube kawai saitaga shari'ar HINDU HAMEED HUSSAIN.....

"Toh fa gawata Mai suna irin na ustaziyar gidanmu, Bari mugani"

Budewa tayi tafara kallo...

"Innalillahi 😲wa'ina ilaihirraji'un,Nashiga uku🙆‍♀️"

Kuka tafashe dashi😭,takira Habib a waya

😭 HINDU 😭Where stories live. Discover now