1

506 24 1
                                    


✨💫✨💫
*SHAHEED*
✨💫✨💫
*1442H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:- HIJJART ABDOUL*

*SADAUKARWA GA:-* FANS

*TUKUICI GA:-* SWEETHEART

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook:-https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 1📑*

*__________📖* Makaranta ce babba wacce ta had'a both primary and secondary School, primary section daban haka ma secondary da junior suma section d'in su daban yake sai dai duka a had'e suke Maza da Mata ce school d'in yanayin makarantar da tsarin ta kad'ai ka kalla zaka ga abin burgewa kawo daga ginin nata zuwa su kansu student d'in makarantar ta tsaru iya tsaruwa kana gani ma zaka san private school ce.

Break da akayi yasa duka students d'in tafiya dining dan ci abinsu wasu suna zuwa da nasu yayin da wasu suke ci a school d'in, mafiya wayanci a school d'in kowa ke ci idan kaga wsni yazo da abinci to new comer ne dining kowa ya nufa Mazan da Matan su dan dokar makarantar ce ba'a cin abinci a class, haka suka fita sai wanda baza suje ba. Kasancewar yanayi ne na sanyi duka students d'in sunsa rigar sanyin iri d'aya kowa ya d'aura a saman uniforms d'in sa.

Yarinya ce wacce bazata wuce 13 years ba tana tafiya a tsakiyar makarantar tasha sabbin uniform gashi ya d'au guga da takalmin ta cover shoe bak'i a cikin safa fara,rigar ta kamar ta kowa ta sauko hijabin ta k'arami iya gwuiwar hannu ya tsaya Kamar yarda na kowa yake sai dai bata sa rigar sanyi ba Kamar kowa kuma da'alama hakan be wani dame ta, d'an d'aga k'afa tayi ta kamo wanda ta gani a gaba yana tafiya.

"Excuse me?"

Ta fad'a a hankali, tsayawa yayi be jiyo ba ta Kuma cewa.

"Baka ji ba?"

Juyowa yayi fuskar sa d'auke da murmurshi tare da nuna mata wani symbol, bin hannun sa tayi da kallo har wurin ganin ansa no speaking of venacular yasa ta jan k'aramar tsuka ta maida kallan ta gare shi.

Tace, "sai kuma ban iya ba".

"Baki iya ba".

Ya fad'a yana mata kallan dagaske?

Tace, "kai me kayi yanzu to?"

Besan sanda wani murmurshi ya k'wace masa ba ya shafo kan sa.

Yace, "ke kika sani nayi, amma mu haka dokar school d'in nan yake kin gane?"

Shiru tayi bata ce komai ba.

Yace, "what do you want?"

"Din...ohh wurin cin abinci nake nema zanci abinci a class wai ba'a ci".

"Sai kin koma baya kuwa kin baro shi".

"Da nisa?"

Ta tambaya tana ya tsine fuska.

"Sosai ma".

Ya bata amsa yana gyara tsayuwar sa, wata 'yar k'ofa ta kalla ganin haka yasa yabi inda ta kalla da kallo sai gani yayi tabi wurin hannun ta kuwa da flask d'in ta, da sauri yasha gaban ta.

Yace, "Ina zaki je?"

Sai da ta had'e fuska tamau.

Tace, "can zanje naci abinci".

SHAHEEDWhere stories live. Discover now