👨👩👦👦*ZAMAN Y'AY'A👨👩👦👦
(*Based on true life story*)Story&written by *Mmn muhibbat*
Vote on wattpad _Mmnmuhibbat_
Dedicated to *TASKIRA MEMBERS*
Edited by *Khadija Manga*
This page is for again Fatima musa arugungu (Aisha Abdulaamad)HBD Allah ya karo shekaru masu albarka Allah ya raya zuri'a.
Page 30
Ta bangaren Salma rayuwa su sai hamdala domin dai yara sunan zaune gabanta sule ya biye ma yarsa samha kan cewa tunda umar bai zuwa shi ma bazai bi sahu ba kuma ya ara ya yafa wai taya yarsa kishi yake yi.Sule kudinsa da ya dawo da su daga abuja ne ya tamalmala ya hada ya bude shago a kofar gidansa yana saida kayan provision duk da bai kai wancan girma ba da fadi.Su salma ma suna sana'a sosai suna taimakon kansu da ita dan kuwa sule yanzu ba komai ne yake iya yi masu ba saboda kada a cinye jarin.
Salma taga ranar koyon sana'a.Ita duk da bata tara dukiya kamar ta wasu matan masu kitso da gyaran jiki ba saboda ketar miji amma alhamdulillah tana da sana'ar da take dogara da ita.Su samha ma yanzu da karfinta take kara aza su kan gyaran jikin amarya da suke koya Samha har da su kwalliyan amarya taje ta koya saboda su kayatar da sana'ar Mamansu duk da suma suna son idan suka koma dakin mazajensu za su cigaba da sana'arsu.
Zainab ta sake zuwa ganinsu inda take kwatanta ma samha akan hakuri da juriya a gidan miji da rike sirrin miji bai kamata ace akan abu kadan ba suna zuwa gidansu kawo karan juna hakan yana sauran lalata aure,ta koyi yadda zatai maganin matsalolin gidanta da kanta wanda bata iyawa tayi addu'a Allah ya gyara mata wadda kuma akwai cutarwa a gaba tou shine zata saka iyayenta kuma a cikin hikima.
Samha ta ji dadin shawaran Aunty zainab duk da ita ta tashi da wani tunani a zuciya na cewa ita fa namiji bai isa ya taka ta ba sai dai su taka juna saboda irin labarin muguntar maza da take ji daga wurin su mamanta da mata masu zuwa kitso da kuma hali irin na babanta.
Hmm ta ce a ciki. Zuciya ita wlh ita da maza sai Allah zai raba su bata taba raga masu yanzu itama ba gashi ya nuna mata halinsu ba.Subhanallah ta ji zainab ta ce haba samha da hankalinki kike irin wanna magana.
Dafe baki tayi dan bata yi zaton maganan ya fito a waje ba.
Ta ce Allah Aunty maza basu da halacci da adalci ga keta ki duba abunda umar yayi mani da kuma abunda baba yake ma mama.
Jinjina kai zainab tayi yana daga cikin abunda ke cutan wasu matan past na iyayensu,yana zauna masu akai sosai mace ko namiji idan suka taso suka ga iyayensu wani na zaluntar daya ko kuma suna fada a gaban yaran suna girma da tsanar wanda yake musguna ma dayan wani yaron har ya girma yana ganin ai duk gidan aure haka yake idan yayi rashin sa'a bai hadu da abokiyar zama ta gari ba sai ka ji yana ma mata kudin goro ko kuma ta yi ma maza kudin goro wanda hakan kuskure ne.
Kama hannun samha tayi ta ce samha hakan bai da ce ba maza ba duka suka taro suka zama daya ba kada zancen mata da karin maganarsu ya rudeki tabbas a cikin maza da mata akwai nagari idan Allah ya hadaka da wanda ba haka suke ba sai kayi tunanin haka suke duka kinga ni,na auri miji wanda ba nagari ba amma hakan bai saka nayi ma maza kudin goro ba da na bawa suraj dama kinga ya zo ya nuna mani tabbas maza ba haka su ke ba duka.
Jan numfashi samha ta yi ta ce nagode aunty wlh kullum da tsanar halayen maza nake kwana nake tashi sbd irin labarin da nake ji da kuma wanda suka faru da ni.
Zainab ta ce haka ne daman mutum zai ta gani suma maza wasu haka suke gani mata basu da kirki idan muna dora ma juna laifi kullum to yaushe za mu gyara yanzu da wani namijin zai baki labarin irn ukubar da yake ci a hannun mace sai kin mashi hawaye,kawai dan su ba kamar mu suke ba da raki kuma ba'a ji.
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
Non-FictionLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...