👨👩👧👦ZAMAN YA'YA👨👩👧👦
*Based on true life story*
Story&written by Mmn Muhibbat Abdullah
Vote me on Whattpad@Mmnmuhibbat
Dedicated to Taskira Members.
I dedicated this page to u *Zaman ya'ya grp* Especially Maman madina &ummy moimada comment din ku ya saka ni farin ciki.
*MARAICI A MATSAYIN WEAPON NA CUTAR DIYA MACE*PAGE 10
Zainab ce ta bude idanunta a lokacin da goggonta ta shafa mata ruwa a fuska ta dawo daga suman da tayi.Kallonsu take one by one dan so take ta tuna me ma ya sameta kallon fuskansu tayi taga ba mamanta a cikinsu sannan ta tuna abunda ya sameta zabura tayi ta mike zata fita aka rikota kuka ta fashe da shi lokacin da ta fada jikin goggonta ta ce "yanzu shikenan na rasa mamata na rasa baba ba da dadewa ba yanzu kuma mama ta tafi ta barni Ya rabbi!!!Ya rabbi!!Ya rabi! Ka duba lamarina kuka take sosai duk wanda ke wurin sai da ya tausaya mata kwarai da gaske.Jameel kanenta ne ya shigo inda take shima idonsa yayi ja sbd kuka ga tausayin yar uwarshi da yake damunsa abu goma da Ashrin gwara shi namiji ne amma ita fa kama hannunta yayi ya mikar da ita ya ce" ta zo su yi bankwana da mama dan an gama shirya ta za'a kaita makwanci sbd magrib ta kusa.
Goggo ce da makwabtansu zainab suka rike ta sbd yadda take kuka shiga tayi dakin babansu inda akai ma mama wanka fadawa tayi jikin gawar mamarta tana wani irin kuka mai taba zuciyar mai sauraro sunkuyar da kanta tayi ta sumbaci goshin mamarsu tana mata addu'o'in da sai da duka dakin aka sake fashewa da kuka jameel ne ya zo ya janyeta. Dangin mamansu ne suka shigo suka dauki gawar mama domin kai ta makwancinta.Kuka zainab ta kara fashe wa da shi mai sauti tana cewa shikenan mamana gata na shikenan na rasa gatana duniya Asirina ya tono ya rabbi ya dafa mani lamarina.
Jameel ne ya rufa mata baki yana maimata mata hasbunallahu wa ni'imar wakil.Goggo ce ta rike zainab sbd jameel ya tafi akai mahaifiyarsu gidanta na gaskia sbd daman daga shi sai zainab su biyu Allah ya ba iyayensu tunda zainab mace ce bazata saka mahaifiyansu kabari shiyasa sai dai shi zai je ya sakata.
Ya illahi yana ji yana gani ya kama gawar mahaifiyarshi tare da yan uwanta ya maida kasa ya rufeta babu tsumi babu dubara dole wannan rana zata riske ko wani bawa muna ji muna gani wata rana tun muna rufe masoyanmu har wata rana makusantanmu sukai mu su rufe su juyo gida duk kaunar jameel da mahaifiyansa iyakar gatan da zai mata kenan aka barota daga ita sai aikin da ta shuka a duniya su zasu zame mata abokan zamanta .( *Dan me yasa muke saida lahiranmu sbd duniya,dan me yasa zaka/ki sabi Allah sbd ki mallake miji ko ki kore kishiya ko ki cutar da ita ko kuma ki afka cin haramun domin kiyi ado ke da yaranki ko kuma ki afka sharrin zina sbd zaman ya'ya gulma,hassada,kyashi shigar banza,saka turare mai tsananin kamshi yayin fita unguwa,fitar da gashi sune suke kai mata da yawa wuta gaya dai tana biyayyar miji amma biyayyar Allah ta gagareta ya subhana ka shiryamu*).
Zainab kuwa tana can gida haka tana gani yan kai mamanta makabarta suka dawo shikenan fa rayuwan ba su sake haduwa sai a mafarki😭😭Hmm wani kuka ne ya sake zuwar mata,haka zainab ranar ta kwana sallah tana neman saukin rayuwa a wurin Allah ita da goggonta ne gidan sai jameel a dakin babansu sai yaranta.Haka aka share zaman makoki aka watse sai zainab da goggonta suka rage a gidan sai masu zuwar mata daga baya gaisuwa talle ma ya zo mata gaisuwa sbd mutuwar ta bashi tausayi sosai ganin an share kwanaki zainab bata fara shirin komawa gida ya saka goggonta yi mata magana yaushe zata koma gidanta shiru tayi can ta nisa ta ce "goggo ai ya sake ni " Zabura goggo tayi ta saki salati tare da ta'awizi kmr taji sabon Allah ce wa tayi garin ya'ya ya sake ki zainabu.Shiru tayi can ta ce goggo na roke ki da girman Allah kar ki sake tambaya ta dalilin sakin domin alkawari nayi babu wanda zai ji wannan maganr insha Allah amma wlh goggo ba laifi na ba ne.
Goggo tace ke kuwa zainabu ai hkr ake ko dan saboda yara nan, kuma yanzu zaman zawarci wuya gare shi gaki marainiya kuma. Dan Allah ki daure ki yi hkr ki koma gidan mijinki ko dan yaranki.
Shiru ta yi ta ce "goggo da hkrin na magani tabbas da nayi goggo wannan matsalan ba hkri bane zai maganinta ba sai dai hakan da nayi shi ne dai dai. Iyakar kokarina goggo nayi amma na gaza shi yasanya.
![](https://img.wattpad.com/cover/245334753-288-k728662.jpg)
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
Não FicçãoLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...