👨👩👦👦*ZAMAN Y'AY'A👨👩👦👦
(*Based on true life story*)Story&written by *Mmn muhibbat*
Vote on wattpad _Mmnmuhibbat_
Dedicated to *TASKIRA MEMBERS*
Edited by *Khadija Manga*
Page 31
###Al'ameen ne tsaye a kofar gidansu balki fakin din motarshi yayi ya fita ya je yayi knockin maigadinsu ya bude mashi (sbd yanan shi bai tafi ba ya zauna saboda sabo da sukayi da gidanshi da matarshi). Sallama yayi ya shiga cikin falon.Balki ce zaune da mima sannu hanya sukai mashi bayan ya zauna kasan carpet,balki tayi tayi da shi ya zauna saman kujera yaki.
Cikin daki mima ta shiga bayan sun gaisa.Mama ina wuni ya kara cewa"
Lpia lau.Ya su hajia
Ya ce suna lpia.
Tace An gama karatu Allah ya sa alheri ya sa tsawon rai akai mawa.
Ameen ya ce.Shiru sukai dukkansu.Balki ce ta ce mashi sai ka ji abunda ya same kanwarka.(sbd tasan maganr ba inda vai je ba)
Ya ce wlh kuwa sbd haka daman nazo mama.
Allah sarki ta ce.
Ya ce mama daman ina son in turo su kawu su nema mani auran afifa idan ta aminci tana so na bayan ta haihu sai a daura mana aure.Balki sakin baki tayi sbd yadda maganr da shigar mata zuciya Allahu Akbar yanzu har akwai mai son afifa a haka Allah sarki rayuwa.
Ta gaza boye murnanta ya gani ta ce mashi yanzu kana ganin ba matsala ace afifa zaka aura kana saurayi ace ka auri wadda ta taba haihu ba tare da aure ba kana ganin a can wurin iyayenka ba wata damuwa da wurinka ma.
Al'ameen cikin jin kunya ya ce mama ai kaddara ce ta fada mata babu wanda ya wuce Allah ya jarabceshi da kwatankwacin kaddara irin tata dan haka ni wlh da zuciya daya nake sonta xan aureta,Sannan su mama nasan bazasu bani matsala ba insha Allahu.
Murna sosai balki tayi bakinta yaki rufuwa,mikewa tayi ta ce bari ta turo mashi afifa su gaisa( sbd tunda cikinta ya fito ta rage zama falo kullum tana daki).
Dakinsu ta shiga ta isketa kwance mima na lallashinta domin duk idan abun ya fado mata cikin rai sai tayi kukan bakin cikin yadda rayuwanta zata kasancewa a gaba.
Balki zama tayi kusa da ita ta ce ta tashi ta wanke fuskanta Al'ameen na kiranta.
Bata fuska ta yi ta ce wani al'ameen kuma?
Mima ta ce na gidan kawu Aminu.Shiru afifa tayi tasan shi sama sama sbd ita maza ko yan'uwanta ba wai sake masu jiki take ba bare ya'yan dangi.
Toilet ta shiga ta wanke fuskanta dogon hijabinta ta zura ta fito.Zaune ta ganshi ya kura ma kofar dakin ido.Kallonsa tayi yana sanye da shadda blue da hula kalar kayan yayi kyau a cikin shigar kasancewarsa mai matsakaicin kyau irin na hausa fulani.Mamaki take me ya kawo shi gidansu da har yake son yin magana da ita su kadai bata saba kebewa da namiji ba shiyasa duk sai ta ji ta takura,gaidasa tayi cikin sarkewan murya kasancewarta ba mai yawan magana ba sannan wannan cikin ya saka ta kara zama shiru-shiru.
Lpia lau ya ce yana mata kallon tausayi cike da soyayya sosai ya kare mata kallo sadda ta fito daga dakinsu yarinya karama Amma kaddaran rayuwa ya hau ta.Yanayinta da natsuwarta ya saka ya ji ya kara kaunarta yaga cikonta ya fito kasancewar yanzu yana cikin wata na 6 kenan.
Ya babyna ya ce.
Dago kanta tayi cikin sauri tana mamakin dalilin da zai jingina kansa da dan cikinta,tunda ta samu cikin nan inda ba mima ba babu wanda ya taba tambayarta lpiar babynta,tana kaunar babynta da tausaya ma rayuwan da zai fuskata idan ya zo duniya ya ji hanyar da aka samar da shi kasancewarta musulma mai daukan kaddara ya saka bata kin jini babynta sbd shi baya da laifin komai a rayuwansa.
![](https://img.wattpad.com/cover/245334753-288-k728662.jpg)
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
Non-FictionLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...