TONON ASIRI

273 38 0
                                    

👨‍👩‍👧‍👦ZAMAN YA'YA👨‍👩‍👧‍👦
*Based on true life story*
Story &written by Mmn muhibbat Abdullah
Vote me on whatpad @Mmnmuhibbat

Dedicated to *Taskira members*
   
   Page 11
   *TONON ASIRI*
   Zainab ce zaune tana soyar kosanta yan saye sun zagayeta wasu yan mata ne ta ji su na gulmar attine wai mijinta ya dawo unexpected ya sauka a sabon layi tare da wata kilaki su ka zo daga lagos kawai sai ya ganta ta fito daga wani daki wani mutumi rike da hannunta shi ne wai fada ya kaure tsakaninsa da kwarton Attine shi ne shi kwarton yayi masa gori ya ke ce wa "idan har ba Azzalumin namiji ba wanene ke tafiya ya bar matarshi ba kulawa dan haka su ne gatan duk wace mace da ta hadu da maketacin namiji irin habibu mijin attine.Shi ne wai shi jan wuya zai bugi mutumin aiko ya bashi kashin bala'i shi ne fa ya sauke haushin kan attine da ta rude ita ta manta ma da karuwa ta ganshi haka akaita dauki ba dadi da mutumin da habibu dakyar aka raba su .

Shi kuwa ya taso attine a gaba yana mata tonon silili a bainar nasi har gidan kawunta ya kawota wanda daman tsakani gidanta da gidan kawun ba nisa sosai da gidansu zainab. shi ne mutane yan son jin gulma suka bi a cikin gida suka ji ya rafka mata saki 3 saboda wai ta ci amanar auran sa Allah ya isa tsakanin shi da ita aikuwa jin wannan saki ya saka kawu yayi mata wulakantacen bugu kowa ya hau zagintaa da tsine mata ta ci amanr aure .Alhali ba wanda ya bi mata hakkinta da shi habibun ya tauye sabda ita diya mace ba mutum bace, ba wanda yake damuwa da kukan ta sai ta aikata aikin assha sannan za ku ga duk duniya sun shaida haka amma lokacin da take neman taimako babu shegen da ya iya tallafa mata.Daman ita diya mace idan ba'a kula da ita ba lalacewa take shiyasa farko gaban iyayenta daga nan sai gaban mijinta daga nan sai karkashin kulawar yaranta amma ita attine an sakar mata ragamar kula da rayuwanta ba'a barta nan ba sai da aka hada mata da kari wato yaranta guda 5.
Sadda tana kawo kukanta habibu na tauye mata hakkinta a matsayinta na mai rauni ba wanda yaji kukan ta sai dai aka ce tayi hkr tayi zaman ya'ya shin idan mace ta samu ci da sha da sutura da sauran abubuwa shin bukatar namiji fa waye zai biya mata shi yana can uwa duniya.
Abu 2 suna saurin halaka bawa yunwa ,sha'awa shiyasa ma Allah ya umarce mu da azumi dan yaga masu imanim cikin mu domin abunda muke so ne aka hane mu da shi.Shiyasa ladan azumi Allah da kanshi yake badata sbd girman ibadar.

Haka jama'a sukai ta tufin ala tsine da attine har da masu cewa hukunci kisa ya kamata a zartar mata tunda ita matar aure ce.( *Shi haddul zina yana tabbata ne ga wanda aka iske yana zina sannan shaidu 4 suka kama shi yana aikatawa tou dole a kamu shi ayi mashi haddi.ko kuma wanda yazo yayi zina kuma ya kawo kanshi ya fada yayi sannan kuma yna son ayi mashi haddi)

Haka mutanen nan da yan gidansu attine aka taru kanta da wulakanci ita dai ga ta nan dai zaune ba uhm ba uumm saboda takaicinta yanzu idan yaranta da ta bata rayuwanta sbd zaman su,suka ji ya za su ce mata ta san zasu tsaneta sbd bata kyauta masu ba sannan ta bata masu suna yanzu haka tana jin wasu suna cewa anya ma yaran habibu ne.
Inda Allah ya taimaketa daya duka yaran habibu suna kama dashi sannan bata fara zina ba sai bayan ta haifi yaronta na karshe saboda a lokacin shekarunta sun doshi 30 shiyasa ta kasa rike sha'awanta har ta afka halaka ta cuci kanta ta cuci yaranta ita dai *zaman ya'ya* ya jaza mata (na ce da kuma tsoron zawarci).

Kawunta cewa yayi kada wanda ya sake y rika bata abinci sannan ga daki can bakin zaure nan zata zauna a ciki kar ta gurbata mashi tarbiyan yara sannan ya hana kowa mu'amala da ita.

Haka ta tattara kayanta ta koma ita kadai dakin kmr mayya domin da taje kwasar kaya taga kallon tsana da kyama da danta yake mata bata san wani kilbabben ne ya gaya mashi ba sbd shi kadai ne mai wayau sosai ckn yaran.

Zainab dai tana jin su amma bata tanka masu ba sbd ita cewa tayi taji da nata zunubin ma haka nan kawai tunda fara safiya ta hau cin naman mutane.

###Rayuwa tayi ma attine zafi sbd halin kuncin da ta shiga ciki yanke shawara kawai tayi ta koma bariki zai fi mata zaman yunwa da take yi .Tana son ta shiga gidansu zainab ta bata hkr tayi mata gaisuwan iyayenta amma tana jin kunya amma ko ba komai zata je ta nemi gafarar ta ko Allah ya saka wani bala'in da ke shirin tunkararta yayi mata sauki sbd tasan ta shiga hakkin zainab da ta zama sanadin kashe mata aure duk da wlh bata san mijin zainab bane da bata bishi gidansa ba .

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now