JAHILCI MUGUN CIWO

406 43 0
                                    

👨‍👩‍👧‍👦ZAMAN YA'YA👨‍👩‍👧‍👦
   *Based on true life story*
   *Story&written by Mmn Muhibbat Abdullah*
   *Dedicated to Taskira Members*
I dedicate this page to u fatima Aminu(Maman madina) Comment dinki yana kara mani karfin gwiwa😘😘🥰
   Page 4

****Ma'u ce zaune tana kuka saboda tsananin bakin ciki yanzu shikenan Mudi ya sake ta yanzu ina zata saka ranta ya rayuwan yaranta zaya kasance.Yanzu shikenan haka zata tafi ta bar yaranta tsakar gida shikenan su sha azaba wurin kishiyar uwa kuka ta kara fashewa 😭da shi a lokacin da ta tuna haka.

  Shi kuwa gogan Mudi baccinsa kawai yake bai ma san tsiyar da ya shuka ba.

   Washe gari haka ma'u ta tashi cikin sanyin jiki tana tattara kayanta domin ta bar mashi gidansa tana yi tana hawaye sani na gefe yana kallonta.

Ya ce mata mama ina zaki?
Ta ce gidanmu za ni sani ta fada cikin hawaye😭
Dariya ya fashe da ita yana tsalle jin cewa zasu koma gidan kakaninsu da zama at least mamansa zata huta da bugu kullum.
Cikin doki irin na yara ya tashi yana hada kaya.

Kallonsa tayi da ya dawo yana dauke da akwatinsu na karfe dakyar yake janshi.
Ce mata yayi mama ta shi mu tafi.

Wani kallo tai masa cikin tausayi tace ai banda ku zani,ku zaku zauna gidan babanku ne.

Ihu ya buga yace walahi mama bani zama baba ya kashe ni da bugu tunda baki nan babu wadda zai buga.

Cikin hanzari ta buge mashi baki tace in kara jin ka kana fadin haka ga mahaifinka ranka zai baci na gaya maka.

   Rikicinsu ne ya tada Mudi daga baccin da yake daman ko sallar Asuba bai ba haka ya fito kayan jikinsa a yamutse.

Kallonta yayi tana hada kaya ya ce me ke faruwa ne?
Kallonsa tayi cike da hawaye ta share shi

Karaf sani yace gidan su mama zamu tafi baba in mun girma zamu dawo da maama.

Harararshi yayi yace wuce ka ba mutane wuri kafin in tsinka maka mari marar kunya.

Sumi sumi ya wuce yana magana kasa kasa.

Shi kuwa mudi kallon ma'u yayi da lokacin har ta saka mayafinta ya ce ke bana son shashanci ya ina maki magana zaki wani share ni gidan uban wa zaki.

Kallonsa tayi ido cike da hawaye tace baka ce ka sake ni ba har saki uku zaman me zanyi.

Kallonta yayi ya ce saki😳yaushe akai haka ni walahi ban sake ki ba.Rage muryanshi yayi ya ja hannunta suka shiga cikin daki ya kora su sani makwabta.

Ya ce ma'u kiji tsoron Allah yaushe na sake ki ko dai guduna kika fara yi ne.

Kallonsa tayi cike da mamaki tace haba mudi kaifa da bakinka ka furta haka jiya.

Ya ce niii!!😳ni gaskia ban ce ba dan haka ba inda zaki.kuma ma waya gaya maki ana daukar maganr wanda bai cikin hankalinsa baki san bara da naje tafsirin ramadan ba naji malam yana cewa an dauke alkalami ga mutum 3
1.karamin yaro
2.mai bacci har sai ya farka
3.mahaukaci har sai ya sami lpia

Kallonsa tayi cike da zakuwa tace da gaske!!

Ya ce walahi kuwa ai bani da hankali sadda nayi sakin .

Aikuwa take ma'u ta yadda saboda daman tana tunanin ina zata bar yaranta shiyasa jiya ko baccin kirki bata yi ba.
( *Allah sarki ma'u karamin sani ququmi a lokottan baya daman ilimi ya mace ba wani muhimmaci ake bashi ba har a yanzu ma wasu mutanen musamman kauye suna banza tar da ilimin diya mace ada har cewa ake wai sabbi (izif daya)saukar mata saboda wadda tayi kokari takai izif daya ta safke saboda wasu talla suke yi a wancan lokacin sannan ko a yanzu gani muke idan mutum yasan Alqur'ani ko yayi safka ilimi ya wadace shi baccin kafafen yada labarai kmr su Tv da radio suna kawo karatuka da har yanzu fa muna nan a wannan gaba domin dai mace kullum kallonta ake she belong to kitchen and other room🤣 shine kawai abunda ake koya mata shiyasa al'amarinmu na aure ya tabarbare ya lalace yar uwa ki nemi ilimin addini ko a birnin sin ne dan kinsa qur'ani kadai bazai rikeki ba ga al'amarin addiniku domin ba'a fahimatr alqur'ani sai da hadisi ba'a fahimtar hukunce hukuncen alqur'ani sai an san fiquhu da sauran littatafai a yanzu gani ake mace mai ilimi itace yar boko shiyasa da muka tashi sai muka dauki akidar bokon ba wai karatun bokon ba ,bawai nace ilimin boko bai da kyau ba a'a mu hada duka domin shima ilimi bokon ba'a son musulmi yayi duhun kai a wani sabon karatu da ya shigo domin Annabi saw yace ku kare addini ku da harshen ku da kudin ku tou baka iya komai ba ana ganinku wasu jahilai taya zaku kare addini ku sannan ilimi ko wani iri ne dadi gareshi.Annabi s.aw ya umurci a koya ma matarshi Hafsat R.A rubutu duk da shi ummiyi ne baiyin rubutu saboda ta iya kada a rubuto mata matsala ta kasa karantawa. SANNAN Annabi s.aw ya umurci wani sahabinsa da yaje ya koyi rubutun girkanci domin yahudawa suna rubuto ma Annabi s.aw wasika da yaren su tou bai son ya saka bayahude ya karanta masu yayi karya.* )

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now