MACE TA GARI

282 35 0
                                    

👨‍👩‍👧‍👦ZAMAN YA'YA👨‍👩‍👧‍👦

*Based on true life story*
Story&Written by Mmn muhibbat Abdullahi
Vote me on wattpad@Mmnmuhibbat
Shin yar uwa kinsan inda saka miski bayan kowa ce al'ada ko bayan haihu(Nifas)ya samu asali:
"Daga ayshata R.A daga nana Asma'u ta tbye Annabi s.a.w game da wankan haila sai ya ce mata" dayan ku ta samu ruwanta da ruwan magaryanta ta tsarkake gabanta tsarki mai kyau sannan ta samu cotton(kada)ta saka a cikin miski ta saka a gabanta..........,zuwa karshen hadisin(Muttafakun alaihi)Dan haka matan Albarka ga sis dina maman hydar ta zo maku da misk dahara akan farashi mai sauki ku neme ta ta wannan numbern +2349061214997

Page 17
   ##Gaje haka ta yini cikin daki dakyar ta bude da bala ya buga mata zai bata yaro ,komawa tayi ta rufe.
Lekawa tayi ta window ta kira almajirinsu ta aike shi gida a kirawo mata samarin gidan su,su ce ga balki nan zata kashe ta.
Tafiya yayi ya je gidan su ya gaya ma yan uwanta aikuwa daman aka taki sa'a suna nan dauko sandunan su sukayi suka biyo bayan almajiri wai yau sai sun bugi balki har da yayar gaje.

Gaje na jin sun shigo ta fito daga daki ta fara sakin ashar.

Balki na jin ta fara mata gorin ai daman bala ya ce mata zaman kaddara yake da ita zaman ya'ya take, abunda ko dadin ta bai ji habwa balki na jin haKa ta fito domin kuwa tunda take ba'a taba ci mata mutunci irin haka ba tana fitowa taga yan uwan gaje tsakar gida, fitowa tayi bata ji tsoron su ba itama aka fara bata kashi tsakanin su ance sarkin yawa yafi sarkin karfi,balki ganin za su illata ta ya saka ta fara ihu aikuwa sai ga makwabta sun shigo yaranta sai kuka suke su ma babbansu dan shekara 12 ne ya shigar ma uwarsa aikuwa gaje ta fasa mashi kai ganin abun zai kai ga kisan kai ya saka wani makwabcin su ya je ya kira bala kasuwa da saurinsa ya iso.Tambayrasu aka fara yi me ya hada su gaje ce ta fara kora bayani aikuwa bata ida sa ba balki ta tare ta itama nan ta zazzage irn zagin cin mutuncin da yake ma gaje.
Gaje sarki zuciya ta sake balki ta koma kan bala cakumar rigarsa tayi aikuwa sai keeee kake ji karar yagewa direta tayi gida biyu .
wanka mata mari yayi yan uwan gaje ganin an mari yar'uwarsu ya saka suka far ma bala sukai mashi tsinannen duka har baya iya motsi.
Ce wa yayi ya sake gaje ta tattara ta bar mashi gidansa tunda yan uwanta yan iska ne aikuwa ita ma tana bisa dokin zuciya dan haka ta kwashe kayanta tayi ta bi yan'uwanta.(Daman tabarmar kunya da hauka ake nadeta)

Balki ce ta matsa kusa da shi zata taimaka masa ya rufe ta da bala'i itama ya ce ta tafi gidansu sai ya zo tunda har ta iya tona mashi asiri gaban mutane kuka balki ta fara tana rokonsa dan Allah ya taimaka ya rufa mata asiri kar ya koreta bata da wani gata da ya wuce gidansa .
ya taimaka mata ya ce ai daman kin ce haka tun da nan ne kadai ki ke cin dadi ba ki je gidanku, ki ci miyar kuka ki ji in ina da rana.Haka tai ta bashi hakuri yana mata gori yana gaya mata magana.Da yake bata da zuciya haka ta nace sai da ya kyaleta.

############################Sady da sule kuwa an isa abuja lpia yaron sule ya yi mamakin kara ganin sady ta dawo gidan sule bai yi tunanin zai dawo da ita ba kam, amma Allah ne ya kama oga sbd ya cika zaluntar uwargidansa shiyasa Allah ya bashi dai dai shi.

Gida ta shiga abunta ta je fa kara gyara dakinta ta leko waje neman almajirin da xai sayo mata cefane tayi masu girki,yaron sule ne ya amsa shi sakon ya je ya sayo mata ta shiga cikin gida ta tsara girki abunta ta fidda na sule ta ci nata.Sule ganin girki ya saka ya mance da fushi da yke da sady dan haka ya saki baki ya kwashi girki.

Washe gari da ta tamabyeshi kudi kin bata yayi ta ce tou wato halin na nan bai tafi ba kenan.Banza yayi mata ya shige bayi dan yin wanka.

Tana ganin ya shiga bayi ta duba aljihunsa ta ga kudi yan dubu dubu amma shi ne dan keta bai bata 3k ta cira na kwana 10 sbd ta huta da kullum sai ta tambaya.
   Fitowa ya yi daga bayi ya iske ta daukar mashi kudi bala'i ya fara ya na ja mata Allah ya isa banza tayi mashi dan bata da lokacin biye masa ita dai ai taimakonsa tayi ya sauke nauyin hakkin da Allah ya dora mashi nata dan haka banza tayi mashi.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now