Duk Abunda ka boye

529 40 1
                                    

👨‍👩‍👧‍👦ZAMAN YA'YA👨‍👩‍👧‍👦
*Based on true life story*
     Story&written by Mmn Muhibbat Abdullah👩‍👧‍👧
  *Dedicated to TASKIRA MEMBERS*
I dedicated this page to Ciwon Ya mace grp
  Page 3
*******Tun Daga soron gidan take mamakin Abunda ya dawo da Talle amma tayi tunanin may be wani Abu ya dawo dauka saboda ranar working days ne.

Tana shiga Abunda ta gani ne ya razana mata tunani ya saka zuciyarta tayi tsayuwan some seconds.

A firgice suka kalleta suna mamakin abunda ya maidota Talle ne tayi saurin tashi ya fara neman Abunda zai rufe jikinsa.
Laure ko tsoro da kunya ne suka hanata tashi.A hanzarce Talle ya finciko Laure ya wurga waje yayi hanzarin rike zainab da ke shirin suman tsaye.

Zainab kuwa fisge jikinta tayi ta ja jikinta ta zauna kusa da gadon karfenta,tunani take shin mafarki take ko a farke take?Me Talle ya rasa cikin dakinta fa Ya Allah Abunda ta furta kenan cikin zuciyarta sai tasbihi take dan samun saukin zuciyarta.

Shi kuwa gogan zama yayi bisa karamin gadon su kunya duk ta rufe shi hakuri yake son bata amma kunya ta hanashi magana.
Can dai ya daure ya ce "zainab dan Allah kiyi hakuri sharrin shaidan ne"

Wani mummunan kallo ta jefa mashi wato al'amarin dan Adam yana bata mamaki sai ya gama aikata son zuciyarsa yace sharrin shaidan ne.

Kallonsa tayi cikin kunan rai tace sharrin shaidan fa kace sadda zaka aikata son zuciyarka shin baka tuna Allah yana kallonka ba shin baka tuna ba cewa wata rana Asirin ka zai tono ba?shin ka manta kwanciyar kabari ne ko kana tunanin hisabi wasa ne?

Matsowa yayi kusa da ita zai bata hakuri ta daga mashi hannu domin kuwa hakurinta yana daf da karewa ta gaya mashi mummunar magana domin wlh yadda kimar sa da girman sa ya zube a idonta farat daya ba ,Abunda  baza ta iya gaya masa ba.

Kukan da sani yake ne ya dawo da ita daga duniyar tunani amsar sa tayi daga hannun babansa wanda wurin amsar shi ma ko hannunsa bata son ya taba jikinta ji take kamar ta shakesa tana da tarin abun ce masa Amma jira take zuciyarta ta gama sauka dan kar ta saka ta aikata mashi mummunan aiki.
   Shi kuwa talle mikewa yayi domin yaje ya wanka duk Abun duniya ya damesa ba wai yana nadamar abunda ya aikata ba a'a yana nadamar me yasa bai kulle gidan ba ne ,kuma da yasan zata dawo da ba gida suka hadu da Laure ba da sabon layi ya isketa tunda daman can suke hadewa.

Har yayi wanka ya gama ya fito tana zaune inda ya barta tana kuka ,matsowa yayi zai dafata ta mike ta kyakeshi tambaya daya tai mashi wadda ta buga mashi zuciya
Ce mashi tayi tsakanin shi da Allah wannan ne na farko ko daman ya saba yaji tsoron Allah ya mata rantsuwa da Alqur'ani gaskia ya fada mata

Zaro idonsa😳 yayi domim shi kanshi bai iya tuna sau nawa yayi kuma yaushe ya fara shiru yayi wanda shirunsa shi ya bama zainab Amsar da take nema cewa ba yau ya fara ba.

Mikewa tayi ta shiga toilet dan dauro Alwala da ta fito ta tada sallah,karatu take Ammma kuka take saboda tsananin bacin rai da tazo sujjadan karshe ta dade tana kwararo Addu'o'i domin Allah ya bata karfin gwiwa da karfin zuciyar tunkarar lamarin.Domin a rayuwarta ta so Allah ya bata Mijin da zai tsare kanshi da tsare iyalinsa daga wuta kmar yadda Allah s.w.a yace (Yaku wa'anda kukai imani ku tsare kanku da iyalanku daga wuta)TALLE bai tsare kanshi ba itama ba wai yana mata kishi irin wanda Addinin islam ya koyar ba a'a kishi yake mana ta irin ja jahilci.
Domin duk Abunda ya kamata ace ya kiyayeta daga fadawa halaka ba shi yake yi ba tunda gidanta cike yake da Mazan da ba muharamanta ba gashi ba ruwanshi ko da zata nuna kwalliyarta gare su haka ma idan zata fita unguwa bai damu da duk shigar da taga dama.zatayi ta fita ba ko da kuwa zata bade kanta da turare ne sai dai yace tayi kyau uwa uba rashin barin ta taje ta nemi ilimi sai dai yawon unguwa.

Tana gama sallah a nan ta kwanta har dare yunwa daman ba'a maganarta a wannan halin salla kadai ke tada ta har isha tayi talle bai dawo ba.

   Shi kuwa talle gurin bhaba
ya wuce yana labarta Mashi Abunda ya faru.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now