DAGA KIN GASKIA

298 33 2
                                    

👨‍👩‍👧‍👦 *ZAMAN YA'YA*👨‍👩‍👧‍👦
*Based on true life story*

Story &written by *_Mmn Muhibbat Abdullah_*

_Dedicated to taskira members_

_Edited by *Khadija manga*

_Wannan  page din naki ne qawar arziki khadija (ummen Abba) ina miko gaisuwa Allah ya bar qauna._❤️❤️❤️❤️

*Page 24*

   Dakin su ta shige tana guna guni wai wannan munafukar tsohuwar ta saka mata ido ina ruwanta da rayuwarsu

Hajia kuwa tana falo tana jiran mudi ya dawo ta gaya masa ta ji ya akai yayi sakaci da tarbiyan diyarsa haka yarinya karama

Tana zaune  kuwa taji karar motarshi yau ya dawo da wuri sbd su yi hira da mahaifiyarsa

Da sallama ya shigo dakin ya duqa har kasa yana gaidata,  anan ta rufe sa da fada tana gaya masa abunda hanifa ta aikata yau.

Ji yayi lumfashinsa na shirin daukewa sbd firgici. Hanifa de yar ficiciyar yarinyar nan ce zata kawo masa namiji cikin gida bada saninsa ba lallai kuwa yau zata gane kuranta.

Haurawa sama yayi ya kwala wa ma'u kira da har takai legas cikin baccinta😂

A firgice ta tashi tace lpia naji kana mani kiran mafarauta haka ?

Ce mata yayi su sauko su duka kasa har da su hamza duk a kira masa su.

  Bayan minti 10 duk suka hallara hamza da ganinsa a buge yake amma yana ta kokarin kada kwaya ta rinjayesa ya kwabsa gaban wannan munafukar tsohuwar aje a samu na fada wa mutane a cewarsa.

Tambaya ya fara jero ma hanifa a take cikinta ya murda har amira dake gefen su ta tsorata da jin tamabyar. Sani hanifa ya ke kallo bai ji mamaki ba dan ya san zata aikata sbd abunda ya karanta a wasikanta ya nuna har a makaranta ma suna haduwa da yaron bayan classes inda ba mutane.

Shru tayi ma'u ce ta taso masa da bala'i ta ce wane munafuki ya gaya maka?

Ya ce uwata kike ce ma munafuka lallai sannunki ma'u.

Hajiyar ta gaya maka yanzu tsakani da Allah yarinyar nan yar karama da ita har a kitsa maka wannan labarin ka hau bisa ka zauna ina hanifa ina tsayuwa da samari a cikin gidansu har ya kai ga rike mata jiki haba jama'a shikena dan ba'a kaunarka shikenan sai a bi yaranka da sharri dan bakin ciki da hassada irin na mutane.

Kuka hajia ta saka ta ce ma'u ko ina ma mutane sharri kinsan bazan ma jikata ba idan nayi mata sharri dadin me zan ji da me zai amfaneni?

Ranshi ya kara baci ganin yadda hanifa ta ke murguda ma uwarsa baki a fakaice aikuwa bugu ya hauta da shi yana tambayarta sai ta gaya masa dan gidan uban waye yaron yau sai ya saka an daure shi shida ubansa

Kuka take tana ihu ma'u ta taho zata amsheta a hannunsa ya ce wlh kina matsowa sai na karya ki na kuma kora ki gidanku ai ki dakata ina zuwa kanki ne wlh.

Jin ya ce zai kora ta gidansu ya saka ta dakata amma idan ranta yayi dubu ya baci ta kara jin ta tsani hajia domin kuwa sharri ake ma diyarta wlh yaran da ta bari suna kallo a falo sune za'a ma wanna bakin sharrin.

Wuka ya dauko a dinning yace idan bata gaya masa ba ko wanene shi zai yankata wlh jikinsa sai kyarma yake tsabar bakin ciki.

Ce mashi tayi dan schl din su ne kuma wlh book dinsa yazo amsa.

Hajia tace menene book?yaron da ya jima da zuwa ne xaki ce wani book yazo amsa to ko shine kika bashi cikin hijabi.

Zaro ido tayi ta ce littafi fa ni wlh ban saka shi cikin hijabi ba.

Ma'u ce tayi magana tace ka dai ji littafi ya zo amsa ai ni dai ko da na ji.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now