👨👩👦👦*ZAMAN Y'AY'A👨👩👦👦
(*Based on true life story*)Story&written by *Mmn muhibbat*
Vote on wattpad _Mmnmuhibbat_
Dedicated to *TASKIRA MEMBERS*
Edited by *Khadija Manga*
_Wannan page naki ne *FATIMA MUSA ARUGUNGU TASKIRA*Ina miko gaisuwa tare da godia Allah ya bar kauna.
Page 28
Ihun da tayi ne ya saka afifa ta warka jin jikinta ta yi wani iri kamar iska ya yi mata yawa tana dubawa taga babu komai jikinta yunkurawa tayi da niyyar tashi amma zafin da ta ji ya saka ta koma kwance kuka ta fara yi mima ma kuka ta fara domin ta rasa yadda za'ayi ta taimaka ma yar uwanta ta mike,dakyar da dubara ta saka kayanta dafa mima ta yi suka fito falo jakar su suka dauka anna ta ji wayarta na ringing kin dauka ta yi domin dai yau tasan ta shiga uku hannun iyayenta musaman bala dan sai ya kusa kasheta idan ya ji.Dakyar suka fito wurin get din fita aikuwa bisa kuskure wani ya tako motanshi da karfi ya buge su gefen kafar afifa ya buga dan haka wata irin kara ta saki.Rudewa yayi ya fito ya na ba su hakuri ce wa yayi su shiga motan ya kai su asibiti a duba su sbd kafan afifa kafar ya gurde dakayr ya taimaka mata ta shiga domin azaba goma da ishirin.
Private hospital ya kaisu aka duba kafar afifa aka ce ta goce a kafan dole suka daura mata kafan amsar numbern balki yayi ya kira ta yana masu kwatancen asibitin.
Ta roki mima Allah da Annabi da ta rufa mata asiri kar ta tona mata bayan an ba su daki domin dai sun riketa ta huta.
Ruwan zafi ta tambay aka ce a toilet din akwai mikewa ta yi dakyar tare da taimakon mima domin tana son ta dan gasa jikinta domin ta taba karantawa a novel idan akai first night da amarya ana gasa mata jikinta shiyasa ita yau ta ke son gwadawa ko ta samu sauki.
Har toilet suka shiga da mima ta taimaka mata tana mai rufe idonta kuka sosai suke ita da miman saboda sun san bala'i da za su fuskanta idan har baban su ya gani sannan uwa uba ace shi arif ya gujeta bata san wa zai aureta haka ba.
Sadda su balki suka iso afifa tana sallah daga zaune bisa gadon asibitin.
Hankalin iyayen ya kwanta da suka yi karyan tun dazu motan ya buge su.
Kwanansu biyu asibiti suka dawo gida tana dingisa kafa shiyasa ko washe garin faruwan abun balki bata gane abunda ya same diyarta ba.
Wayar gari akayi arif ya kwashe duka kudin bala na banki ya gudu ya kuma ajiye mashi wasikan ce wa baya auran afifa.Bala sai da ya kwanta asibiti sbd tashin hankali domin satar kudin bai kai mashi sosai a zuciya ba irin fasa auranta da ya ce ya yi.
Afifa da labari ya zo mata ji tayi kamar ta yi hauka ta shiga tsananin damuwa sbd tana bala'in kaunar arif ga bakin tabon da yayi mata.Bala ya fi wata daya kwance a asibiti shiyasa balki bata lura da rashin lpia da afifa ta ke ba irin na masu ciki hankalinta duk yana wurin bala domin abu biyu ke son hade masa ciwon HIV daman bai son damuwa to sai gashi jininsa ne ya hau sosai aikuwa ciwo yayi masa sallama.
Dakyar su talle suka kwantar mashi da hankali ya nuna mashi ai indai yana da kudi samar ma afifa miji bai da wuyar samu.
Ya je neman arif a gidan da yake kwana amma aka ce ai ya saki hayar gidan ya tafi kauyensu.Bala har kauyensu yaje nemansa da yan sanda amma dakyar ya gano garinsu arif da gidansu sbd bai taba zuwa ba iyayensa suka ce bai dawo ba.Iyayensa sun ji tashin hankalin abunda ya aikata musamman mamanshi da tasan dalilin da ya saka ya aikata bata taba tsammanun daman wannan danyen hukunci zai dauka ba.
Da yan sanda za su tafi da babansa ammma bala ya ce a kyalesa duk daren dadewa ai zai dawo dan haka zai saka a kama shi.

YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
Non-FictionLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...