KISHI BA DADI

440 33 1
                                        

👨‍👩‍👧‍👦ZAMAN YA'YA👨‍👩‍👧‍👦*Based on true life story*
   *Story and written by Mmn Muhibbat Abdullah*
Vote me on whattpad@Mmnmuhibbat

Dedicated to *Taskira Members*
I dedicated this page to Yan uwan juna grp especially my Aminiyas&My namecy Maryam ibrahim(yee 💃🏻💃🏻na koya mata krtun novel🤣)

Fatima Aminu (Maman madina)kullum comment dinki na daban ne luv u dozeen dozen😍😍😍😍😍❤️
   Page 6

*** Ta ce ni kuwa maigd albashin ka nawa ne an kara muku kudi ne naga kana ta facaka da kudi haka naga jiya ka shigo da kudi cikin leda ko na mutane sako zaka bada

Kallonta yayi yana murmushi yace nawa ne fa Allah ne ya buda mana zainab kiyi murna zaki huta sosai.

Ce mashi tai company din ne suka kara maku albashi ne😀

A'a yace mata dama ce ta samu shiyasa muma muke damawa saboda ubangida aka canza mana dan wadaka da dukiyar company shiyasa mu ma muke damawa.Yo Allah na tuba ina zakai sakaci kaima gwara ka wawusa sbd in baka wawusa ba wasu zasu zo su wawusa kudin kuma ma ai dukiyar mu ce nake diba Allah na tuba dukiyar kasa ai yan kasa ce menene dan kaima ka samu damar dibarta.

Shiru tai cikin sanyin murya tace amma maigida bai kmta ka dibi abunda ba hakkinka bane kasan illar da dukiyar haramun take haifarwa ga mutum da iyalinsa kuwa?

Bata fuska yayi ya ce ban gane dukiyar haram ba ince maki ta yan kasa ce kice haramun😒

Murmushi tayi tace kwarai maigd yan kasa ai suna da yawa wanda suke aikin gobnati kalilan ne tou me yasa mutum daya zai handame dukiyar al'umma da yawa kaga hakan haramun ne domin kuwa ba haka akai yarjejene da kai ba lokacin aikinka sannan kayi rantsuwa zaka rike amana amma daga baya kayi ha'ince kaga yan kasa da kai da wanda ba su ma samu halin zuwa aikin ba kaga kun tattate kason su kum cinye sannan ita dukiyar gobnati domin ayi ma yan kasa aiki da ita ne bawai a raba masu gida gida.

Bata fuska yayi ya ce ke fa zainab matsala gareki mata nawa ne suke son Allah yakai mazajen su matsayin da nake kai domin suma su mure kamar yadda kike yi ke komai sai ana zancen lpia sai ki rika ma mutane wa'azin lahira kuma waya gaya maki kafin in mutum ban tuba ba.

Murmushi tayi tace maigda wa'azi dole ne saboda so nake in kama hannuka mu shiga aljanna tare dakai kuma wannan wa'azin kai ya kamata kai mani shi sbd kai ne Alllah ya ce "
*Ya ku wanda kukayi imani ku tsare kanku da iyalinku daga wuta*
Tou maigida ka kawo su dukiyar mutane ka ciyar damu da haramun taya zamu tsira ran kiyama ni da kai sannan ka tuna hadisin Annabi s.aw  da ya ce " *Duk loma daya ta haramun tana kwana arba'in a jikin mutum ba'a amshi ibadar ba* Sannan ya kara da cewa " *Duk jikin da ya ginu da haramun bazai shiga aljanna ba* " Sannan a wani hadisin na goma  da aka ruwaito Annabi sa.w ya na bada labarin *wani mutumi da yake tafiya cikin sahara sai wuyar rayuwa ta same sa sai ya daga hannu yana rokon ubangiji yana ya rabbi!ya rabbi!! ya rabbi!!! Amma ubangiji bai amsa mashi addu'arsa ba sbd abincinsa haramun ne abun shansa haramun ne kuma tufafinsa haramun ne*
Tou kaga maigida idan ka ciyar da mu da haramun ta ina zamu roki Allah ya yafe mana bare kuma idan munje lahira mu iya kallonsa ya yafe mana .

Shiru talle yayi maganarta ta sosa mashi zuciya amma kuma son duniya da son gina rayuwa mai dadi ya rufe masa ido da amsar gaskia sannan kuma yana gani ai yana da lokaci a gaba ya tuba idan ya gama gina rayuwansa ( *hmm mutuwa bata sallama in zata zo bata aiko dan aike balle mutum ya shirya mata tana iske mutum a kowane lokaci a kowane hali ta dauki mutum da ayyukan da yake aikatwa bamu da lokacin cewa bari mu jingirta tuba domin bamu da tabbacin za'a wayi gari tare damu Annabi sa.w.yace idan ka wayi gari  kada ka saka ran zaka kai marece ida. Ka kai marece kada ka saka ran zaka kai dare in ka kai dare kar ka saka rai zaka kai washe gari to mi muke jira da jinkirta tubanmu* )

Shiru yayi ce wa yayi wai ke ina kika koyo wannan karatun ne hala kin fara shiga cikim mutanem masu kafirta mutane da tsananta ma mutane wurin addini  Allah (S.w.a)fa mai yafiya ne ga bayinsa duk laifin da kaima Allah yana iya yafe maka shirka kadai ce bai yafewa.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now