MUNAFUKIN NAMIJI

299 31 0
                                    

👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👦ZAMAN Ya'Ya👨‍👩‍👧‍👦
    *Based on true life story*
*Story and written by Mmn Muhibbat Abdullah*
  Read on Whattpad@Mmnmuhibbat
Dedicated to taskira members
I dedicated this page to you my Aminiyas Maryam ibrahim❤️❤️❤️

Page 7

***** Washe gari aka sha walima(budan kai)kamar yadda aka saba dangin amarya gaje suka kaita amana wai wurin balki,amma sai kalamansu baiyi kama da na wanda suka kawo amana ba dan a gadarance suke magana cikin masifa da isa.

  Yayar gaje ce ta fara magana wai ga Amarya dai nan sun kawo ta shigo gidanta yan bakin ciki sai su yanke jiki su fadi kuma wlh duk matar da tai kuskuren taba masu kanwa zasu kira yan uwanu yan daba su daka mace a cikin gidanta.

Wata kanwar balki ce tai saurin tararta tace aiko kunyi kadan kananun yan iska wlh aunty nan gani nan bari kuma duk mahaukaciyar da ta kuskura ta taba mana yar uwa zata gane kurenta.

Ganin fada zai kaure tsakaninsu ya saka zainab ta taka masu burge tace ku kuwa bayin Allah ba abunda ya tara mu kenan anan ba.

Balki ce zatai magana zainab ta taushe ta,ta  hanyar kallonta da ido alaman kiyi hkr.

Dangin miji balki me suka gabatar da al'adan budan kai yadda aka saba suka bada kudin sayen bakin amarya kamar yadda aka saba.

Zaune take tana jiranshi bayan yan biki sun watse taga ko zai shigo mata sallama amma shiru bai zo ba har bacci ya fara fisganta domin kuwa daman zainab da zata tafi ta kara dannar mata kirji da kalamai masu dadi sannan tace kada ta dauko tunani da damuwar kishi ta saka ma kanta idan taji abun ya isheta ta yi nafila ra'aka ko 2 ce zata samu sauki cikin ranta.Ta ce babu dalilin da zai saka shi yana can yana murna da amaryarsa ke ki hana kanki bacci a banza da tunani masu bata rai dan haka da taga bai zo ba alwala ta daura tayi nafila ta jawo alqur'anta ta fara karantawa har bacci ya dauketa ma bata sani ba (Asuba ta gari uwargdn bala yau da balki ta burgeni)

****Shi kuwa bala angon rawar kai ya saka ma bai fara biyowa dakin balki ba nufinsa ya fara shiga dakin amarya sanna su shiga dakin balki tare.

Da sallama ya shiga dakin sbd daman tuni su Talle sukai sanyen bakin amarya da abokanta sun koma gida shi ne dai sai yanzu ya karaso da zumudinsa ya shiga dakin tana zaune tasha kwalliya.

Magana yai mata akan tazo su je ma balki bankwana yatsina fuska tayi tace waii ita ta gaji haka ya biye mata suka ciyar da juna kazar balki sai da aje ta sukayi.

Babu wata sallar nafila da ma'aurata ke yi dan neman Alherin Allah da neman tsari daga shaidan da shaidanun mutane sbd samun zaman lpia da sukai abunda ya aura dan shi yake ta ma zumudi itama Gaje ba wani damuwa daman tayi da sallah sosai ba.

Kamun farko da Allah ya fara ma bala shi ne Gaje is not virgin yayi tunanin zai ma Allah wayau ya gama watsewarsa da uwar wani matar wani diyar wani yace zai ma Allah wayau ya auro tagari ya aje cikin gida.Ranshi yakai matuka wurin baci ture ta yayi yana tmbyar ta garin ya zatai mashi haka (nace hmm gwano bai jin warin jikinsa sai na wani)

Kuka ta saka mashi tana mashi rantsuwa she was been rape by yaron neigbour din su tsaki yayi ya fita palour ya zauna.

Tunani yake taya Gaje zatai mashi haka ga shi yana bala'in sonta da yau sai ya saketa(daman haka suke zinar mace itace laifi wrn su amma taso Ado ce Allah ka raba mu ado da zunubi)

Gaje kuwa tana daki tana tunani ya akai bala ya gane she is not virgin while she use so many aphrodisiac(kayan mata) dan taga ta koma virgin har wani ta saya maida tsohuwa yarinya ta ya akai ya gane tayi yawo daman tana ta damuwa kar ya gane yayar ta ce tace mata shi kansa wayasan matan da yake bi dan ita ta dan bi maza shikenan duk sai ta damu kanta kuma g kayan gyara nan ta gyara jikinta  har zargi bala kadan ya fara shiga ranta taya akai ya gane haka farat daya ko dai yana bin mata ne sai ta tuna yana da mata fa she is not his first wife.Mikewa tayi dga saman gadon taje parlour dan tayi mashi kukan kissa.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now