SHARRI DAN AIKE NE

300 31 1
                                    

  👨‍👩‍👦‍👦*ZAMAN Y'AY'A👨‍👩‍👦‍👦
(*Based on true life story*)

Story&written by *Mmn muhibbat*

Vote on wattpad _Mmnmuhibbat_

Dedicated to *TASKIRA MEMBERS*

Edited by *Khadija Manga*

_Wannan page  naki ne phareeder kanta tskira HBD Allah ya karo shekaru masu albarka.Allah ya bar kauna ina godia_

Page 27

##Balki duniya ta samu domin kuwa bala ya wadata da komai na more rayuwa kwanciyar hankali ta rasa domin kuwa tunda ta ji cutar HIV ta shigo tana kisa hankalinta ya tashi, matakin da ta daukar ma kanta shi ne gujen ma bala daga shimfidarsa wai dan kar ya goga mata HIV.
Bata san san wannan kuskure ne babba ba da kashe kai da gangan wai da sunan zaman ya'ya domin bai halatta ga mumuni ya ga abunda zai cutar da shi ya tsaya a wurin.

  Shi ma da farko ya ji tsoro amma jin cewa an samu maganin da bama za'a gane mai cutar ba a ido sai dai idan an fada ma mutum ya saka shi ya ji hankalinsa ya kwanta amma duk da haka ya guji bariki bai san aikin gama ya riga ya gama ba.

Ciwo ne ya kama bala da suke nuna alamomin kamuwa da cutar HIV ganin alamomi sun bayyana ya saka asibitin su ka ce ayi masa awon HIV da farko ya musa ya ki ganin an tilasta shi ya saka shi yarda a yi masa awon jinin da result ya fito positive ya nuna.

Bala ya girgiza da jin wai cewa yana da HIV dan haka ya shiga tashin hankali ba na wasa ba.

Balki tayi tambayar duniyar nan amma yaki fadi mata abunda ke damunsa.

Wani abokin barikinsa ne ya kawo masa ziyara domin kwana biyu ya daina ganinsa a sabon layi, fada mashi ciwon da ya samesa yayi yana kuka.

Dariya abokin ya fashe da ita wanda ya kular da bala har ya fara bala'i ce mashi yayi yi hkr wlh dariya ka bani to shi ne me?wa ya gaya maka HIV na hana bariki ai kaima baka san waya goga maka ba dan haka kaima sai ka goga ma wani dan ayi mutuwar yawa nima nan da ka ganni yanzu 5yrs kenan ina da HIV  amma ba abunda na fasa kai ba ma wanda yasan ina da ita wlh ko iyalina shiru nayi abuna da in daga masu hankali a banza kasan mata in suka  tara yara ba inda za su to fada mata na me kuma.

Bala ji yayi hankalinsa ya kwanta kwarai da shawaran abokinsa yo ashe shi a da zai kashe kansa a vanza tun lokacinsa bai yi ba atou wlh yanzu yaji sa'ida cikin ransa dan haka bariki bai barinta sai randa ta ita barikin ta yada su.

Tabawa(kashewa) sukai da abokinsa ya ce sai na ganka indai zaka kiyaye shan maganinka akan lokaci ba mai gane ma kana da wannan cuta.
   
   Haka ya koma sha'aninsa ba tare da ya lura cewa Allah ya bashi dama ta farko dan ya tuba ba,bai yi amfani da wannan daman ba sai ya zabi ya kara durmiyawa cikin halaka ta hanyar cutar da iyalinsa da shi kansa da cutar da matan da mazan da suka ketare iyakokin Allah.

    Balki kuwa hankalinta rabi a kwance rabi a tashe domin dai tasan abunda yake aikatawa bayan idonta kullum cikin Zullumi da damuwan kar ya dauko masu cuta ya goga mata.Ta gefe guda kuma tana mamakin irin takuran da yayi ma afifa ya matsa mata iyakar matsi bata da qawa ,ba su zuwa ko ina bata hulda da namiji ko abokan haihuwanta ne idan kaga ta fita to tare da mamanta ne saukinta daya da mima kanwarta ta fara girma sai ya zaman ta samu qawar hira amma badan ita ba da ciwon kadaici ya dameta sbd ko makaranta ya hana ta mu'amala da mutane ya saka masu saka mata ido a makarantar ba tare da ta sani ba.

***†*"******†****†************
   Rayuwa tana ta tafiyar  masu kwanakin su yana karewa amma bala ya ki hankalta ya gane duniya budurwan wawa ce.Ciwo balki ta kwanta aka rasa abunda ke damunta duk wani test an mata amma ina an kasa gane abunda ke damunta karshe likita ya ce ayi mata awon HIV.Fada ta kama yi ita Allah ya raba ta da wannan mummunar cuta dan haka ba mai mata awon HIV dakyar ta aka samu ta yadda sbd tana jin jiki aikuwa ko da likita ya kawo result dinta ta girgiza iya matukar tsorata da ta ji ciwon da ke damunta kuka ta saka tana zagin bala tana mashi Allah ya isa dan tasan shi ya dauko mata wannna ciwon wurin neman matan shi na fitina.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now