👨👩👦👦*ZAMAN Y'AY'A👨👩👦👦
(*Based on true life story*)Story&written by *Mmn muhibbat*
Vote on wattpad _Mmnmuhibbat_
Dedicated to *TASKIRA MEMBERS*
Edited by *Khadija Manga*
Page 29
### Dole Ma'u ta yi shirin komawarta gida bayan hajiyarsu mudi ta zo jinyarsa,Hajiyarsa ta ji bakin cikin abunda ya same haneefa ta ce tun farkon abun nan da mayi maku magana sai kuka nuna ai nai ma diyarku kazafi amma da yake Allah ne gashi ya nuna maku ai danka ko bai aikata abu idan an fada maka ka yadda kada ka gwaleshe wanda ya kawo maganr danka gabanka sbd zaka saka yaron ya raina mutane ya kuma samu kwarin gwiwar aikata son zuciyarsa tunda daman yasan ko wani ya gani ko ya fada ba yadda zai ba ta ina mutum daya ke tarbiya Ma'u tarbiyan yara nan nake ne na makwabtanki ne na mutanen unguwa ne Amma da yake Allah ya kawo zamanin da iyaye ba su son laifin yaransu shiyasa zaki ga ba wanda yake gaya ma wani gaskia bare ya hukunta yaron kai ko yan uwanku ne suka hukunta maku 'ya'ya haushi kuke ji ina amfanin rayuwa haka.
Ma'u shiru ta yi cike da nadama da dana sani ta ji kunya matuka gashi yanzu tashin hankalinta yadda zata iya rayuwa a gidansj domin ita daman bata cikin matan da idan sun samu arziki ko dakin uwarsu su gyara bata cikinsu ba ruwanta.
Hajiya ta ji tashin hankali lokacin da ake gaya mata ai auransu ya kare fada ta shiga yi ta ce yana hauka ne ya zai sake uwar yaransa a wannan gabar su fa maza wasu ba su da zurfin tunani ba su damuwa da halinda yaran su za su shiga a lokacin da suke sakin mata sudai da mace ta yi laifi ko ta fita ransu sai saki ba su tunanin makomar yaransu.
Ganin yadda ta dauki dumi ya saka Ma'u gaya mata gaskiar lamari,mutuwar zaune tayi tana jinjina jahilci da son zuciya irin na danta da matarshi lallai sun jefa rayuwam yaransu cikin fitina.
Kuka ta saka tana yanzu shikenan tana da rai amma suka aikata bakin shirme haka me ke damunsu,yanzu yaran guda nawa ne shegu.Maimata mata abunda malamain da yayi musu fatawa ta yi hankalin hajiya ya dan kwanta amma idan ta tuna cewa auran danta da matarshi ya zo karshe sai ta ji ba dadi ga laluranshi gata hamza jiya zaune suka kwana sbd haukan da yake tuburan,dole sai da sani y kira wani abokinsa likita akaita mashi alluran bacci.
Hajiya ita tsoronta kar haukan ya tashi ya karya kofar dakinsa ya kasheta a banza tunda daman haushinta ya ke ji.Haneefa tunda abun ya faru take boye ma mutanen gidan kullum tana dakinta ta rufe kanta abun duniya ya dameta sosai da sosai,ba abunda ya daga mata hankali irin jin cewa babansu yai ka mamansu saki 3 saboda ita ba ta yi Allah wadai da halinta da ya raba auran da tun kafin a haifeta aka kullasa,kuka take sosai da sosai tana nadama.
Tana zaune a dakinta tana lissafin yadda zata iya rayuwa a gidansu da ko katifar kirki babu saman gadon mamant tana jin tun wasu kayan dakinta da ta bata kwance lokacin ta haifi Amira ita zatai da rayuwanta yanzu kuma kayan gadonta ba inda zata saka su ko ta dauka sanna wa ma ya sani shin ya bata kyauta ko a'a.
Hada kayanta tayi tsab Sani ya sauko mata da su,bankwana hajiya sukayi da hajiya tana ta sharar kuka ta so ta zauna zaman 'ya'yanta amma tana tsoron halakar da zasu sake jifa kansu idan Mudi ya warke da ace masu ilimi ne da tsoron Allah sai shi ya bar mata gidan ya koma wani ya zauna ita kuma ta rike yaranta dan babu dadi ace mace ka aureta tun kuruciyarku sannan ace da rana tsaka kace ta bar maka gidanka da yaranta ai ciwon zai mata yawa ,shiyasa musulinci ma ya ce ayi mata hasafi amma dai yanzu dole idan ya samu sauki ta saka shi yayi mata wani abun alheri idan yana da kudi tunda an kore shi a aikinsa.###########################
Mai keke nafef na sauketa a kofar gidansu kunci ya rufeta saboda yanayin gidan da tsarinsa irin na mutane talakwa ne sosai kuma bata taba tunanin zama zai dawo da ita ba gidan nan kusa da ta gyara shi wlh lokacin da take ganiyar samun kudi a gidan mijinta.Yanzu dan Allah haka abokanta manyan hajiyoyi za su zo su ga wannan gidan gaskia da sake zata kira sani ta ce kar a gaya ma kowa an saketa.

YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
NonfiksiLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...