👨👩👧👦ZAMAN YA'YA👨👩👧👦
*Based on true life story*
*Story and written by Mmn Muhibbat Abdullah*
Vote me on whattpad@Mmnmuhibbat
Page 5Salma kuwa rayuwa tai mata tsanani saboda yanzu sule yayi wata 7 bai zo ba dan abunda ya bar mata daman ko na 1month bai kai ba kayan Abinci kuwa daman masara ce ya auno mata sai gero suma sun kare tuni .
Kitso ta fara dan ta samu abun rufa ma diyanta asiri saboda yanzu salma ta sake haihuwar yara biyu yanzu yaranta 3 ne kuma duk yan mata Allah ya bata shiyasa yanzu take kitso dan ta samu abunda zata rufa ma kanta asiri duk da sule wani zuwa da yayi yai ta bala'i wai tana tara mashi mata cikin gida ana gulma shi bai son wannan sana'ar (😏😏Sai kace kudin kayan bukata na gida yake bata)
Haka dai innarsa tayi ta bashi hakuri da baki domin tasan cewa sana'ar ita ce take rike salman saboda son zuciya bata iya kwatanta ma danta ya rika dawowa gida da wuri ba ya daina shafe watanni kuma bata gaya masa yadda salman take shan wahala ba wurin kula da gidan ba .Domin kuwa duk wanda yaga salma yasan tana cikin wahalar rayuwa sosai duk ta lalace shi kuwa Azzalumin yayi kiba yayi kato kamar bijimin sa.
Wani zuwa da su balki sukai mata ne suka lura tana cikin wuyar rayuwa shiyasa su ke taimaka mata da abunda Allah ya hore masu domin su ba laifi suna cikin wadata.Har zainab take dan kwatanta mata me yasa baza ta kai sule kara ba wurin iyayen shi ayi mashi fada ya rike dawowa gida da wuri ba sabd wahalar da take sha yayi yawa ga yara.Balki ce tace a'a ai zaman aure dan hakri ne tayi ta hakuri Allah zai saka mata da sannu sai yaga abunda ya shuka (hmm da salma tasan inda Allah zai saka mata da ta saka waliyanta da nashi sun mashi magana)
Haka dai zainab ta bata shawaran ta fara sana'ar kitso ko wanki da guga kasancewar salman ita kanta duk sauran yunwa ce ya saka bata iya wankin sai dai kitson shi ne ya zo da wannan bakin kilbibim wai ana tara mashi mata a gida suna gulma.Yaran ta ne zaune suna wasa amma rabin hankalinsu naga kofar matar wan babansu da take soya kifi zata yi abinci da shi hankakin su ma kai sabd rabon da su ga nama ko kifi sun manta gwara nama tun na sunan karamar kanwar su ,sun ci wanda itama kanwar yanzu one year gareta sai na layya suke saka rai in anyi za'a basu sadaka.
Ita kuwa salma tana daki ciwo ya ci karfinta ga shi daman kitson da take kwana biyu bata yi ba sabda jikin ba lpia .Bata da kudin zuwa asibiti shiyasa take kwance gida ko da taima inna magana ko zata kaita asibiti dan Allah tun da innar ba laifi tana sana'a kuma sauran yaran ta suna kawo mata kudi sai ce maga tayi ta cika raki meye na zuwa asibi dan masassaran da take ta jika ararrabi da sabara tasha zata warke haka salma ta jika take sha amma abun ba sauki saj wurin Allah.
Haka matar wan mijinta ta shigo ta aje mata kwanon abinci tana mata sannu da jiki ta koma sashenta da gudu yaran salma suka saki wasan da suke suka taho cin abincin.Bar masu tayi domin tasan suma yunwar suke ji ce masu tayi dan Allah su rika bama kanwar su domin itama sai kuka take na yunwa ba ruwan nono.
Take suka cinye abinci daman hannu baka hannu kwarya suke cin sa bayan sun gama tashii sukai suka koma wasan su karamar kuma ta kwanta jikin salma zatai bacci.
Salma na nan kwance cikin ciwo ta mike zata tafi toilet ta yanke jiki ta fadi.Bata farka ba sai a gadon asibiti taga mamarta zaune sai kannen ta mata har da amaryar da za'ai ma biki ba da jimawa ba kallon su tayi cikin kasala.Mamarta ce ta taso da kanwarta hafsat suka tada ta suka kaita toilet tayi wanka da alwala ta fito suka shimfida mata prayer mat ta kabbara salla dg zaune sbd ashe ta kwana biyu a kwance.
Ashe hafsat kanwar ta da za'ayi ma biki taje rabon abotta(gayyar kawaye) a unguwarsu salma tana da kawa shine fa biyo gidanta su gaisa shi ne ta zo ta iske ta kwance ta suma shine ta fita ta samo taxi matar wan mijin salma da wasu neigbours din salma suka taimaka mata suka shigar da ita a taxi din ta dauke ta sai general hospital.
Dakyar ta samu aka basu gado saboda salma na cikin hali sannan ta juya ta tafi gida domin gaya ma mahaifiyarsu.
Bayanin da Dr yai masu ya bata ran mamar salma saboda fada yai tayi yace yunwa ce ta kama ta ga damuwa shiyasa ciwo ya isheta fada ya rikayi yana cewa ina mijinta?
Mama tace ai baya nan yana abuja sai dai a rubuta mashi wasika sabd lokacin ba waya ke da akwai ba.Shima mahaifin salma da yazo yaji tausayin salma sabda yadda ta rame ta lalace cewa yayi idan an sallami salma su dawi gida da ita har sai mijinta ya dawo.
Bayan ta gama salla abinci suka bata taci wanda rabonta da irin shi tun zamanin amarci sai kuwa in taje gidansu da yake babansu yna da rufin asiri ba laifi.
Sai da salma ta share sati 1 sannana aka sallameta sabd har wani dan kumatu tayi sabd samun kulawa da take daga wurin iyayenta.
Gidan ta taso wucewa saboda yarant tayi kewarsu kwana biyu basu zo ba sabd makaranta sai karamar ce kawai hannunta.
Babanta ce wa yayi bazata koma gidanta ba sai sule ya biyota an musu sulhu sabd zai yadda da auran yunwa ba.Kuka ta kamayi saboda tana tunani ina zata bar yaranta gashi shima sulen ba damuwa yayi da yaran kuwa ba shiyaaa ba mai jawo nashi a jiki.Da kukanta da komai baba y saka su cikin taxi sai gida.
Haka ta yini gidan jikinta sukuku sabd tunanin yaranta da baba yaga yadda take sai ga bashi tausayi kudin taxi ya bama hafsat taje ta dauko su.
Da murnan su da komai suka biyo hafsat daman sunyi kewar mamansu tana zaune ta gansu suna shigowa da murnan ta tare su.Haka suka zauna gidan su salma da yaranta har aka fara bikin hafsat sule bai zo ba mamar shi kawai tazo itama sau guda wai tazo bada hakuri baba yace ai ba ita tai laifi ba sule ne a bari gazo ya amshi laifinsa shi ne tai zuciya ta koma gida wai kawai suna son zuga yar su ne dan kar ta zauna gidan mijinta to ai sai tayi ta zama gidan ubanta in sun gaji sun maido ta ai mazaje tsada suke yi dan haka da kafarta zata dawo.
Shi kuwa sule yaga wasikar salma bata lpia tun sati daya da aka rubuto ta kawai haka nan bai niyya zuwa ba sabd kar ya bar shagonsa ciniki ya wuce sa ida ya samu mai zuwa katsina ya bada sako a kawo mata.Sule baya neman mata kawai tsabr cuta da mugunta ce irin na wasu mazajen ne shi mace bai dauketa a bakin komai ba sai kawai wadda zata mashi bauta ta haifa masi ya'ya kuma shi abunda ya kara bashi haushi har yanzu salma taki haihuwar da namiji wanda zai gaje shi a kasuwanci yanzu wazai rika tsare mashi shago.Dadi yake ci bana wasa ba shiyasa gake ta mula kiba abunsa ba ruwansa da tunanin wani hali iyalinsa suke ciki.
Haka ya samu wani da zai je katsina ya bashi kudi da baza u wuce na sati 2 ba yace a kaima salma da aka kawo kudi daman inna lokacin tana cikin bukatar kudi zata sayi wata akuya mai haihuwan yan biyu aikuwa ta amshe kudinta ta sayi akuya akan cewa idan ta samu wasu kudin zata kaima salma duk da ma ai salma na gidan su bata bukatar wani abu(kuskuren da wasu iyayen miji da mijin ma suke aikatwa wai lokacin da mace take gidansu ko ciwo ko zuwa haihua shifa gani yake wani ai an hutar dashi bai komai kuma hakkinsa ne ko tana gida ya kaimata abunda zata ci ta kula da kanta ba hakkin iyayenta bane ciyar da ita kuma ko ba ta sayi abinci ba akwai wani abu da zata bukta taya saya ga kuma yara ko rabuwa ce sukayi hakkinsa ne ya kula da yaranshi da uwarsu ya rabu bada su ba )
Haka sule sai da ya share 2month sannan yazo kuma ko da yazo ya iske salma bata gida bala'i yai ta yi innarsa na zuga shi har da cewa ai da ta kaimata kudin shi kin amsa tayi tace a maido masa (ita kuwa daman bata samu kudin akuyar d ta ranta bane tana tsoron a tada magana ace bata kai ba)
Aikuwa haka yaa zuciya har yazo ya koma bai je ba wurin salma.***********#*******
Ita kuwa Zainab zaman su da talle ba laifi domin kuwa yana kokarin ya boye ma zainab halin da yake ciki.Zaune suke tana son tambayar talle wata muhimmiyar magana amma tana tsoron yadda zai fasarata itaa kuma Allah ya sani baza ta so Talle ya ciyar fa su da haram ba domin tana tsoron Abunda haka zai haifar.
Sai da ta bari ya gama cin abinci y kishingida suna hira ta sako mashi zancen
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
Non-FictionLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...