RASHIN GIRMAMA NA GABA

283 32 0
                                    

👨‍👩‍👧‍👦 *ZAMAN YA'YA*👨‍👩‍👧‍👦
*(Based on true life story)*

Writing by *Mmn Muhibbat Abdullah*

*_Dedicated to taskira members_*

*_Edited by KHADIJA MANGA_*

*_INA GODIA MANGANMU_*

_Ina mika gaisuwa ga duka members din Zaman ya'ya musamman maman madeena ina godia_🥰🥰

*Page* *23*

    Bugawar kofa da ake ne ya saka yayi saurin rufe sytem din shi da yake kallon porn da ita, Waye? ya ce ranshi na baci dan ya kai kololuwa wajen sha'awan..

Sani ya ce ni ne wai uban me  kake cikin dakin ne da baka son ka bude ne?

Dan Allah kada ka ishe ni da masifa fadi abunda zaka fadi ka kara gaba ya fada a gadarance domin kuwa hamza wata irin tashen balaga ke cin sa ta rashin kunya ga shaye shaye ga kalle kallen fina finan da basu dace ba. Daman shi saurayi idan yakai matakin balaga jin sa yake dai dai da kowa, musamman idan ya samu iyaye masu sakaci kmr su ma'u da suke bama yaro duka yanci a lokacin da bai kamata ba suna ganin gata ne a sake yaro yayi abunda yaga dama ba'a bibiyar lamarinsa. Dakinsa, abokansa,wayoyinsu da sytem na su aga me suke kallo a shiga browser na su da su goggles da gallery na su aga me suke ajiyewa sbd duk yadda bamu tunani wasu matasan waya da sytem ya taka muhimman rawa wurin bacewan tarbiyansu.

Ce mashi yayi mama na kiransa.. banza yayi da shi domin lokacin babu abunda zai saka shi fita waje domin Tabb as za'a gane halinda yake ciki.

Ganin hankalinsa na tashi a banza ya saka ya jawo wiwi dinsa ya shiga banka dan ya samu kansa ya dauki caji ko ya huta domin tukunna bai fara neman mata ba, domin kuwa bana ya shiga level one shine aka sai masa sytem sbd ya samu saukin karatu kmr yadda ake yi ma matasa a shekarun baya sbd rashin zuwan waya mai browsing shiyasa duk aka saya musu shi da su sani.

Sani zuwa yayi ya ce ma ma'u yaki zuwa, se cewa tayi a kyalesa  daman wai abinci ne za su ci tunda yaki zuwa shi ya sani cikinsa..

Ba ruwanta da bibiyan lamarin yaranta, a rana idan ba lokacin dinner ba bata haduwa da yaranta sbd makaranta idan suka dawo ba islamiya suke zuwa ba musamman hamza da yace wai shi ai ya girma da zuwa islamiyya haba haka kawai sai a ganshi yana saka uniform cikin shaqiyanci.. Bata damu ba ta kyalesa bata tursasa shi ba kusan daman yawanci iyaye namiji da yakai s.s class ya yi bankwana daga islamiya kuma a hakan muke rayuwa bamu damu ba mace ce ma wata har ta gama secondary sch tana sauqa ta gama zuwa itama a ganinmu wai ilimin ya ishe ta bamu san Annabi (s.aw)yace mu nemi ilimi daga farkon rayuwanmu har mutuwarmu ba. A kullum idonmu yana rufewa ga tura yaran mu neman ilimin duniya sbd idan sun gama su samu aikin yi su samu kudi tou yanzu yanayin kasar ya canza. Akwai wata waka da ake ma yara wai *EDUCATION IS A KEY TO SUCCESS.* To yanzu leaders din mu sun canza padlock din _we own the key_ but an canza padlock.
Shiyasa mu nemi ilimin addini sbd lahirarmu sbd ba musan yaushe zata zo ba, mu nemi na boko sbd zaman duniya badan muyi aiki ba idan aikin yazo alhamdulillah idan bai zo ba kuma mu kama sana'a .

Haka ta mike ta shige dakinta sbd daman da ishaa take hayewa sama su hanifa da bari suna kallo daman a saman dakinta da na su hanifa da amira sai dakin mudi yana da wani a kasa daban wanda ke hade da falonsa, Sai dakin su Sani da hamza da daki guda suke kwana su 3 amma sbd bakin halin hamza sai ya canza daki wai bai son kwana da kowa munsharin su na damun shi haka suka kyalesa da sani da hanif suke kwana tare hamza shi daban yake kwana.
Kwana yake kalle kallen porn  tunda aka sai masa system din abun nashi ya lalace sbd yana da yancinsa cikakke da iyayensa suka bashi ubansu yana can sakarcinsa haka ita kuma ma'u da an gama dinner ta haye sama ba ruwanta da bin dakunan yara taga wace rayuwa suke yi me suke yi bare akaita ta biyo su tsakar dare taga wake bacci wake sakarci.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now