👨👩👧👦ZAMAN YA'YA👨👩👧👦
*Based on true life story*
Story&written by Mmn muhibbat
Vote on wattpad@_MmnMuhibbat_
Dedicated to taskira membersEdited by khadija manga
Wannan page din naki ne mai sunan sister ZAINAB ABDULLAHI ROGO(ZEE ROGO)❤️❤️kiyi yadda kike so da shi.
Page 25
An sha bikin su samha salma da yan uwanta sunyi bajinta domin dai sule daga kayan gado bai kara komai ba ita ce kayan kitchen da kayan iyayen miji da sauran hidima su hafsat sun yi rawan gani sosai.Dangin sule sai tsogami suka raba daman haka biki yake ko yaya kayi sa sai wani ya ce kayi masa ba dai dai ba.
Amare a farkon zaman su abun gwanin ban sha'awa amma da zama yayi zama halin kowa ya fito.Shi umar Allah yayi shi mutum ne mai gori ga rashin rike sirri domin ko abu kadan tayi masa sai ya fada ma abokansa ko danginsa ita kuma daman a gadarance ta shigo gidan dan haka komai zai mata sai ta rama ya rainata ya raina iyayenta ga gori da ya zo ya taradda da abu ya kare ta ce babu sai ya hau bala'i ko ta kaima iyayenta.Sai ya ce" daman matsalar auren makwadaita kenan idon su na kan abunda ka saya ka aje ma yar su.
Yau ma kaji ne ta ce ma shi sun kare guda biyu ne ya sawo tun wancan satin tana manage amma baya gani cewa yayi ai dole daman baza ta tattala mashi ba tunda gida babu dole anzo an ga nashi a hau masu cin yunwa.
Samha ce wa tayi matsalar auran matsiyaci kenan gori shi matsiyaci ko ya yayi arziki sai ya nuna halinsa ta hanyar nuna karanta da gori.
Mari ya wanka mata aikuwa bata yi kasa a gwiwa ba ta rama daman ta fadi baza taba saurara ma namiji ba idan ya ce mata suma sai ta ce mashi mutuwa.
Tsaye yayi ya sake baki yayi mamakin rashin kunyar samha daman haka take lalle ce wa yayi zai bugeta ta ce bismillah vata hana sa ba amma ya kuka da kansa duk abun ya biyo baya.
Tsorata yayi, amma ya dake ya nuna mazantaka. Dan haka borin kunya ya kamayi yana fita daga gidan ya ce mata zata gani bari ya dawo ta ce Allah ya maidosa da alheri.
Ta kasa tsaywa ta kwantar da hankalinta ta fahimcesa su xauna lpia shima ya kasa kwantar da hankalinsa ya fahimceta sai bakin gori da dan banza tonon asiri kullum maganarsa na waje daman duk ma'auratan da suka ce wai halinsu ne kai maganarsu waje to ba abuda ke saurin zubar da mutunci irinsa ga shi yana saka dangin miji ko na mata su tsani ka/ki.
Ita kuwa farha tana can suna zaman lpia daga farko sai dai matsalanshi dizgi kamar ubanta sule bai jin nauyin kunyata a gaban ko waye sai dai in bata yi mashi laifi ba ita da yake bata da baki sai dai ta shiga daki tasha kukanta ta rikesa cikin rai kmr uwarta kafin kace me ye wannan duk ta fada sbd daman ba abunda ke kashe bawa irin rike damuwa cikin rai.Hakan nan basu ji ba su gani ba suna amsa laifin mahaifinsu kuma daman ai mamansu tayi mashi addu'a Allah y saka mata to kuwa ga shinan yana saka mata kan yaranta daman ita addu'ar mace wani lokaci takan fada kan miji ko ta fada kan yaranshi,shiyasa a rayuwa kada ki rika ce wa Allah ya saka maki (Allah ya isa) gwara ki bi hakkinko wanda baki iyawa kuma ki yafe yafi sauki.
Salma na zaune yau tana tunanin abunda zata bama yaran kwana biyu ba ciniki kam daman kasuwanci ya gaji haka wata rana riba wata rana faduwa daman ga shi bayan bikin su samha ta samu kudi sosai dan kuwa ita mutuniyar mutane ce makka ta biya ma kanta itama taje kam.
Sule ya ji takaicin biyan makkan salma dan ya so ta saya mashi gida da kudin ya maido sady ciki amma tayi saurin biyan makkanta dan ita dai ko hajiar nan dai a rika ce mata ina dalili kullum tana samun kudi ta rasa inda take kai su.Su innar sule da yan uwansa da suka ji tsogami suka kama yi wai ya za'ayi ta je makka mijinta bai je ba ai sai a rika ce mashi mijin hajia.
A farko ta damu amma da hafst ta ce mata ta fita sabgar su ai makka kiran Allah ce duk wanda ya kira zai je ne idan ya ji haushi ya biya shima.
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
Non-FictionLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...