👨👩👧👦👨👩👧👦ZAMAN YA'YA👨👩👧👦👨👩👧👦
*Based on true life story*
Story and written by Mmn Muhibbat Abdullah
Vote me on Whattpad @Mmnmuhibbat
Dedicated this page to u *Zaman Ya'Ya* grps membersI dedicated this page to Maman Madina ke kike bani karfin gwiwar rubutun nan ur Comments make me smile🥰🥰🥰Luv u lodi lodi Allah ya barki da bbn Madina.
Page 8
*Kuskuren wasu matan auran akan hakkin iyayensu*#####Salma ce zaune tanan tunanin komawarta gidan sule domin zaman gidan su ya fara isarta sbd da bikin hafsat kanwarta tasha habaicin mutane musamman dangin babanta da suke tunanin auran ta ya mutu sbd tana zaune tana ma Hasfsat nasihan hkr a gidan aure kawai yayar babansu ta katse ta tace sai ki bari masu Aure su bata shawara ba wai ke da kika kaso auranki ba sbd rashin hkr yo Allah na tuba ko me akai maki ai hkr zakiyi ki zauna ko dan yaranki ku dai yaran zamani ba ku da hkr kuma laifin babanki ne da ya daure maki kugu kike zaune zaman gida yadda mata sukai yawa ai kuwa kin rasa mai aurenki.Haka kuma wasu kawayenta ma taga duk sun canza mata fuska a tunaninsu Aurenta ya mutu yanzu ita ba sa'ar su bace wasu kuma na ganin kada ta aure masu mazaje irin dai tsangwamar da wasu zawarawa suke fuskanta a ckn al'umar mu da suke kallon mace budurwa ko bazawara a matsayin mace ce marar daraja ko kuma wanda zasu kashe aure shiyasa mata da dama suna tsoron su bada shawara ko su rika fita su shiga ckn kawaye sbd suna gudun idan matsala ta taso za'ace ai sune sbd sun ki zaman aure sun zo zasu kashe ma wata aure.( *Wannan babban kuskure ne da al'umma ke yi shi aure,mutuwa,sakin,haihuwa duk abu ne da idan lokacinsu yayi sai anyi su amma mutanen suna gani su da suke zaune gidan aure iyawaesu ce ta zaunar da su ,su kuma yan mata da zawarawa gazawarsu ce ta saka basu samu miji ba akwai shirme ckn wannan tunanin kwarai sannnan kuma kuna jefa zuciyoyin bayin Allah da ya jarabta a ckn wani hali wannan kuskure ne* ).
Wurin baba taje tana rokansa akan ya aika gdnsu sule ace ya zo bikonta kallonta baba yayi kmr ya wanka mata mari amma sai ya kyaleta yace mata kin gaji da zaman gidan ne ni da ina son in kwato maki yancinki ne amma tunda baki so to ki bari idan yazo da kanshi sai a maidaki .Tashi tayi badan ranta yaso haka ba amma ba yadda ta iya ta hkr akan duk randa yazo ranar zata koma gidanta.
Innarsu da baba ya tmbyeta ko tana ma salma wani abu cewa tayi a'a anan yake gaya mata abunda da salma tace ranta vaci yayi sosai.Iske salma tayi daki ta wanketa tass sannan ta ce idan har ta rubuta ma sule wasika akan ya zo ya dawo da ita bata yafe mata ba sannan fa salma ta hkr da tayi niyyan rubuta mashi kuwa.
Bayan sati daya da wannan magana kmr hadin baki sai ga sule ya zo bikonta sbd innarsu ce wannan dawowan da yayi tace ya maidota sbd yan kudin da yake bata ya daina aiko mata da su.Baba ne ya zaunar da shi zai masa fada da nasiha amma salma ta rika leken su ta zaure ganin zata tona mashi asiri ya saka baba tashi ya ce bari ya kira ta su tafi Allah ya kara basu zaman lpia dadi sule yaji sbd baba bai masa fada ba.Gida ya shiga ya ce ma salma da tuni har ta hada kayanta ta fito su wuce ,jikinta na kyarma ta ja yaranta suka wuce haushi kmr innarta tayi ta bugunta.Haka suka koma gidansu ba wata nasiha da iyayen salma sukai masu.
####Haka kwanaki su ka ja har sule ya koma Abuja ba tare da ya sake aje mata wasu wadattun kudi ba da kayan abinci.Ita kuwa sabuwar duniya ta bude ta tara yaran mata kisto gidanta sai ya zama wata karamr majalissan yaran mata inda kowace sakarai take baje sirrin gidanta ga maganganu na rashin kamun kai kuma abun takaici yaran salma suna zaune cikin iyayen su salma bata taba ce ma yaranta su tashi ba haka zasu rika maganganu na batsa da rashin kamun kai gaban yara.Wata makwabciyarsu ce ke saida kayan mata haka ko wace idan ta saya zata zo tana rika buda sirrin mijinta ana dariya kunne yaran salma yana wurin wai a haka *Zaman Ya'ya* take yaran ba su da tarbiya ko kadan ga zagi ga sallah basu dame su ba tou daman ita kanta salma idan aka kafa majalisan tana ma mata kitso da wuya ta tashi tayi sallah sai idan lkcn bacci yayi zata hade su a mika a jimlace.Daman aikin gidan ta sakar ma babbar yar ta da yanzu take da shekaru 10 a duniya ita kuma tana can tsakar gidan ana labarin asara.
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
Non-FictionLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...