BABI NA 33

90 14 7
                                    

👨‍👩‍👦‍👦*ZAMAN Y'AY'A👨‍👩‍👦‍👦
(*Based on true life story*)

Story&written by *Mmn muhibbat*

Vote on wattpad _Mmnmuhibbat_

Dedicated to *TASKIRA MEMBERS*

Edited by *Khadija Manga*

Ni har kunyarku🙈 ta saka na rasa abinda zance amma dai ina mai bada hakuri.
   

    Tunda balki ta tafi hankalinta na wurin yarta musamman da babu caji a wayarta bikin ma a sukuku ta yi shi ba cikin jin dadin rai ba dan haka asuabar fari ta daka sammako sai Katsina,tun daga get maigadi ke gayawa mata abinda ya faru ba bata lokaci ta nufi asibitin SBD daman tasan inda Zainab take aiki,a reception da iske Al'ameen yana biyan Bill na Asibiti,sunkuyawa yayi har kasa yana gaisheta ta amsa a cikin fara'a cike da jin kunyar tare da yi Mashi godiya da addu'a bisa ga dawainiya da yake da Afifa.Nuna mata room din da su afifan suke ciki yayi ,yana mai cike da damuwa rasuwa babyn afifa domin dai yasan dole afifa ta shiga damuwa sbd ita uwa ce da dauki cikin danta wata tara duk da ga hanyar da yaron ya zo amma soyayyar uwa da ɗa a daban take.
   
   Kwance take tana tunanin babynta tana kuma mamakin yadda uwa irin ta su ke haihuwar yaran su ,su zubar a bola SBD gudun abun kunya,wa su yaran su mutu wa su kuma su tashi a gidan marayu ba dangin uwa ba na uba wannan hakkin da me yayi kama, yaro bai ji ba bai gani ba amma yana paying the price da ba shi ya aikata zunubi ba.Dafata da akai ya saka ta dawo daga dogon tunanin da take aunty Zainab ta gani tana share mata hawaye tana kuma kokarin tashin ta ta sha tea,karba ta yi tana mai kara gyara zamanta Mima na saka mata pillow a bayanta dan ta ji dadin zama,ita ma  share hawaye ta take yi SBD tausayin yar'uwarta da kaddarorin da suke ta Bin ta Babi babi buɗe kofar da akayi ya saka duk hankalinsu ya kuma ga mai shigowa balki ce ta shigo sai al'amin da brother din afifa.Kusa da ita ta zauna tana mai dafa kafaɗarta cikin lalllashe domin taga gawan baby a waje a wurin brothers din afifa za su gida a rufe shi.lallashin ta ta cigaba da yi kamar yadda ta iske Zainab na yi suna kuma kara nuna mata ta gode ma Allah da ya takaita mata wahala ya saka baby ba mai rai bane domin da a gaba abinda zai taso na tambayar asalin yaron shi kanshi tashin hankali ne a gareta.Haka sukai ta bata baki har ta hakura ta warware aka cigaba da hira,ita dai bata ci komai ba har sai da Al'ameen ya tashi SBD yadda take jin kunyarsa ,shi ma gida ya koma domin yayi wanka ya huta kafin a sallame su.Haka su kai ta hira har tana dariya sbd yadda balki take ba su labarin bikin.

      Around 12:00pm aka discharge din daga Asibitin ,Al'ameen ne ya maida su gida tare da driver din Zainab da ya zo daukanta dan lokacin dutyn din ta har ya fita ta tsaya ne Sbd su afifa.

   Da taimakon Mima ta fito daga motan tana dukar da kai tana takawa a hankali SBD stiches din da akai mata har falo ya raka su yana mata sannu SBD balki ta shige gida tunda Zainab suka ajiye ta domin ta ce bari ta je gida ta yi wanka ta huta da yamma za su dawo da su ma'u.

  Falo ta zauna shi kuma yai masu sallama ya tafi,matar maigadinsu ce ta shigo domin tai mata wankan jego domin ta riga su baro asibiti ta zo ta saka ruwan wanka a public toilet din su ta kaita ayi wankan SBD zafi da kuma kayan wanka na gargajiya masu hade jikin mace nan da nan da zatai mata amfani da su da kuma potassium (pupple ce a chemist ake saida ta )wadda ake sitbath da ita tana ɓata tiles.Sakawa tayi afifa ta dauko mata sabuwar breezier mai kama jiki ta bata ta saka mai Brown  colour ta ce mata ita ce zata riƙa sakawa duk sadda zatai mata wanka SBD kada breast din ta su zube(bcos abinda ke fara zubda ma mace breast bayan ta haihu rashin saka breezier mai kama jiki lokacin yin wanka SBD first week of delivery mace nononta yana wani mugun tauri na cikar ruwan nono musamman idan ba baby har fever kake sbd nauyin su da cikar su kamar na mai yaye to wannan sakin sun da ake yi shi ke sakawa vein din wurin take ja SBD nauyin su sai kiga idan suka sake wurin ya fita sai kiga nono har saman ciki SBD jijiyan wurin kmr roba ta ke ja ta ke yi,in kikai hakuri kwana 7 kar ki rabu da breezier kuma kar ki matse su  sai ki ga ko sun kwanta to da tuwansu.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now