*Based on true life story*
Story &written by Mmn muhibbat Abdullah
Vote on wattpad @MmnMuhibbatDedicated to taskira members
Page 22
###Gida ya koma hankalinsa tashi domin yana cikin tsananin kololowar sha'awan zainab dakin gaje ya shiga ya isketa zaune tana kallo magana yayi mata ganin yaran duk sun kwanta bacci daya ke da wuri suke bacci ce wa yayi ta zo su je dakinsa.Binsa tayi sai da suka je yake nuna mata abunda yake so tsaye tayi domin kuwa bata sallah dan haka ita bata da wayan yi ma miji dabara ya samu natsuwa shiyasa wani da kin haihu amfaninki ya kare wurinsa sbd daman shi a wurinsa amfaninki kenan kamr yadda ya yadda balki sai ta yi 40days ba su iya wata dabara ba dan haka ta dawowarta daki dan ita yanzu tunda tayi yara biyu sai hankalinta ya koma wurinsu ba sosai take kwana dakin ba duk da tana da yar aiki amma yarinyar dakinta daban tana dakin masu aikin part dinta.Haka ya zauna bala'i na cinai ya kasa zaune ya kasa tsaye ganin 10pm tayi ya yanke hukunci tafiya sabon layi cikin darenan ya rantse bai iya hkri kuma zainab zata gane kurenta tunda tayi mashi wulakanci shi mace har ta isa yayi niyyar lasar zumanta ta hana haba wlh bata isa ba.
Yazo dai dai kofan dakin yar aikin gaje key din motarshi ya fadi tsaywa yayi ya duka dauka yana mikewa ya hango cikin dakin yar aikin tana kwance yar karamar yarinya yar shekara 12 amma dayake shaidan yana doka mashi tamabari ji yayi sabon layi yayi mashi nisa kan diyar amana zai huce haushin zainab dan haka dakin ya tura akai rashin sa'a bude ta barshi ya shiga kuwa ya kulle ya afka ma diyar mutane .
Cikin bacci gaje taji kamar ana ihu ihu dan haka ta Kara kasa kunnenta taji aikuwa kamar ihun sahura take ji mai aikinta dan haka da sauri ta mike dakin yarinyar ta nufa ta kama kacaniyar bude shi amma rufe yake window ta leka abunda ta gani ne ya saka ta suman tsaye bala ne ya keta mutuncin diyar mutane gashi sai marinta yake suna kokowa da shi, munafukin ko tausayinta bai ji, ihu gaje ta saka wanda ya tada duk ilahirin mutanen gidan ciki har da asiya dan tanan bata tafi ba fitowa sukai da balki da asiya da afifa gani yaran mazan ma sun fito ya saka asiya jan su ta maida daki ta saka su komawa baccin dole sbd taga gaje ta fita hayyacinta zuba kawai take tana tonon asirin bala balki sai cewa take ta rage murya kar a jiyo su amma ina hanklinta ya gushe tabarya ta samu ta cigaba da bugun kofar wanda ya dawo da hankalin bala jikinsa tashi yayi jikinsa yana kyarma yana neman hanyar boyewa amma ina gaje tayi nasaran karya kofan daki ta shigo, toilet ya ruga zai rufe kanshi amma sai da ta maka mashi daya saman baya sanna yayi hanzarin saka sakata ya rufe kofar.Gaje ta gigice ta rude ji take zata iya kashe bala.
Bala'i ta rantse da Allah .Balki ma kuka ta kama yi ganin diyar mutane ko motsin kirki bata yi,dakyar asiya ta kamata ita da balki sukayi dakin gaje da ita dan su bata taimakon gaggawa.Da yake yanzu suna driving dan haka gaje key ta dauko ta ce asibiti zata kaita balki zare ido tayi ta ce asibiti kin san baza su amsheta ba sai da police kinsan rape case ba karamin case bane.Gaje ta ce eh zanje in dauko yan sanda daman sbd a taimaka ma diyar mutane da wuri.
Ido baki ta zare, akan yar aiki zaki tona ma mijinki uban yaranki asiri gaje?
Kutumar uban nan !!!inji gaje bala'i shi baki ga tonan asirin da yayi ma baiwar Allah ba sai ni dan na bi mata hakkinta .
Balki tace yar aiki ce fa yana wuce ki maida ta kauyensu a hada ta da kudi da kayan arziki shikenan an rufe maganr.Ta ce eh tabbas dan ba diyarki bace ko !ko dan ba afifa akai ma haka ba kike cewa haka ita yar aiki ba mutum bace ina ce kina zaune ya lalata maki diyar yar uwa amma kika zura mashi ido ke ga jaka wai zaman ya'ya kar a tona mashi asiri ki guji randa Allah zai tashi saka ma yaran mutane ya hada dake da yaranki wlh balki.
Ni ba jaka bace sai dai ki ce jaka waddda zata tona asirin mijinta.
Allah ya tona asirin duk wanda ya tona ma wani asiri inji gaje Allah ya tsine ma asiri indai irin wannan ne na dade ban hankade shege ba banza da ke wadda bata san darajar dan adam ba.
Nan fa fada ya kaure tsakanin gaje da balki .
Asiya ganin abun nasu zai wuce hankali ya saka ta janye balki ta maida gaje dakinta wurin yarinyar da ke neman sumewa sbd azaba nan hankalin gaje fa ya tashi ta saka asiya ta taimaka mata su je asibiti.
Tsalle balki tayi ba inda zata wlh badai yar uwata ba taje raka ki tona asirin mijina.
Asiya ture balki tayi suka kama sahura suka saka a mota jikin gaje sai rawa yake yi haka asiya ta taimaka mata suka shiga mota ta ja suka bar gidan yau asiya ta sure da halin balki wani irin bala'in son miji ne da zai hanaki ganin hakkin yaran wasu yanzu wannan dabbacin da ya aikata ace har yana da sauran kima a idonta lallai ma balki.
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
NonfiksiLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...