👨👩👦👦*ZAMAN Y'AY'A👨👩👦👦
(*Based on true life story*)Story&written by *Mmn muhibbat*
Vote on wattpad _Mmnmuhibbat_
Dedicated to *TASKIRA MEMBERS*
Edited by *Khadija Manga*
* _BAN HAKURI_*Ina Mai bada hakurin rashin jina da kukayi kwana da yawa,insha Allah zaku rika jina akai akai duk da ba kullum ba sbd makaranta nagode da kaunarku gareni.🥰🥰🥰🥰🥰
32
Not editDago fuskanta tayi ta kalleshi a banzace ta ce in kana ma tashi ka bani wuri ka tashi dan aure ne kai da wannan yarinya ban aminta ba!!! haka ya tashi gwiwa sage Dan yasan mama shi ba Wai zata ji maganansa ba tunda har Yar'uwarta ta ki jinin abun to bazata taba saukowa ba. Ta shi yayi ya rufe Mata kofa, dakinsa ya nufa jikinsa duk yayi sanyi Yana jin zuciyansa wani iri Amma zai dage da addu'a har ta yarda ta sauko yasan mamanshi tana da saukin kai sai dai ita mace ce wadda Bata da ra'ayinkanta sai yadda yan'uwata sukai da ita Amma insha Allah zai dage da addu'a har ta aminci domin tabbas Yana kaunar Afifa amma bazai taba aurenta ba idan babu albarka mamanshi ba.
###$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
Ta bangaren hamza yana ta samun sauki cikin yardar Allah sbd alluran da akai masa masu saka bacci sun taimaka masa wurin fara mantawa da shaye shaye duk da ba duka ba sbd abun daman farat daya ake fara shi barinsa sai a hankali.Ma'u Kuma kasuwanci yana ta cigaba domin dai sana'a goma maganin mai gasa ta fara ba abunda Bata saidawa tun daga kayan provision na awo a cikin gida har yar tireda gareta a kofar gida sannan tana saida su atamfofi da yan kunne da kayan lalle a cikin gida sannan tana dorawa a waya ana saye.Wani lokacin har Kano take zuwa sari sbd yadda Allah ya saka Mata albarka cikin kasuwancinta bata raina riba ko mai kankantarta indai zata maida kudin Bata da matsala fa riba Shiyasa nan da nan mutane suka san ana sana'a gidanta sbd saukin kayanta.A wannan karon bata manta da neman albarkan iyayenta ba ko yaya ne domin taga illar rashin neman albarkan su a wancan lokacin sosai iyayenta ke mata addu'a musamman mamanta Kuma tana ganin haske a cikin sana'arta tuni suka shirya da babanta tunda bata daura mashi nauyinta ba, Ashe daman shi zawarci in kana da sana'aka na biyan bukatun yau da gobe ba a cika tsangwamarka ba sosai .Sai ga babanta ya bude baki yana ta bama innarta labarin ai daman yasan mijin ma'u bai ji bai son aurenta ya mutu ne Shiyasa ya ja bakinsa yayi shiru sbd yana tunanin kada dawainiya ta kara haye masa(Da yawa wasu iyayen sun San ana cuta ma yaransu a gdn aure amma sbd tsoron responsibilities na yaran in sun dawo gida kada ya haye masu sai kaji sun yi tsit,shi Kuma wani namijin da ya lura da hakan sai yayi ta shuka wulakancinsa son ransa Allah ya kyau ta).Masu son ma'u da aure suna ta fitowa Amma dai taki Maida hankali kansu sbd tana son ta aurar da haneefa tukun sannan hamza ya samu lpia zata Fi samun kwanciyar hankali tunda wasu maxan ba danka su ke so ba kai su ke so.Takan ziyarci yaranta ta duba su dan taga wani hali suke ciki ta ji dadin ganin canzawarsu ta Kara yarda cewa ilimin addinin da aiki da shi ,Yana kawo rabauta duniya da kiyama.Ita kanta tai ma kanta sha'awan shiga islamiya domin ta yarda shi ilimi ba'a girma da nemansa islamiyan matan aure ta shiga a kusa da su sosai taga matan aure da ya'yansu da komai suna kawo haddan sumuni har 3 a cikin sati guda sai taga ita duk aikin me ta tsaya yi gashi nan an barta baya.Sosai take samun nutsuwar zuciya Wanda har Hakan ya Nuna a jikinta wani lokacin in ta tuna baya yadda ta naace auren mudi sai ta yi ta ganin wautarta ga kudi a lokacin Amma ba kwanciyar hankali Ina amfanin auren fasiqi wani auren nacee masa ba alheri ba ne ba gashi da ta cigaba da zama da duk wannan hasken musulunci da dandanon kwanciyar hankalin bata same su ba Ashe da can baya a banza Zainab take kallonsu ta fi su kwanciyar hankali.
Haneefa ta samu mijin aure Ma'u ce wa tayi ayi gaggawar aurar da ita in har ya yarda zai aureta a haka Allah bar shi tayi karatun a dakinta tunda mace nawa take karatun da aure,mijin ya yarda zai aure ta a haka domin soyayayya yake Mata ta tsakani da Allah shi abun farin cikinsa ma da tayi kuskure ta tuba kuma Bata munafuncesa ba ai ko Allah Yana son bayinsa Wanda idan suka yi zunubi sai su tuba Kuma su yi alqawarin ba su komawa zuwa ga aikata zunubin.
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
No FicciónLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...