👨👩👧👦👨👩👧👦ZAMAN YA'YA👨👩👧👦
*Based on true life story*
Story &written by Mmn Muhibbat Abdullah
Vote me in Whattpadd@Mmnmuhibbat
Dedicated to taskira members
This page is for again Maman madina🥰🥰🥰Page 9
####Talle ne yayi saurin ankara da faduwar Zainab jikinsa na kyarma ya sauko daga bisa gadon ya baro Attine da hankalinta ya tashi matuka domin kuwa zainab ta santa ita matar aure ce da ke aure unguwarsu zainab yaranta biyar amma tsananin rayuwa na rashin kulawa daga mijinta da yake tafiya kudu kasuwanci ne ya janyota halin da take ciki yau rabonta da mijinta wata 9 kenan tunda ya zo wancan zuwan yayi sati 2 bai kara zuwa ba gashi daman ba wani abun arziki ya bar mata ba na kula da yaranta abincin sati biyu ya bar mata ba ruwanshi da lpiar yaran shi da ilimin yaranshi da suturansu da sauran bukatun su na yau da kullum yayi tafiyarsa da sunan neman kudi.Attine ta kasance marainiya shiyasa bata da wani gata sai na Allah sbd gidan kawunta ta tashi da shima gayyar ya'ya sun mashi yawa saboda daman ba wani karfi ne da shi na rike mace daya ma bare mata har 3 kowace ita ke kula da yaranta ta ina zata je zawarci ga ya'ya kuma daman mijin ba wani tsananin bincikar danginsa akai ba kawai daman kawun yana Allah Allah ya rabu da yan matan ko ya ji da kananun yaran shiyasa ba wani binciken kirki yayi ba.( *Daman wasu iyayen musamman masu tara iyali ba kulawar kirki basu cika maida hankaki wurin binciken irin mazajen da yaransu zasu aura ba sai gaggawar a rabu d yarinya kawai*).Haka kullum idan taje kai mashi karan mijinta tun kafin yaranta suyi yawa haka tun tana da yaro daya ya fara kaiwa irin wannan watanin a baya bai wuce wata 2 amma yanzu sai yakai wata 9 sai kawun yace mata tayi hkr ta zauna zaman yaronta yanzu in ta fita tana da tabbacin wazata aura haka dai yai ta mata huduban tsiya da saka ta fidda rai da tsammanin cewa Allah shi ke bada miji nagari ga macen da ta roki Allah wadda bata cuta ma mijinta na baya ba.Al'amarin zuciya yau da gobe ga wahalar rayuwa ga bukatan mijinta wanda daman duk mace mai aure dole tana da wannan bukatan daman shi ne abunda gidan iyayenta bazata samu ba amma al'ummarmu wasu basu dauki bukatan diya mace abun muhimmantawa ba sai ta da namiji shiyasa matan da imani bai wadace su ba sai su fada halaka in sunga basu da yadda zasuyi daman Abun biyu saurin halakr da mutum yake yunwa da sha'awa.Ruwa ya debo ya shafa mata duk ya rikice ya rasa yadda zai da ita bude ido tayi ta kallesa sannan ta kara maida idon ta rufe sbd tsananin takaici talle ya fice mata daga rai sosai da sosai.
Attine ce ta zo zata fita tana rufe fuska da hijabi zainab ta riko hannunta ji take kmr ta shaketa kallonta tayi ta ce "Attine ki ji tsoron Allah da auranki wace lalacewa ce ta same ki haka.kuka Attine ta fashe da shu sbd kunya da nadama.Shi kuwa talle tsuru tsuru yayi ya rasa bakin mgna yo ai abun da kunya surukinsa ya mutu yau amma shi yana nan yN cin amanar yar sa kai yau yaji kunya bai ji dadin halinsa ba yau.
Da gudu Attine ta tashi ta fita waje kannen zainab da ke jiranta maamki ya kashe sa da yaga attine ta fito daga gidan gaidata ya tsaya yi amma bata kulasa ba tana ta sauri tana tunanin makomar auranta da kuma image din ta da zai baci kuma ya yaranta zasu ji idan suka girma kai tana cikin tsaka mai wuya ta jefa rayuwarta a bala'i sbd zaman ya'ya ita dai in haka ne zaman ya'ya bai mata rana ba.Haka ta isa gidanta tana tunani ta iske yaranta sunyi bacci sbd daman kanwar ta ce ke tayata kwana sbd daman can gidansu a matse suke yan matan sbd kuncin muhalli.Zainab kuwa dakyar ta tashi ta shiga dakinta har wata juyawa kanta yake yi sbd tashin hankali me yakai bakin ciki ace ka kama mijin auranka a bisa gadon sunnar su kuma ranar da mahaifinka ya rasu innalillahi wa'inna ilahil raji'una take maimaitawa sbd tsanannin tashin hankali kayan ta dana yaranta take hadawa sbd wlh wlh duk duniya in zasu taru su bata hkr ta gaama auran Talle mutumin da yaje makabarta yau ya tona kasa ya rufe surikinai amma ace ya dawo gida yana aikata fasikanci sbd rashin tsoron Allah shi ta sabon Allah yake lkcn da wani yabar duniya shima zai iya binta ko a yaushe amma ya zabi sabon Allah subhannallah.Kwashe kayanta tayi baki daya dana yaranta zata fita sukai karo da talle a bakin kofa hkr ya shiga bata yana mata rantsuwa shi wlh bai sake neman mata.
Shiru tayi ta kallesa ta ce "Wlh yau ba gobe ba sai ka rubuta mani sakina talle ban kasance mazinaciya ba ban kasance fasika ba balle ace zaman mu da kai yayi dai Allah s.w.a yace a ckn suratul nur aya ta 3" lah yace mazinaci bai aure sai ga mazinaciya yar uwaesa ko mushrika Allah ya haramta haka ga muminai" wucewa tayi zai riko hannuta ta dago idanun ta da suka koma ja sbd tsabar kuka yau taga jarabawan rayuwa ta kallesa ta ce "Wlh talle da ace mu hudu muka kama ka da babu abunda zai saka in kai ka court ayi maka haddi tou shaidan mutum daya bata isa dan haka ka bani hanya in wuce.
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
NonfiksiLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...