👨👩👧👦 *ZAMAN Y'AY'A*👨👩👧👦
*(Based on true life story)*Story&written by *Mmn muhibbat*
Vote on wattpad_Mmnmuhibbat
Dedicated to _*TASKIRA MEMBERS*_ Gdan dadi 💃🏼
Edited by _*Khadija Manga*_ _(Allah ya kara jaddada rahama yakai haske kabarin iyayenki Ameen)_
_Mmn madina ina kara miko gaisuwa qawar arxiki_
Wannan page din naki ne Husna AKA Hussy taskira(Mmn eman) ina miko gaisuwa🥰🥰
_Aunty hadiza taskira ina godia da vote da comments a wattpad Son so fissabilillah_
*Page 26*
Zaman zainab a london zama ne na kwanciyar hankali da amana, bata ce ba su samun matsala da mijinta ba amma abunda ta yarda da shi shine tsakanin harshe da hakori ma ana samun sabanin bare tsakanin miji da mata amma tana kokari taga idan sun samu sabanin to su yi sulhu sbd shi daman sulhu alheri ne ga ma'aurata. Babu wata rayuwa ta ibada da za'a ce za 'a sameta da sauki dan shiga aljanna ba wasa ba amma ibadar aure tana zama mai sauki ga ma'aurata idan dukkansu suka dauketa ibada.
Lokacin da ta samu cikin twins dinta ta so ta daga hankalinta sbd karatunta sbd tana gani kamar bazata iya ba amma da ya nuna mata karatu bai hana haihua sai dai in mace batai niyyar yi ba.
Tsarin karatunta ta canza ya zamana cewa kullum take duba abunda aka koya mata sbd ta samu sauki idan exams yazo.
Ta haifi yaranta twins yan mata duka an saka masu Safna d safina sunan mamanta da maman dr aka saka sbd ta rasu bada dadewa ba bayan sun tafi karatu, dr ne kadai yazo sbd ita tanada ciki a lokacin.
Yaransu ma an saka su a makaranta dan haka zainab yanzu bata da wata matsala babba ta gidan aure a kullum idan ta kalli dr takan gode ma Allah da ya bata mijin da ya nisanta da aikata manyan zunubai sannan mai kokari bakin gwargwadonsa kan hidima da iyalinsa sai abunda ba'a rasa ba wanda daman dan adam tara yake bai cika goma ba.
Tun bayan tafiyar zainab wata rana safwan ya kirata yana kuka ya ce babansu ya kore su daga gidanshi sbd an yi masa satan kudi talatu ta ce su ne dan haka ya rufe idonsa ya ci musu mutunci tunda daman kule yake da uwarsu wai ta yi aure ta bar shi ta bi wani gardi kasar waje,kasar wajen ce bazai iya kaita ba ne ko me take nufi.
Ce ma su tayi su yi hkri su dawo gidan iyayenta wurin inna iya su zauna. Da dr ya ji fada ya kamayi dan me ya saka ba za su dawo gidansa da zama ba ai gidan su ne su ma.
Murmushi ta yi ta ce ba wai na ki ta naka bane amma kasan su yara ne samari da suke tashen balaga bai kamata a basu ragamar rayuwansu ba a halin da su ke ciki ba babu wani babba da zai tsawata masu su zauna gaban inna iya tana gani shige su da ficen su.
Sun gama karatun su cikin nasara sun dawo kasar su tare da yaransu baki daya dan haka yanzu gidan ya zama cike yake da albarkan ya'ya.
Sun koma bakin aikinsu duka zainab tana kokarin nuna ma dr zuwa aiki akan lokaci ta ce Amana ne su ka amso daga lokacin da aka dauke su aiki sannan Allah yana gani su sunyi rantsuwa ce wa za su xo akan lokacin da aka saka masu idan suka saba alqawari Allah yana kallonsu.
A kullum tana tsoron mijinta ya kawo mata haram komai yawanta ta fi son halal komai kadan dinta shiyasa rayuwa su ke cikin godiyar Allah da wadatar zuciya.
Duk inda aka san mace mai aiki ko yaya ne ba'a rasa inda take taimakon mijinta a cikin gida haka ta kasance ga zainab takan yi kokarin yi masa wani karamin abu na gida amma bata zabi abu guda ba tace wannan hidimanta ne sbd kar ta gaza wata rana idan wannan watan ta sai masa maggi wani watan ruwa zata saya wani watan ma bata sayen komai dan kuwa ya sayi abunsa.

YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
NonfiksiLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...