RABA ZUMUNCI

260 29 0
                                    

👨‍👩‍👧‍👦ZAMAN YA'YA👨‍👩‍👧‍👦
*BASED ON TRUE LIFE STORY*
Story&written by Mmn Muhibbat Abdullah
Vote on wattpad@Mmnmuhibbat.

Dedicated to taskira members

*DAN ALLAH KUYI HKR KUN JINI SHIRU KWANA 2 BAN LPIA CIWON KUNNE YA MATSA MANI*

PAAGE 20

Zainab zaman ta da jidda sai hakuri domin tunda ta gano take taken jidda sai ta ci maganin zama da ita a farkon zuwan su gidan idan yaranta sun shiga dakin jidda kallo ko gaisheta sai ta tsiri cewa ai suna bata mata falo ko kuma ta ce an fasa mata cups ko filaet ko Cristal din ta na jere kullum da kalar abunda zata ce ya faru idan jameel ya dawo ta gaya masa sai yace tayi hkr yara ne zai masu fada ita kuma zainab in taji sai ta kama yaran ta zane sbd tana gani ai ba su kyauta ba alhali ba su suka fasa mata kaya ba ita ke fasawa da kanta idan sun shiga dan kawai ta jama masu sharri daga baya zainab ta ce su daina zama dakinta da sun shiga sun gaida ta su fito.

Sai ta cire cewa ai yanzu suna mata wani gani gani sun zo gidan uban da ba nasu ba suna mata iskanci zainab dai bata cewa komai haka zata kama su ta buga ga zagi ga hantara ga bakin goru da rowa ita daman rukayya tana da wayanta shiyasa ko abu ta gani hannun jidda take kauda kai mama ce ke bata da wayau sosai amma ita ma daga baya sai ta yi wayau  ta daina kallon jidda amma haka nan sai ta hau bugunsu wai suyi zuciya su koma gidan uban su shegu.Wata rana tana bugunsu jameel ya shigo yakw tmbyrta dalili sai ta ce zaginta sukai yasan karyat take sbd yaran zainab ba su zagi tun suna yara dan haka ya rufe ta da fada anan fada ya kaure tsakanin jameel da jidda.Zainab ta fito ba su hkr sbd ranar week end ne tana gida aikuwa jidda ta ce mata munafuka shegiya dangin mayu bazawarar banza ta kashe auranta ta zo zata kashe na kanenta aikuwa jameel ya dauke t da mari zai cigaba da bugunta zainab ta rike shi ta ce ya daina ba kyau haka yana namiji zai bugi mace hakan kuskure ne jidda cigaba da zagin zainab tayi ta ce ta kyale shi ya bugeta din ai ba sbd ita ya saka ya ke bugunta ba ce wa yayi ta tafi gidan su sai ya neme ta tunda har ta kira su dangin mayu ai shima mayen ne kenan.

Zainab ce wa tayi a'a Jidda baza ta tafi gd ba wlh yo sbd me ai zafin zuciya ne ya saka ta ce haka kuma in ban da abunsa ai dan ta bugi yaranta sai ya saka mata baki ai itama uwarsu ce ko.

Jidda ce wa tayi wlh bata zama dan haka sai ta tafi sai ya zaba ko ita ko zainab,idan ita ya zaba tou fa dole yau zainab ta bar gidan idan kuma zainab ya zaba dole yau tabar gidan ce mata yay ya zabi yar uwansa dan haka ta kara gaba.

Daki ta shiga ta dauko mayafi zata fita zainab ta riketa ta ce bata fita amma jidda ta ture zainab ta yi gaba abunta.

Jameel cewa yayi sai ya saketa amma xainab tayi rantsuwa duk randa ya saketa tou fa ba ita ba shi dan haka dole ma ne yayi hkr da matarsa ai suna zaman lpia damuwarta kawai ita ce da yaranta tou dan me yasa zai rabu da matarsho sbd ita kuskure ne babba haka ai daman shi dan adam tara yake bai cika goma ba.Ba yadda za'ayi a tursasa jidda ta so abunda zuciyarta ke ki sai dai da lallabwa da kai zuciya nesa sannan har Alllah ya saka wata rana ta so zainab din amma idan vata so ta ba ,ba laifi bane ai daman ita duniya ba dole ba ne kowa ya so ka dole wani bakai mashi laifin komai ba ya ki ka.

Shiru jameel yayi yana mamakin zainab yadda yarinya ta gama zuba mata rashin kunya amma tana kareta in wata yar uwan miji ce va tuni zata saka a kore jiddda ba ya ce "yanzu duk abunda tayi maki baza ki ji haushin ta ba sai kare ta ?
Ta ce" dole in mata uzuri ai idan rukayya ce ko mama suka je suna abunda jidda take yi ai baza ka so a saka maka so ba ko?

Kai haba Allah ya sauwaka ai mun va su tarbiya baza su yi haka ba

Hmm jameel kana mamakin rayuwa da duniya da mutanen cikinta ko kana raina sha'anin zuciya ita zuciya al'amarinta mai girma ne sbd sai dan adam yayi kokari ya danne abarsa sannan zata danno babu wanda zai maka wannan aikin sai kai yanzu kai kana tunanin iyayen jidda laifinsu ne ba su bata tarbiya ba kake gani wlh ko kusa so da dama mukan aurar da yaran mu su tafi su bar mana yarbiyan da muka ba su ko kuma su manta da tarbiyanmu musamman idan suka hadu da abunda zuciyan su bata so mafi yawancin lokutta ana gani idan mace ta burkice ko ta canza sai ace wai ai laifin iyayenta ne ko a dora ma kawayenta laifi ace su ke zugata ko wani makusancinta ko makwabtan ta ace su ne ai wance ba halinta bane sun manta al'amarij zuciya musamman idan ta hadu da abunda bata so tofa zata yi ta zuga ka ne kayi kaza ka bar kaza in ba kayi kokarin danneta ba da azkar da ta'awizi sai ta kai bawa ka aikata dana sani.

ZAMAN YA'YAWhere stories live. Discover now