WASIYAR AURE😭❤️❤️
By: Najaatu Shehu Naira
Wattpad: Najaatu_NairaFKD PRODUCTION FANS WRITERS ((((42))))
Sometimes the dry tears are still wet, only because they are falling inside our HEARTS.
Tana tsaka da kuka taji andafata akafada, tajuyo dasauri danganin waye, Yusuf tagani tsaye yace "Ushna lafiya?" tana shashsheka tace "Yaya yasakeni" jiyayi kamar ta saukemai guduma saman kai, yakauda kai cike da takaici yace "toh burinki yaciki" Shiru tayi takasa furta ko kalma sai shashshekan kuka ita kanta tarasa dalilin zuban hawayen ba 'ka'k'kautawa, ganin batada matausayi tatashi da gudu tayi 'dakinta tabar Yusuf da 'ya'yan a parlour,
Kuka taci ma'ishi
tun tana iwu har sautin muryarta yadaina fita makogoronta yabushe idonunta suka 'kafe jijiyoyin kanta suka tashi ra'do-ra'do harshenta 'daci,
Tana zaune abun duniya yadameta takifa kai jin'karar bude 'daki yasa ta'dago kai ahankali da mamaki taga bata gani sai dushi-dushi, muryan Mama taji tace "Mahaifinki yace nagaya maki kina fita idda kifito da wanda kikeso a'aura maki batare da 'bata lokaciba",
Jitayi maganar nadukan zuciyarta, wani 'bangaran farinciki wani bangaran kuma tarasa dalilin 'bacin ranta, sam zuciyarta ta'ki bata ha'din kai, shiru kawai tayi har Mama tagama fadace fadacenta tafita bazace ga kalma daya data tsinta ba,
Hoton Hamza kawai take gani yanayin dayashiga sanda yafurta mata kalmar saki..
Nashiga uku tafurta azahiri tace "nadauka zanyi farinciki amma why, why Hamza you're always my problem, duk kaikaja wannan", nan tahau wurgi da kayayyakin 'daki ta cillah wannan can ta harba wancan can,
Jin'kara tartsatsi agida Alhj Shehu yafito yanufi dakinta daidai fitowar Mama daga nata 'dakin sukayi kicibus da Yusuf akofar dakin,
Cikin 'bacin rai yakallah Mama yace "Ushna ko?" Bata bashi amsaba tashige,
Ido tazaro atsorace ta'karasa da gudu ganin tafasa madubi hannunta nazuban jini daidai shigowar Yusuf yace "maizangani haka?" Tsaki Alhj Usman yayi yakallah yusuf yace "Yusuf koyamata hankali inaso Ushna tasan tanada nagaba da'ita"
Mama na 'ko'karin riketa tana fincikewa Yusuf ya tsinketa da mari yace "wani irin shashancine haka, baki da hankaline" "eh banida hankali" tafada cikin tsawa tace "kasan mai akaimin ne, gaba daya ni aka cuta"
"Ushna waya cuceki" Mama tafada cikin kuka,.
Tana kallon Mahaifiyar tata dake zubda hawayen takaici, azuciya tace "kaina" azahirikuma tace "Hamza" tana kallon fuskan iyayenta dake dauke da tambarin bakin ciki tace "shiya tarwatsamin duk wani farincikina",
Tsaki Alhj shehu yayi ya'daga mata gira yace "tunkan aje ko'ina harkin fara nadama? Aini nadauka zakizuba ruwa a'kasa kisha dan murna",
Dasauri takallah Mama tagirgiza kai tana kuka mai radadi tace "Mama ba nadama nakeba", kai kawai Mama tagyada tace "naji nasani muje nawanke maki hannu jini kike zubarwa", tajata jiki asanyaye suka fice,.***********
Babu yadda Daddy baiyiba Hamza yayarda yabishi gida ya'ki fafur hakanan babu yadda ya'iya yamaidasa gida adaddafe yakaishi har dakinsa yakwanta da taimakosan, saida yaimai nasiha mairatsa jiki kan yatafi,.
Gaba daya satin Hamza adaki yayishi baya fita, so tari inyaji damuwar Ushna yamai yawa saiya dauko qur'ani yafara karatu ko yakira Mama yaji muryar 'Ya'yanshi, lokaci daya komai yai dib arayuwarsa, tunani yake wani lokaci saiyaga abun kamar mafarki, lalle wannan shi ake kira tafaru takare, karo nafarko dayasan zafi da 'kunan so, lalle so kaddarace mara tabbas kuma yazun yayi imani dakaso gwanma asoka....**********
Hakan take awajan Ushna saida tai Sati biyu bata fita kobakin daki saidai akawomata abinci ko 'ya'yanta Mama kerainansu intaga suna bukatar Mahaifiyarsu ta aika yan aiki sukaimata, wani lokaci kuma takan shiga tadubata su Madina ma sai jefi jefi take shiga dubata danmakaranta.
Ahaka kwanci tashi lokaci yaja tana gabda fita idda takunna wayarta dake kashe natsawan lokaci,
Minti daya batai ba kiran wayar Fidyan yashigo tadauka dasauri cikin tausassar murya tana murmushi tace "Fid",
Jiki narawa kamar tana gabanshi yace "Mine kinanan dai lafiya ko?" Gyada kai kawai tayi tace "um", nandanan kwallah yacika idonta tace "Hamza yasakeni",
Yanda yaji muryarta yasan badaidaiba, ya'dau 'dan lokaci yana tunanin abun gayamata can yace "Ushna ya'bata rayuwarki, a'dan 'kan'kantan shekarunki yasa kinshiga tashin hankali kala-kala, yamaidaki karamar bazawara Mine kiyi hakuri kijirani dazaran kingama idda zandaukeki kizama mallakina",
Hawaye tashare tayi danmurmushi azahiri tafurta "nadauka zanji dadi inya sakeni, amma kuma banajin dadi Fid inatsoro kar,,,,,," dasauri ya katseta yace "dole kiji tsoro mana sabida iyayenki, kwata-kwata basu maida damuwarki tasuba, Ushna namaki alkawari zanmaidake sarauniyar mata, zansaki alfahari, kituna rayuwarmu ada, zanrabaki da bakinciki Ushna kituna irin kaunar danake maki Mine kitunamu kituna rayuwarki Ushna u're not meant for him, yakikeyi kamar,,,," jin murmushinta yasa ya tsagaita yace "are u ok?" Dasauri ta gyada kai tace "i want me back, gaskiya dole innemo Ushnata nagode yau daya katunamin da rayuwar farincikina," dariya yai sosai yace "that's Mine da saboda wancan old fashion dinkike 'bata ranki? Kinmanta yadda ya azaftar dake yaraba tsakaninmu kobakya tausayi nane", murmushi kawai tayi tace "ni, ni?" Dariya suka kwashe yace "dazaran kingama idda kisanar dani, i'll come for u and make u mine" yakashe wayar tare da ajiyar numfashi azahiri yace "da maitake tunani, kai mata toh bata sonane?" Ji yayi gabansa yafadi rasss dasauri yagirgiza kai yace "bazai yuhba Ushna tawace,....*************
Washe garin ranar da Ushna tafita idda Hamza yaje da sassafe kwaso 'ya'yanshi, duk hanyar dayasan zaiganta ya'kaurace, zama yayi adakin Mama saida suka tattauna tsab ta tattaromai kayayyakin Madina da Fahad ta dan'kasu jiki asanyaye tace "toh su 'Yanbiyu amma zaka lamince sai anyayesu ko?" Saida yadau lokaci kan ya lumshe ido yace "Mama inaso nahada kan yaranne waje daya ayanzun sukadai nakeso narayu dasu, idan Ushna nagida zan'iya barmata amma banyarda suje agolanci ba, kiyi hakuri", dasauri ta girgiza kai tace "anya kuwa, gaskiya Mahaifinta yatasota gaba banjin zata wuce sati guda agidannan bai aurar da'itaba, saidai koni narainesu yaso insunkai shekara biyu ka karbesu kaji?", dakyar yagyada kai badan zuciyarsa tasoba, ya debi yaran yatafi suna murmushi banda Fahad dabai wani saki jikinsaba dan sabon dayayi da Mama,.*********
Duk yadda Ushna taso tazalle maganar aure tahuta na wani lokaci Mahaifinta ya'ki, babu yadda ta'iya sanin hanyace yadauka dan hukuntata agidan badan tasoba tabama Fidyan dama yafito aure, bada jimawaba yasauka Kano gurin danginsa tare da yimasu kyauta mai yawa suka amince suka shigemai gaba wajan neman aurenta,.
Daniyan gaisuwan surukai sukazo da kudin gaisuwa Alhaji Usman yakarba batare da 'bata lokaciba ya'daura aure nan take,...Ushna nazaune kiran wayar Fidyan yafado wayarta, tadauka da sauri tace "Fid" cike da murna yace "kinji yadda sukayi?", kamar tana gabansa tace "ah maiya faru?"
Yana zumudi yace "gaskiya Baba mutumin kirkine Mine, kawai daga zuwa neman aure yadaura mana aure",
Dasauri tazaro ido waje ta dafe kirji tace "aure fa?"
Wani irin farinciki mara musultuwa ya baibayeshi yace "kwarai kuwa Mine, yanzun sai maganar tarewa inajin kamar nazo nadaukeki mutafi yanzun",
Wuff tamike wayar dake hannunta ya sulbe asukwane tace "nashiga uku" tafito da gudu tashiga dakin Mama bata tadawo parlour dagudu taganta tana kwance takishingida babban kushin tace "Mama dagaske wai andauramin aure?"
Gira Mama ta'daga batare da ta'dago takalletaba tace "yawuce wai"
Batasan sanda siririn hawaye ya ziraro kan kuncinta, zuciyarta na bugawa dib-dib cikin kausarsar murya tace "toh Yaya Hamza fa?"
"Ya'yanshi zaki bashi",
Alhj Shehu yabata amsa yana shiga yana kakkabe babbar riga yace "nabaki nanda kwana uku kitare dan bazan saida akuya tadawo tana cimin dinga ba" yafada aharsale yazauna gefen Mama,
Bata iya juyawa takalleshiba cikin kuka tace "amma nidai gaskiya ba'aimin adalciba wlh aiko,,,,", jinsaukar mari kan fuskarta yasata tsit tarike fuskarta hannu bibbiyu,
Ganin yadda ran Alhj Shehu ya'baci Mama tatashi cikin rarrashi tace "ya'isa karka 'daga hankalinka rabu da ita"....
Tsaki yaja yanunata da yatsa yace "gatan da muka nuna maki yasa kikeso kimaidani 'karamin mutun? toh bazai yuhba, kuma shima wannan auren wlh inkika kasheshi toh kinemi wani uban bagidana ba," yakakkabe babbar rigarsa yahaye sama Mama nabiye dashi Ushna tazauna da'bas kan gwuiwarta tana zubda hawaye
Votes
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...