WASIYAR AURE 34

603 113 8
                                    

WASIYAR AURE😭❤️❤️

By: Najaatu Shehu Naira
Wattpad: Najaatu_Naira

FKD FANS PRODUCTION WRITERS
(((34)))

Hamza nazaune a parlour tare da Maryam tanamai bayani kanyadda taron bikinsu zaikasance, dukda hankalinsa baikanta amma hakan baisa tabar rawan kai da kara'di danganin taja hankalinsa gareta ba,
Suna tsaka da magana kiran wayar Dr Aliyu yashigo,
Dasauri Hamza yadauka cikin zumudi batare dayagaisheshi ba yace "Dr nagaya mata amma kamar Ushna bata kaunata, kana ganin hakan danayi daidaine?"
Dasauri Dr Aliyu yagyada kai kamar Hamza nagabanshi yace "Daidaine mana domin yakamata tasan tarin irin kaunar da kake mata kafin tabama soyayyarka dama, kuma karka gaza harsaikaga kayi nasara",
Shiru Hamza yayi cikin 'dar kan yace "likita tunda nagaya matafa haryau bansata a idoba kullun naje dakinta saina tarar arufe, ina tsoro gata da juna biyu",
Murmushi Dr Aliyu yayi kan yace "amma wannan karon kafara fa'dawa soyayya ko?"
Gawurtaccen ajiyar numfashi Hamza yasaki kanyace "toh dukda naso Matana amma wannan karonne naga 'Yamace na guduna, ban'ankaraba Allah ya jarabceni da tsananin kaunarta, inafatan komai yayi daidai tsakanina da'ita domin inaso nariketa amana"
"kabata lokaci insha Allah everything will b fine, duk wannan mai wucewane, nahadu da case din dayafi naku kuma yanzun suna rayuwa cikin aminci kaima karka cire rai",
"Toh nagode Dr sai anjima" Hamza yace yakashe wayar,

Ahankali yasauke ajiyar zuciya, cikin da'ki'ka yadawo haiyacinsa, sai alokacin ya yatuna gaban wacce yake, akunyace ya'dago kai dasauri zaimata magana karab idonsa yasauka kan idonta dake zaryan hawaye,
"Subhanallah maikike haka" yafada yana kallon kwayar idonta dayai ja jajir,
Cikin muryar da bata fita tace "dagaske kanason Ushna?"
Dasauri yakauda kai yace "bahuruminki bane wannan",
"Kafadamin gaskiya dagaske kana son Ushna kuma agabana kake cimin fuska"
Cikin sanyin rai yace
"Kiyi hakuri"
Cikin tsawa tace "ammadai Ushna ba 'irin matan da kakeso bane",
Nandanan ya hassala yajuyo dasauri yakalleta yace "ke harkinsan kalan matan da nakeso? Dan Allah karki 'batamin rai kibarni naji da abudaya, zantura maki kudin dakike bukata, maqarasa magana ta watsapp bazansami daman zuwaba kwana biyu duk abinda akeciki mayi waya",
Yatashi yabarta zaune tana cizan yatsa,

Koda yakoma gida yaja kofarta ya'kara taddashi akulle, jiki a sanyaye yakoma 'dakinshi,.
Washe gari da safe yaji hayaniya a Parlour, dasauri yafito sanin inba Ushnaba saidai ba'kinta dan tunbayan komawar Madina da Fahad wajan Mama babu yawan zirga-zirga agidan,
Dan likita yagani da brief case tare da Yusuf azaune suna tattaunawa da Ushna,
Ganinsa Ushna tataso da sauri tace "yauwa likita gashinan kadubashi, tunbayar rasuwar Auntymu wallahi haryau baidawo haiyacinsa ba",.

Jiki asanyaye Hamza yagaisa da Yusuf tare da likitan yakallesu yace "Yayanmu ya akayi naganka da sanyin safiya haka?"
Nan Yusuf ya'kara gasganta tabbas Hamza ya ta'bu, inba hakaba yazai kalleshi yakirasa da Yayanmu,
Atsorace yakallah Likita yace "gaskiya akwai matsala babba Likita kadubashi,"
Nan likita yadada matsowa gabda Hamza yace "Malam Hamza zaka iya tuna yau yaushe?"
"Yau monday" yafada yana kallon Ushna data 'kuramai ido,
Likita yanuna Ushna dayatsa yace "Wancan wacece?"
"Matata abar kaunata" Hamza yafada ba shama'ki,
Adaburce Ushna tataso tace "Yaya kaganiba wlh nagayama Yaya Hamza yahaukace baicikin hayyacinsa"
Dasauri Hamza yakallah Likitan yace "wa? Hauka! Ni 'din?"
Kanya bashi amsa Ushna tamatso jikin Yusuf cikin ra'da tace "Yaya hargidannan akazo akaimin fyade, da wani maihankaline kozaizauna dani aisaiya zubda cikin amma kaganshi saima kyautatamin dayake",
Cikin 'bacinrai Hamza yakallah Yusuf yace "in ita batada tunani Yusuf saikai ka biyemata, satin dayawuce nakallah Ushna nagayamata inasonta daganan ta 'kauracemin saiyau nasanyata a idona, laifine danna gayamata inasonta dahar zaka daukomin 'kato hargida dasunan ina hauka?"
Lokaci daya jikin Yusuf yamutu, ganin ta'inda Hamza keshiga batanan yake fitaba yadauko laifin gaba 'daya ya tattarashi kansa,
Ganin bala'in Hamzar ya'ki 'karewa kamar wanda yake jiranshi yagaji yami'ke yakallah Ushna yace "ke dan Mijinki yace maki yana sonki shine kike kira hauka?"
Dasauri ta gyada kai tace "come to think of it Yaya yazaicemin yana sona, kaima kaduba fa",
Tsaki Yusuf yaja yakallah Likitan yace "zomuje, dan Allah Yaya Hamza kayi hakuri",
Yajashi suka fice,

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now