WASIYAR AURE 45

500 131 3
                                    

WASIYAR AURE😭❤️❤️

By: Najaatu shehu naira
Wattpad: Najaatu_naira

FKD PRODUCTIONS FANS WRITERS (((45)))

Kuimin vote
Hamza baitashi tsintar kansaba sai afa'da'dan filin da bazaice ga iyakacinsa ba dan fa'di, bude idon dazai idonshi yasauka kan Hajiya Hafsah dake tsaye tana jiran farfadowarshi,
Dasauri ya fincike zaimike yaji hannunsa katakam sun dauri, cikin zafin rai yace "mainaima ku? kurabu dani"
Murmushi Hajiya Hafsa tayi tace "toh ni maizakaimin ai babu abunda kaimin kajira dai wacce takamaka tazo tai magana"
Baibi takantaba ya'daga kai yakalla gardawan dake kansa masu kirar Allah ya'isa yace "zanbaku duk abunda kukeso dan Allah kurabu dani kukwance ni inada marayu",
"Hamza agaskiya mutuwa zakayi" Hajiya Sadiya tafada tare da tunku'do Maryam tafa'di kan jikinshi tana kuka,
Mamaki yahanashi magana sai kyarma da jikinshi keyi yana fatan Allahsa wannan mafarkine,
Ya rintse ido dakarfi ya jujjuya kai da fatan yafarka yaganshi saman gadoshin, take suka fashe da dariya,
Hajiya Sadiya tajanyo kujera tazauna gab dashi tace "Hamza kaban wahala" jinkukan Maryam yacika wajan ta falleta da mari tace "yimin shiru nayi magana",
Take tai tsit kamar anyi ruwa andauke wajan,.

Cikin tsananin tashin hankali yace "mainai maki dan Allah dazakimin danya hukunci haka?"
Zaro ido tayi takai fuskarta gab datashi tace
"Hamza tunda nasa 'kafata gidan ubanka kahanani zaman lafiya kahanani sakat gaba daya nida 'ya'yana abanza muke gunsa, yafifita sonka fiye da kowa, danhaka yanzun sonake naga karyar tsiya, sonake naga inbaka shi zairayu ko zaibika, inma yarayu nizan turoshi gareka",
Lokaci daya zuciyarsa tai rauni yace "toh duk akanmai kike haka, dan Allah kitaimakeni kinsan inada marayu idan fannin Daddyne wallahi zangayamai abunda yake baikyautawa yachanza dan Allah kimin rai",
Murmushi tayi ta no'ke wuya tace "a'a ada kenan, amma yanzun fansan raine, shinma inmaganar yarane karka damu zanturosu gareka", gabadaya suka fashe da dariya banda Hamza dake ganin abun kamar almara, yakallah Maryam dake hawaye yace "Hajiya duk abunda namallaka zanbar maki kiyi hakuri kibarmu mutafi  zanyi kaura da yarana natafi inda bazaku sake ganinmuba zanhakura da Daddy nasan zaki kula dashi" dariya tayi tashafa fuskarshi tace "'Dana Hamza kaban tausayi wlh da kafin Kamal yarasa ransane ta sanadiyarka dana karbi dukiyar narabu dakai"  ta daure fuska tace "amma yanzun wlh bazan rabu dakaiba"
Yakallah Maryam dake kuka cikin tausayawa yace "toh ita kuma wannan maitaimaku?"
Kallonta Hajiya Sadiya tayi tace "gani nayi ita kadai tasan shirina kuma ni banson barin baya da 'kura, kaga dole kutafi tare"
"Hajiya kiyi tunani" yafada yana kallon kwayar idonta daba idon imani, kwatankwacin kallon dayake mata take mai batare da kibtawaba tace "kawai ku kasheta", take Baushe dake tsaye yasa kasan bundiga yubu kan Maryam tirrr jini yahau tsalle yana kwarara,,
Ganin haka Hamza yai matukar firgici jijiyoyin kanshi suka tashi 'baro 'baro yazaro ido atsorace yakallah yada jinin Maryam yai tatsa-tatsa akasa yafasa gawurtaccen iwu,.

****************
Bayan kwana biyu Alhaji Shehu nazaune bayan yagamashan maganin saukar da zazzabi wayarsa ta buga, dasauri yakallah dasaran yaga kiran Hamza sai Alhaji Bello yagani kan fuskar wayar,
Take yaji gabansa yafadi, yana kallon wayar na kugi harta katse baidauka ba, yana tsaka da zancen zuci wayar tasake bugu daidai da shigowan Mama ta'karaso takalleshi tace "ah Alhji bakaji wayar na 'kugiba", daganin sunan Alhji Bello tadauka dasauri tace "gashi", yakarba yana kallon kwayar idonta ganin halin dayake ciki taimai alaman tambaya da hannu, baibata amsaba ya'amsa sallamar da Alhaji Bello kemai suka gaisa cikin aminci dukda yana iya tantance yanayin aminin nasa balafiyaba awayar, yace "am inafatadai lafiya ko Bello yawajan Hamza",
"Balafiya ba Shehu inacikin mayuwancin hali narasa tudun dafawa, narasa ina zanbi zuciyata ko abunda nake gani zahiri",
"Maike faruwane" Alhji Shehu yafada cike da damuwa,
Cikin dar da 'dacinrai Alhj Bello yace "dan Allah Bello inafata zakaba hukuma hadinkai yanzun haka SSS nahanyan zuwa gidanka kan binciken 'batar Hamza, inaso kasan zuciyata nagayamin babu sahannunka amma bincike yanuna kanada sa hannu dumu-dumu kuma kasan ba abunda yarinyarnan Ushna bazata iyaba, watan baya yafada hadari duk asanadinta,,,,"
Dasauri Alhaji Shehu yakatseshi yamike yace "karka bari shedan yai tasiri azuciyarka Bello wlh saidai inmakircin makiya ya za'ayi nacutar da Hamza 'dana ko Ushna saidai ace rashin kunya amma ina Ushna zata hada kai da 'yanta'adda? saidai ko makiya abokan hamaiyarka na siyasa, Bello kadai natsu kaduba lamarin,,,,,"
Jin anyanke kirar ya'dago kai yakallah Mama data dafe kirji tace "mainene kuma?", cire hullar kansa yayi yai jifa dashi yace "abunda nakeso dake duk halinda zaki kasance inna tafi kikasance maijuriya kuma kiba Yusuf baki karyai yunkurin wani hauka yadda zasuzo sutafi dani lafiya haka zandawo lafiya",
Tuni fuskarta tajike sharkab da hawaye tace "ina zasu kaika?" Zaibata amsa yaji ana kwankwasa kofar gida, yaisauri ya laluba hular daya jefar yace "sunzo kiyi zamanki anan karki damu", zaiwuce tarungumeshi tabaya tana kuka tace "wallahi ba inda zaka babu abunda kayi", dakyar yafuncike hannunta biyu data 'kankameshi yace "kikwantar da hankalinki gaskiya zatai halinta",
Yaja dasauri yawuce tabiyoshi dasauri ya'karasa baibi takantaba yabude gida yatari jami'an tsaron dasuke tsaye da ba'ka'ken suit yace "barkanku dai",
Yauwa suka amsamai suka gaisheshi tare da fiddo farar takarda babban cikinsu yabudemai yace "ranka yadade anbamu izinin kamaka bisa sace 'dan mataimakin Governor dakayi", dasauri Alhj Shehu yace "anadai zargina ko? Karkace na aikata", aiduk shedu sunhallara akanka ranka yadade, muje" yafada fuska a murtuke,.
Kanya 'daga 'kafa Mama tasake rushewa da kuka harda sa hannu aka tace "nashiga uku", fuskarta yashafa yajanye hannun data daura yace "karki damu in anzo bincikan gida karki taurinkai kibada hadin kai sannan dan Allah karkiyi yinkurin nemo lawyer kuyi hakuri gaskiya tai halinta dankar a'bata zumunci bakidaya",
Yaja yawuce yabarta tana rusa kuka tuncin karfinta har yashiga mota.

**************
Gaba daya satin Ushna da Fidyan a hargitse sukayi sa, da yazo inda take zata mike tabarmai wajan, duk yanda yaso ya kebe da'ita abu yaci tura tun yana ganin abun kamar wasa har yalura Ushna da gaske take,
Satinsu daya cirr agidan ya mamayeta tsanmaninta yafita tafito tana shawagi da yaranta kamar sakarkiyar tsuntsuwa, nan Allah yabashi sa'a yai ram da dantsen hannunta yace "ke baki da hankaline duk wannan abun namainene?" Atsorace tajuyo ganin shine tasaki tsaki tace "namainene kuwa? Inafatan bazakace kana kulaficin wannan BAZAWARAR ba" tanuna kanta tare da 'dagamai gira,
Tsaki yaja yace "dama duk akan wannan ne? Toh ke ba bazawarar bace? Nan kikaje gidan radio kika nunama duniya irin kaunar da kikema sakaran tsohon mijinki, agaban idona a asibiti kika watsamin 'kasa a ido duk naji nagani nadauka yanzun narungumeki lokacin da Ubanki ya watsar dake shine zakice bawanda zaki wulakanta yanzun saini? Wlh karyarki, abunda nadauka da yanzun bazan daukaba"
Zuciyarta ne kawai ke tafarfasa tarasa abun cemai, lamarin Fidyan gaba yake dadayi yazama tsiya, azahiri tafurta "natsaneka", fal ya tsinketa da mari ya janyo gashinta yace "tun yaushe? Toh ni tunran da kika auri wancan shegen na tsaneki, amma nataba gayamaki?" Atsorace tazaro ido tace "inka tsaneni harhaka to maiyasa kadunga bibiyata harka rabani dashi Fidyan?" Tafada cikin tsawa tana kallonshi da kwayar idonta dayai jajir tattare da tsanarsa,
'Kara sha'keta yayi yace "sabida banson ganinki da kowa" wani irin ziririn hawaye yabi kuncinta tuna Madina da Fahad datayi tace "Fid bakasan ganina dakowa bakasan ganina da iyayena? harda Madina da Fahad da suke  bu'katar Uwa suke bukatana fiye da kowa?" Tsaki yaja yace "waike bazaki barkawomin maganar data shafi Hamza bane, Madinan banza natsani jininsa" ya mangareta tabugu da jikin cushion, zatai magana ya'dago fuskarta yasa bakinsa cikin nata zai kiss ta tureshi da karfi ta rungume hannunta tana hawaye tace "waikai wani irin jakine?",
"Jaki" yamaimaita yana kallon fuskarta daya jike sharkab da hawaye,
Cikin zafin rai yayo kanta yace "barin nuna maki aikin jakkanci" ya tube wandonsa tare da cire botiran rigarsa yayo kanta,
Duk yadda taso ta tureshi tanaji tana gani yasa karfi yarabata da kayan jikinta yana fadin "ai dama dahaka Hamza yai nasaran shiga ranki, nikuma yau sonake naciresa a ranki, banso kikara tunanin wani 'da namiji saini",
Cikin zafin nama tai wuff tatureshi tafada kitchen da gudu tasa key tahau ajiyar zuciya hannunta nakan kirjinta,.
Tsaki yaja yabita yabude kofar yajita akulle yayi-yayi ta bude taki, abakin kofa yace "Ushna yau zansaki kiyi danasanin furtamin kalmar tsana, sainasaki kinsoni kinmance da kowa da komai murayu nidake cikin farin ciki agidannan gwanma kisani danni akayoki",.
Yawuce,.
Saida tashafe awa biyar akitchen jin cikinta nakiran ciroma take ta tuna Hussaini da Hassana data barosu parlour tunsafe, dasauri tabude 'kofa batare da shakkan haduwarta da Fidyan ba tafice, tana tafe tana aiyana toh lafiya ni ko kukansu banjiyoba insun farka,.
Koda taje Parlour taga basu ciki tadawo 'dakinta taduba ko tabarsu nan, nanma basu,
Lokaci guda taji zuciyarta yafara bugu tara-tara, ahaukace tadawo tahau duba duk wani kusurwa nagidan basu, nan aguje tafita harharabar gidan basu ba alamarsu,
Nandanan tahau kwarara zufa zuciyarta nabugu 'dari akowani 'dakiki taje ga dirowar (wardrobe) din kayansu gaba daya basu, koda taduba jakar kayan madararsu duk basu, babu wani sili ko alaman Hassana da Hussaini dayai saura agidan,...
Jiki nakyarma tahau kwada kiran sunan Fidyan kamar zautatta tana fadin "Fid-Fidyan a'h ina kakaimin 'ya'yana" takare da rusa kuka mai sauti,.
Ganin kuka bazai fushshetaba ta 'dauko wayarta daya siyamata sabuwa fil tare da Sim tabude tasa numbersa, koda takira sai jinta tayi akashe switch off, takira yafi so dubu stwitch fa, tana daga tsaye taji duniyar na juya mata tana kiran wayarshi tana gani dushu-dushu har idon ya rufe kib tafadi sumamma.

Yamakomar abotar Alhaji bello da alhj shehu, hajiya sadiya da Hamza agefe ga Hamza da Hajiya Sadiya?.
Kuyi vote kuyi following dan samun pages dazaran na daura.

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now