WASIYAR AURE 30

750 176 9
                                    

WASIYAR AURE😭❤️❤️

By: Najaatu shehu naira
Wattpad: Najaatu Naira

FKD Production Fans Writers 《《30》》

Har gado yakaita yakwantar, zaijuya yafita tarike hannunsa dasauri ta matse,
Cikin muryar da bata fita tace "dan Allah karka tafi, katsaya kusa dani"
"Toh" kawai yace yakoma yazauna yana rungume da Fahad yakalleta ahankali yace "kidaina kukannan haka, kinsan bansan 'bacin ranki"
Yanda yaimaganar ta'dago kai takalleshi cikin ido tace "sabida mai?"
Kasa janye nashi idon yayi daga nata yakuma kasa bata amsar tambayarta ahankali ya janye jikinsa yacanza zancen yace "zanje na kwantar da Fahad adakina, saiki samu kihuta",
Haryakai bakin 'kofa zaifita cikin kuka tace "toh amma mai naimasu dazasumin hukunci irin wannan? Fid yacanza yadaina sona"
Cikin kuka ta'karasa maganan tana fadin "laifina daya auren dole da akaimin amma daidai darana daya banta'ba cireshi araiba sabida ina matukar kaunarsa, inasonshi shi,,,,"
Baitsaya yacigaba da sauraronta ba yayi wuf yafice,
Jin sambatun nata yake kamar tana sokamai mashi a'kahon zuciya
*******

Fidyan nasauke Maryam takalle yadda jikinsa ke 'bari tace "Love karfa ka'daga hankalinka akan Ushna domin ita tadade da mancewa dakai yanzun tana zaune lfy 'kalau da mijinta" ganin hankalinsa baikanta tata'bashi tace "Love", zunbur yajuya kamar mai firgici yace "kije zamui magana",
Batace 'kalaba tatafi hartayi nisa tajuya takalleshi cikin kwayar ido tace "Fidyan zangayama gsky, wallahi karka kuskura kace zakai amfani dani danka 'kuntatama Ushna, dont use me"
Baitsaya bata amsaba yaja motarsa yabartanan tsaye,
Ganin yadda yaba'deta da 'kura ta cije le'be tare da 'kwafa tashige gida.
************

Saida Ushna tai kwana biyu bata fitowa konan da chan,
Duk yadda Hamza yaso yaganta koyasan halin da takeciki abu yaci tura, duk wasu sabgoginta adaki takeyinshi, batare da tayi mu'amula da kowaba,
Domin dazaran safiya tayi zata turo Fahad parlour yacigaba da rarrafanshi da wasanni harsai Hamza yafito yadaukeshi koma sufita yawo tare,

Hakan yasa hankalin Hamza yatashi kwarai, yabugama Dr Usaini waya yaimai bayanin duk abunda kefaruwa,
Shiru Dr Usaini yayi kanyace "Hamza inaganin zaifi ka sawakema Ushna inhakan zaisamar mata farinciki da kwanciyar hankali",
"Wannan tuni nariga nayi Dr, domin dazaran Ushna tahaife abun dake cikinta zanbarta tai rayuwa yadda takeso takuma auri wanda take kauna, amma saidai kafinnan banso naga zubar hawayenta ko naganta cikin kunci, hakan na 'dagamin hankali Usaini",
Shiru Dr Usaini yayi yana nazarin wannan sabuwar 'dabi'a ta Hamza, shin Hamza yafada soyayyane kokuma tsabar kulane saidai koda kulane toh tabbas,,,,,"
Jin Hamza nakwadamai kira ya watsake daga duniyar tunanin daya fada yace"Abokina kasan kowa da fanninsa wallahi Ni ayanzun banda wata shawarar da zanbaka, saidai inhadaka dawani likitan halayya(psychologist)
Dr Aliyu Haydar insha Allah zai taimaka kwarai,"
Cikin hanzari Hamza yace "turomin Numbersa yanzun", yayanke kirar,

Ba'afi 'yan sakonniba Dr Usaini yaturomar,
Ba'bata lokaci Hamza yakira layin,
Kira daya yadauka suka gaisa Hamza yaimai bayanin kansa da halin dayake ciki,.
Atsanake Dr Aliyu yace "gaskiya yanzun bana 'kasar amma domin fito da 'bera daga rami dole saika tanadi daddawa, ayanzun kayi 'ko'kari kasan yadda zaka rabata da zaman kadaici harnan da wata guda kan indawo,
Yaso innadawo zanbaku appointment sai kuzo kusameni a office",
Godiya Hamza yaimai sosai kan yakashe wayar yasaki ajiyar zuciya,.

Washe gari dasassafe yadawo parlour yazauna bayan ya idar da Sallah Subhi yatasa zaman jiran fitowarta,

Karfe bakwai ta bude 'kofa kamar yadda yai tsanmani zata ajiye Fahad yayi sauri ya ri'ko 'kofar atsorace ta zaro ido sukai ido hudu yana kallon cikin kwayar idonta da sukayi luhu-luhu dan kuka,
"Maikakeyi anan" tafada cikin sanyin murya,
Baisan sanda yasa hannu yana shafa fuskarta datai fiyaun sabida tsananin rama da lalacewar datayi,
Ta lumshe ido tare da ajiyar zuciya ta janye hannunsa zatai magana yace "i'm sorry Ushna, kiyafemin",
Cike da rashin fahimta tace "namai"
"Nakomai, komai a sanadiyar aurena dakikayi yafaru, nakuma maki alkawarin farin ciki nagaza, kiyi hakuri",
"Karka damu 'kaddara tace" tafada tare da 'dan ziririn hawaye
"Sai anjima" tafada tare da banko 'kofar,
Yadade jingine abayan 'kofar idonshi nakallon sama ceilling, kafin yayi ajiyar zuciya yadauki Fahad dake rarrafe a tsakiyar Parlour yakoma dakinsa.
Tun bayan ganinsa da Ushna yakasa samun nutsuwa, hankalinsa yatashi kwarai ganin yadda ta rame kamar kudin guziri,

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now