Wasiyar Aure 02

1.4K 268 4
                                    

Wasiyar Aure😭❤❤

By; Najaatu Shehu Naira

FKD Fans Writers 《《 02 》》

Littafina bana kudi bane kuma bansaki/ka dole karatunba, idankuma kinyi ko kayi toh dannamin Vote ko ka/kidaina karantawa.

Kiran sallah farko Ushna dakekan kirjin Fidyan taduro,
Asukwane ta janyo jakarta da sauri taciro waya takallah,
Iwuh tasaki ganin lokaci, karfe uku darabi na dare 3:30am.
tasa hannu dasauri ta daki kirjin Fidyan dake barci,
Ya farka afirgice,
Ta fashe da kuka tace "Fidyan nashiga uku, wlh kagama dani, yau nasan Mama saita kasheni,"
Tana kuka tana janyo kayayyakinta cikin sauri tasa takalmi zata wuce yayi wuf yariko hannunta dasauri cikin rarrashi yace "Mine ina zakije cikin darennan pls ki tsaya dan Allah",
Wani irin kallo taimai jiki narawa tace "ya zaka kabarni nayi barci anan, Fid kasan agida bana kwanan waje kasan halinfa Mama fissabilillah",
Hawayen dakebin fuskanta ya goge,
Idan dakwai abunda Fidyan yatsana shine 'bacin rain Ushna,
Ya 'karbi jakan hannunta murya narawa yace "toh idan bazaki bari gari ya wayeba, muje na kaiki dakaina zan amsa duk laifin, kinji",
Kai kawai ta gyadamai
Ta sassauta masifan ganin hankalinsa ya tashi jikishi yayi la'asar,
Cikin hanzari yaje wardrobe dinsa dasauri yasa doguwar riga Jallabiya fara tare da dauko makullin motarsa ya kalleta yace "Mine muje",
Tana tafe yana binta abaya har bakin motarsa 'kirar Benz Gla E550 2019 fara,
Yabude mata gidan gaba tashige,
Yazagaya dausari yashiga yatada motar,
tare da yima mai gadi horn,.

Minti goma yakaisu Malali GRA Alhaji Abdullahi Closed,
Ta kalleshi jiki narawa idanu nandanan sunyi luhu-luhu tace "Fid kakashe fitilar motarnan gwanma inyi sneaking inshiga tunda inada Key ahannuna, kaga Mama bazatasan yaushe nadawo ba",
Bai mata musuba ya kashe fitilar, cikin lallashi yariko hannunta ya hada da nashi cikin sanyin murya yace "nace maki karki damu, zanyi magana da Mama dakaina bazataimiki komaiba",
"Uhhm" kawai tace.
Yayi parking bakin gate tafito ta kwankwasa Gate din gidan ahankali,
Malam Garba maigadi ya le'ko kai cikin barci suka hada ido,
Yana ganinta yahau bude 'kofar cikin dabaru gudun kar Mama taji 'kara ,

Malam Garba mai Gadi abokin cin mushen Ushna ne,
Yasan duk yanda zaiyi ya kare laifinta wajan Mama, hakan yasa koda yaganta yasan baya bugatan tagayamai laifinta,
Sarai yasan bata kwana agidaba,.

Cikin ra'da Malam Garba yace "Ushna ya'akayi yau kika dade haka, tun biyu nake jiran dawowarki kuma naga Mamanku tadamu dayawa domin batafi munti goma da kashe wutan dakintaba yanzu, kuma nasan ke take jira",
Ba'karamin duran ruwa cikin Ushna yayiba, ta gwalalo manyan idanunta tadafe kirji tace "nashiga uku",
Da gudu taje ta janye Fidyan gefe cikin muryan kuka tace "Fid bazamu shigaba,"
"Toh ina zamu inbamu shigaba? ai gwanma muje mubata hakuri ko",
Fid yafada yana kallon kwayar idonta da suka cika da kwallah.
Wani irin kallo taimai ta matse hawayen ta shartar da bayan hannunta tace "Fid Mamanmu fa ba'irin Mommynku bace Black America, rayuwar ture,
Ita Mama idan tasan tare muka kwana wlh bazata bari muyi aureba, aurar dani za'ayi cikin yaran Abokan Babanmu kamar yadda akaima Anty Rayhana",
Ba'karamin furgita yayi dajin furicinta, nandanan yarasa tayi jiki narawa yace "toh Mine yazamuyi?"
"Muje ka kaini gidan Anty Rayhana sainace acan nakwana",
Bamusu jiki narawa yace "toh muje".

*********
Rayhana nazaune bayan sun idar da Tahajjud tana lazumi,
Madina nagefen Hamza yana 'karamata hadda kamar kullun,
Kiran wayar Ushna ya fado ta kallah screen din,
Azahiri tafurta "Ushna ko lafiya?",
Bata 'kara da'ki'kaba tadauki wayar dasauri, tanayi tana kallan Hamza da Madina da suka zuba mata na mujiya,
"Toh", kawai tace,
Ta tashi dasauri zata fita,
Hartakai bakin 'kofa Hamza ya dakamata tsawa "ke wai'ina zaki haka",
Jiki narawa tajuyo ta kalleshi tace "Ushna nawaje takirani zanje nabude mata 'kofa, kuma naga kamar kuka take"
Jinhaka Madina tataso dagudu cikin murna tace "laaaa My Mummy tadawo",
Zata fita da gudu Hamza ya mike dasauri yanuna mata yatsa yace "Munawwara wlh idan kikasake kikafita nidake ne,"
Guntun tsaki Rayhana taja ganin bata'ita yakeba, zata fita yace "nace kitsaya zanshigo da ita ko".
Cikin takaici tace "haba dan Allah Diamond Yarinya nawaje tanajirana kai katsaya nankana masifa",
Uffan baiceba ya fice yabarsu tsaye cirko-cirko.

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now