Wasiyar Aure
By; Najaatu Naira
FKD Fans Writers 《《 04 》》
Wani irin kallo ta 'dago kai taimai,
Batace uffanba ta tashi takoma kan sofa yabita yazauna gefenta,
'Kala baicemataba sai kwayar idonsa da yazuba mata mai narkar da zuciyarta,
Kasa janye nata idon tayi kan nashi sbd wani irin yanayi tashiga domin 'karara take ganin tarin zunzurutun kaunarta akwayar idon Hamza,
Gajiya yayi ya lumshe ido ganin ta tsunduma cikin kogin tunani,
Yasa yatsun hannunsa yaka'damata daidai zara-zaran kwayar idonta data sha'afa ga kallonsa bako 'kibtawa,
Gajiya yayi ahankali yadafa kafardarta,
Nandanan tadawo haiyacinta harda dan razana, cikin sanyin muryar ra'da yace "Beauty tunanin maikike inakusa dake",
Langwabe wuya tayi tadan mazaye hadi da karka'da fararen kwayar idonta tace "lafiya, badai kakai 'karana ba?",
Dasauri ya girgiza kai yace "haba Beauty nagaji, laifina baikai hukuncin da kikeminba",
Ganin tasake hada rai yasa yasassauta murya yace "dan Allah kiyi hakuri, am sorry am really are My beauty",
Shiru tayi tana kallonsa aranta ta lumshe ido cikin hamdala tace "wat hav i done to deserve such a Guy like Hamza, kyan halinsa yazarce tunanin mai tunani, lalle nasan amaganar bani dagaskiya domin nasan koda wasa Hamza baya karya, mutunne mai magana daya, amma ji yadda yake rarrashina nikaina nasan inyana kusa dani ba Hamza danasani bane shekara biyar dasuka wuce wannan wanine daban Lover Guy maison farinciki da kwanciyar hankalina",Hannu biyu yasa ya janyota kan faffadan kirjinsa hadi da shafa fuskanta yace "tunanin maikike wai? Kirage tunani kinsan kinada ciki",
Ajiyar zuciya tayi ta'kara manneme,
Baiyi 'kasa aguiwaba ya'kara rungumeta kyam ajikinshi, cikin murya maikamar ra'da yace "I love you My Beauty, ina matukar kaunarki",
Zata bashi amsa jin ana kwankwasa gida tadago suka hada ido tace "waye?"
No'ke wuya yayi yace "ina zansani, muje muduba",
Wani irin kallo taimai tace "kayi magana da Daddy yanzu kace baka saniba? Hmmm kaje barinsa Hijab nafito mugaisa"
Murmushi yayi cikin annushuwa da annuri fal fuska yace "toh My Beauty",Abakin 'kofa yatarar da Alhaji Bello yana tsayuwan jira,
Hamza nabudewa yayi sauri ya rungumeshi yace "Daddy",
Murmushi Alhj Bello yayi, ya'dagoshi yanayi yana kakka'bemai jiki cikin kauna da begen 'Dansa yace "ya'akayi Hamza gashi duk karame",
Tafin hannu Hamza yasa dasauri ya toshe bakinsa,
Murya 'kasa-'kasa yace "Daddy munshirya dan Allah karka taso da wata magana"
Kasake Alhj Bello yayi yana kallonsa yace "toh meye dalilin kirana?,"
'Kugu Hamza yarike yace "toh aidama danta saukone kuma tasauko ammani bance kazo kaimata fada ba"
Ko kallo bai'isa Alhj Bello ba yace "matsa nawuce ciki mutumin banza,
Hamza ya rike kai cikin 'dar yana kallon Daddy har ya'kure",Jin sallamar Alhj Bello Rayhana tafito dasauri cikin Hijab mai hula, yanayin kamala dasanin darajar kanta yasa kullun Alhj Bello bashida labari sai nata,
Ta dur'kusa har 'kasa ta gaisheshi,
Cikin annashuwa ya amsa, yana samata albarka,
Akunyace tatashi tace "Daddy bari azuboma abinci",
Daidai Hamza yashigo yana ra'be-ra'be,
Alhaji Bello yana murmushi yakalla Hamza yace "dakata Rayhana Mijinki yakawomin 'karanki shiyasa nazo",
Dago kai tayi da zara-zaran idonta ta saci kallonsa, karap suka hada ido yarike kai dasauri yasa yatsa abaki yana girgiza kai yace "Daddy yaushe mukayi haka dakai? Rayhana 'Yar albarka nikuwa maizataimin dahar zankai 'karanta",
Ya'kara marairaice murya yace "Allah sarki Daddy kai wani irin Sirikine kazo hargidan Mace yimata fada",
Saukar dakai tayi domin irin tatsuniyarnan tasu tasaba ji,
Alhj Bello yagyada kai yace "toh 'Yata dadai nazo baki hakurine amma nafasa gashinan wlh duk abunda kikaga dama kimai,"
Yatashi ya kakkabe kaftaninsa ya kalleta yace "Munawwara fa?"
"Tayi barci" tafada atakaice,
Ya mi'kamata bandir din daribiyar dubu hamsin yace "gashi kiyi hidimar sallah",
Godiya tayi sosai,
tayi-tayi yatsaya yaci abinci ya'ki Hamza nafadin "akoshe yake basai yaciba" suka rakashi harmota.*************
Alhaji Bello deputy Governor of kaduna state,
Mutunne mai barkwanci,
Arayuwar Bello mace daya yaso aure tun saurayi dabudurwa auren so wato;
Hajiya Fatima Mahaifiyar Hamza,
Bayan aurenta da Alhj Bello da shekara Daya Allah yadauki kwananta wajan Haihuwa,
Hakan yasa tausayi, jinkai begensa gabadaya yadawo kan Hamza ganin rikon sakainan kashin da Amaryarsa Hajiya Sadiya kema 'Dan,
Daganan yarage duk wasu ayyukansa na office baiyarda yabaiwa kowa ru'konsaba yairenonsa har matakin girma,
Kana yaturasa karatu waje(abroad),***********
A cushion yasameta tanazaune tazabga tagomi, bayan yadawo rakiyar Mahaifinsa, dasauri ya 'karaso ya zauna gefenta yana 'dan ya'ke da kame-kame,
Fuska ta'dago ta kalleshi tasaki murmushi tare da zuban kwallah,
"Innalillahi lafiya Beauty" yafurta yana kallon kwayar idonta,
Tafin hannu tasa agefen sajensa tana shafa fuskarsa tace "Diamond wannan wani irin kaunace, nasan Daddy duk abunda kakeso yanaso amma aganina bancancanci wannan kaunarba, tayi tsada gareni",
Shiru yayi na'dan mintina azahiri abunda tafurta yamai dadi amma salon maganar yasa yanayinsa yachanza.
Hannunsa yasa yaimata yafice alamar tazo da ido ya zaunar da'ita kan cinyarsa,
Yasa hannu yashare hawayen dake kan kuncinta yafara wasa dayatsunta cikin sanyin murya yace "baki sanniba Beauty kika baro iyayenki domin rayuwa dani, bakida buri saina son farantamin tare da neman aljannarki,
Rayhana banida Uwa toh idan bankyautatamiki nasokiba wazanso? Shawarar dazan baki shine gwanma ki adana hawayenki domin indai kukan farincikine kindunga yinsa kenan, tashi muje mukwanta 'Yar Beauty na",
Lumshe ido tayi tace "toh,"
Ya cinci'beta sama tafashe da dariya tana wasa da kirjinsa tace "kai bakajin nauyine?, dauka kabari saina haihu,"
Dasauri yagirgiza kai yace "ganin farincikinki yau 'daya tak naji kamar anyayemin duk wata gajiya da damuwa dake damuna, ina matukar kaunarki Matana",
Murmushi tayi ta lafe kanta kan kirjinsa tare da lumshe ido cikin farinciki harya kaita dakinshi yakwantar,.**************
Ushna nazaune gefen ruwa (swimming pool) cikin swimming suite tarike iphone 11pro max dinta tana daukan Fidyan hoto dake cikin ruwa yana swimming,
Daga gefe "Maryam Mera Aminiyarta" nazaune tana latse-latsen nata wayar,
Ushna tajuyo cikin zumudi tace "Qawata kallah My Fid gayannan yahadu kamar shi yayi kansa, aini dazaran Allah yasa na'aureshi ba'aimin auren doleba irin Aunty Rayhana ai indai a duniyane toh wlh Allah yacikamin burina",
Kallonsa Maryam tayi ta gefen ido don wani lokaci tanada miskilanci ta'dan yamutsa fuska tace "ke wallahi Ushna kyan Fidyan baikai yadda kike ganiba, aganin wlh koda Aunty auren dole akaimata Ni Yaya Hamza yafimin, gashi fari dogo ga hanci ga wannan sajen nasa,
Yanayin tsarin jikinsa kawai ba'amagana kinga kirji wow,
Ushna wlh kullun naganshi inna tuna Aunty batasha wuyaba ta aureshi sai'ince tasama dami akala,
Ushna Yaya Hamza ga class shiko amaza bada kowani Tom and Jerry zaki ganshi ba, ga kudi ga ilimi gashi musulmi cikakken bahaushe 'Dan dangi, toh mai mace zata nema bayan wannan?",
Ushna dake sauraranta nandanan ranta ya 'baci tana maganar ji take kamar tazubama fuskan Maryam lafiyayyan Mari, takalleta hadi da tsaki tace "ke bakomai bane nasan hassadace kawai ke'dawainiya da rayuwarki, inba hakaba inama Hamza yaga farin da harza'azauna ana magana akai, ina Hamza yakama 'kafar Fid akyau"?
Charab Maryam tace "eh keda kikeda haske kamar tsada aibazakiga farinsa da kyauba, amma Ushna ko Aunty Rayhana zaifita fari"
Tsaki Ushna takumaja tacigaba da daukan hoto chan kamar an tsakureta tajuyo tace "ke kodai kinta'ba cusa kanki wajan Fidyan ne yace baiyinki shiyasa kike wani so kidunga kusheshi, domin inba keba keba babu wani maikushe Fid 'dina"
Yanda tayi maganar tana kallon kwayar idon Maryam yasa Maryam tasan badawasa takeba dan zafin kishi irinna Ushna baikyale kowaba,.
Maryam tagyara zama tace "kinsan Ni Maryam nafi karfin cusa kai wajen 'Da namiji, kuma Ushna Duk wannan abunda kikefa idan Allah yayi bamijinki bane haka zaki hakura"
Cikin zafinrai Ushna tace " toh aisaiki rabamu kinji",
Suna cikinhaka Fidyan yafito daga ruwa yazo daidai gurinsu, fuska babu annuri yace "Mine banace kije kichanza kayaba, dubi gaba daya mazan wajannan idonsu nakanki,"
Juyawa tayi takallah wajen ta ta'be baki tace "Fid kowafa aiki gabansa yake, kaidai muje kacanza kaya karkayi mura nima daganan saina chanza",
Yamika mata hannu tarike yasa dayan hannun daidai 'kugunta yajanyota jikinshi,
suna tafe suna nishadi yana wasa da'karamin towel dindake hannunsa,Sunyi nisa tatsaya chak takalleshi tace "Fid ina wayarka?",
Yakallah jikinshi yakalleta yace "baki daukoba?"
Ta girgiza kai,
Ya no'ke wuya cikin sanyin murya yace "maybe nabarta bakin ruwa mukoma",
Sunkai zata dauka santsin ayaba yajata tipp tafadi,
Nandanan tayi habo jini tahanci tabaki,
Iwuh tasaki nandanan hankalin su Maryam yadawo kanta,
Fidyan ya'dagota dasauri daniyan taimaka mata qashin hannunta yace 'bal............Maryam Mera nacika alkawari👌.
![](https://img.wattpad.com/cover/227361078-288-k99320.jpg)
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...