Wasiyar Aure😭❤❤
By: Najaatu Naira
FKD Fans Writers 《《 07 》》
Ganin tana kokarin fita, Hamza yamatso yana watsama Fidyan kallon tsana,
Yakalleta cikin rarrashi duba daganin yananyinta yace "lafiya Rayhana mainene",
gudu-gudu cikin raunatacciyar murya tace "Ushna takarye Hamza babu wanda ya'iya gayamin harkai tsakani da Allah"
Tashare hawayen dakebin kuncinta da gefen hannu taja hanci cikin fushi tace "yanda kowa yatsana Ushna nasan ko mutuwa tayi babu maigayamin, maita tsaremaku Fissabilillah,",
Bata jira amsarsaba takallah Fidyan dayai sankwarakwai tace "Fidyan muje kaji kakaini",
Dasauri Hamza yariko tsintsiyar hannunta yace "dan Allah kidakata mana targadene kawai, Mama tagayamin sabida ganin yanayin cikinki ga lalura yasa akace aboyemaki dan karhankalinki yatashi, shiyasa kikaga bangaya makiba amma muje nakaiki yanzu, jeki sanyo hijabi nafito da mota mutafi",
Sanin yafita gaskiya yasa tayi shiru bata jaba,
Takama hanya dasauri taje tasa kayan da Fidyan yakawo cikin wardrobe ta dauko hijab tasa hadi da riko hannun Madina tafito,
Har lokacin Fidyan na tsaye, taimai sallamah tashige motar Hamza suka tafi.Suna isa Hamza yatsaya yima Garba maigadi horn yabude taga bazata iya jiraba tabude motar tafice dasauri tahau kwada sallama tana kwankwasa gida.
Mama tafito dasauri tabude jin muryan Rayhana,
Ganin Rayhana tayi tsaye tana goge hawaye, atsorace Mama ta'karaso tace "lafiya Rayhana mainene",
Hawaye kawai ke kwaranya daga kwayan idonunta tace "Mama ina Ushna?"
"Tana dakinta", Mama tace atakaice,
Hadi dabata hanya tatafi da sauri harda ha'dawa da gudu tahaye sama.Ushna nadakinta tayi zugum tasa hannu bibbiyu tazuba tagumi kamar anturo mata sakon mutuwa, duk abun duniya yabi ya'isheta,
Kallon agogo take tana 'kirga, dagakan Seconds, Minutes har hours dinrabonta da Fidyan.
Jin kiran Rayhana yasa Ushna firgit ta farfado daga kogin tunanin data tsunduma,
Dasauri tataso ta rungume maikaunarta daya tilo dukduniya kamar yarda take ikirari, takalleta cikin fuskan tausayi tace "Anty",
Lokaci daya tasa kuka harda shashsheka, tanayi tana zunburwa,
Ganin Rayhana mairarrashinta kawai yasa zuciyarta ta narke taji kukan nazuwa ba 'kakkautawa,
Rarrashi da banhakuri Rayhana tahauyi tana shashsharemata hawaye.Jikin Rayhana yayi sanyi zuciyarta taha sa'kamata irin azabtar da Ushna da akeyi,
Ta dagota ta'kurama ta'kurama jikinta ido kamar mai scanning,
Lokaci daya taga Ushna ta 'kara ramewa kamar kudin guziri, wuyarta takwanjale daga ita sai 'kashi, Rayhana ta rintse ido hawaye wiwiwi babu maibama wani hakuri,.
Shigowar Mama tahau yimasu tsawa cikin fada tace "tashi maza kikoma gidan mijinki tunda babu maima wani fada, kinkama kinbiyema shashashar Yarinyarnar kunzauna kuntasa juna agaba da kuka mai akaimaku?""Mama dan Allah kiyi hakuri", Rayhana tafada tana sharar hawaye,
Mama tayi kwafa tace "kitashi kikoma Parlour kinbar ba'ko",
Rayhana ta janyo hannun Ushna cikin rarrashi tace "tashi muje Parlour",
No'ke wuya Ushna tayi tace "ni babu inda zani",
Rayhana ta'kara tausasa harshe cikin rarrashi tace "Dan Allah tashi ki lallaba muje kinji Masoyiyata",
"Zaki tashi kosai nakaimaki mangari",
Mama tafada cikin tsawa,
Da sauri suka tashi Ushna na kibkibta ido kamar zatasa hannu aka tafasa iwuh....Suna isa Hamza ya dage yacije yace "Ushna yajiki Allah kiyaye gaba",
Yitayi kamar batajishi ba,
Aranshi yace "dama sadaka nayi badan ki amsaminba mara kunya",Mama nabarin Parlour Ushna tahau sabon kuka tana fadin "Wlh Anty ba'asona agidannan tunda nayi targa'dannan banfi kwana ukuba nawarke amma Mama tahanani fita tasamin kulle, Anty wuni Fidyan keyifa akofar gidannan kullun amma hakan baisa tace koso daya yashigo yaganniba, Mama tadauki tsanan duniya ta dauramin wlh Anty barin gidannan zanyi, yau zanbiki gidanki zankoma",
Cikin rarrashi Rayhana tace "toh babu damuwa saimu tafi, kidaina kukan bansan ganin hawayenki",
Madina dake gefen Abbanta tamatso tasa hannu kan fuskanta cikin rarrashi tace "My Mommy kidaina kuka zanbaki chocolate",
Murmushi tayi ta rungumeta tace "nadaina Sweetheart shikenan",
Duk zancennan Hamza nazaune dakejin kamar yasa hannu aka yafasa ihu kowani zaitaimaka mar.
Aranshi yake fatan Allahsa kar Mama tabar Ushna tabisu,
Hakan yasamo asali tunfarkon zamarsu da Ushna Hamza baiji da dadiba komadai ince basuji da dadiba, domin duka su biyun babu mairagama daya.Mama nadawowa tasa aka kawo kayan abinci niki-niki yan'aiki,
Takallesu tace "Hamza ga abincinan kuci fitinar Yarinyarnan yasa kunfito gida baku shiryaba, saida nace karta gayama Rayhana amma tayi kunnan uwar shegu tafada",
Ushna tajuya takallah Rayhana cike da mamaki tace "Anty nina gayamaki?"
Dasauri Rayhana ta girgiza kai tarasa abun fada can talauye tace "a'a Qawarta Maryam tagayamin",
Mama tagamsu kwarai tace "ayya dayake bankwabeta ba, karma kidamu domin harta warke dama 'dan targade ne",
Cikin nutsuwa Rayhana suka hada ido da Mama tana mushi-mushi da baki tace "am Mama dama sonake zantafi da Ushna sabida tayani aikace-aikace",
Kwayar idonta kawai Mama takallah tasan karya take,
Saidai kawai takyaleta ta biyemata tace "indai dan wannanne aisaina 'karomaki 'Yar'aiki amma Ushna tana tare dani anan babu inda zata",
Cikin magiya Rayhana "Dan Allah Mama kiyi hakuri kibari mutafi tare, nima zankula da'ita dan Allah kwanannan sai inji cikina nayawan juyamin kibarmin ita kusa dani",
Kasa fadin uffan Mama tayi domin awannan karon zata iyaganin gasky 'karara akan kwayar idon 'Yar'ta ta, saitaji tausayinta yakamata ganin yanda tagama maganar ta 'kas dakai,
Jin Mama tayi shiru, tadago kai suka hada ido da Hamza tace "dan Allah katayani rokonta",
Gudun kar abun yazamemusu fitina yace "Mama kiyi hakuri taje yaso ko bayan tahaihu saita dawo, lokacinma sunkoma makaranta saita tafi gaba daya",
Ajiyar zuciya Mama tayi tace "toh badamuwa tunda kasa baki, amma dan Allah Hamza kaina barma amanar Ushna dazaran kaga tayi badaidaiba ka kwabar mata, karka sake ka sakarmata kodan Yayanta kaji",
Jiki narawa cikin farinciki yace "toh masha Allah",
Lokaci daya Ushna tafara fargaban tunaninta nakomawa gidan Rayhana ganin yadda jikin Hamza ke'bari dajin zancen Mama kamar anbawa kura ajiyar nama.
https://www.facebook.com/groups/459234504875663/

YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...