WASIYAR AURE 28

717 116 7
                                    

Wasiyar Aure😭❤️❤️

By; Najaatu shehu naira
Watpadd; Najaatu Naira

FKD FANS WRITERS 《《28》》

Bude idon da zatayi tayi ido hudu da Mama zaune kusa da ita ta zabga tagumi tare da Madina.
Agigice ta rungume Mahaifiyar tata tace "Mama dan Allah duk abunda nayimiki kiyafemin",
Ahankali Mama tahau shafa bayanta tace "ya'isa Ushna yihakuri Ni bakimin komaiba, kikwantar da hankalinki jarabtace kuma zaki cinye",
Gyada kai kawai tayi, tana lafe jikin Mama, takallah Madina data 'kuramata ido tajanyota jikinta tahada ta rungumesu baki daya,...

Wuni Mama tayi agidan tana tarairayar Ushna inakasaka inakacire,
Wannan sauyi na Mama ba'karamin dadi yaima Ushnaba, aranta tace "ashe nima ana sona",
Hakan yasa tadada sakin jiki ta narke wani abunma daganga take fadin tanaso dazaran taji ranta yabiya.

Karfe tara nadare Hamza yashigo tare da Yusuf,
Kamar almara Ushna tatashi tana kallonsa, bata ankaraba taji hawayen farinciki nabin fuskarta tuna rabonta da ganinshi tunkan tafara makaranta, shekara biyu kan na'uku suna shabanban ko yazo tatafi ko tadawo shi yakoma,
Tana tsaye tana washe baki yaja kanta kan kafadarshi cikin sanyin rai yace "Qanwata nayi kewarki, naso zuwa tun rasuwar Anty Rayhana amma bansamu damaba",
Dasauri ta'dagokai cikin jajantawa tace "yanzun kasama hutune?",
"Aa" yagirgiza kai yana kallon kwayar idonta yace "rashin lafiyarki tadawo dani, nasan bakomai ke 'dagamiki hankaliba sai rashin Aunty Rayhana, ni zanzame maki makwafinta, babu sauran gaba tsakaninmu",

Tunda yafara bayani Ushna tatsinke da lamarinta,
Take yai nasarar saremata duk wani 'karfin gwuiwa,
wani irin zafi da radadi xuciyarta keyi tana aiyana  "shikenan nima mutuwa zanyi, shiyasa sukeso su yaudareni da nunamin kauna ayanxun"
Takallah hannunsa dake kan kafadarta yana riritata, cikin siririyar murya tace "Yaya kwana nawa yaragemin?"

Dasauri hankalin Hamza da Mama yadawo kanta,
Yanda ta jefo tambayar kamar saukar aradu yasa Mama cikin 'bacin rai tace
"Ushna baki da hankaline? Waya gayamaki ciwon yayi tsanani dahar zaki kawomin zancen mutuwa, ki kwantar da hankalinki zaki warke",
Langwabe kai tayi talumshe ido hawaye mai ra'da'di nabin gefen fuskarta murya dushu-dushu tace "amma Ni nasan mutuwa zanyi",
Tasaki hannunsa taja hannun Madina tashige daki tabarsu a parlour sunyi jungun-jungun.

Tana shiga Hamza yakallah Mama cikin jajantawa yace "Mama ina tsoro, itama Ushna,,,,"
Dasauri ta 'dagamai hannu takatseshi da fadin "Allah ke rayawa insha Allah zata sama sauki, muje inmata bayani kanmutafi",

Uhum kawai yace jiki asanyaye yabita,
Agefen madubi suka sameta tahada kai da gwuiwa tayi shiru Madina na gefenta.

Hamza ya'karasa dasauri yace "Ushna karki jama kanki damuwa",
Batace 'kalaba ta'dago kai takalleshi hawaye na surara gefen idonta,
Wani irin 'kuna takeji aranta domin yau tasheda sawun Giwa ta take na Ra'kumi,
Dalilin dayasa Yusuf yabaro Engila da dalilin dazaisa Hamza yafara bata kula amatsayinta na ma'kiyarsa lalle ba 'karamin abu bane,

Ganin tare da Mama yake tayi sauri tagoge hawayenta,
Mama tace "Ushna zonan magana zamui dake",
Rass Ushna taji mummunan faduwar gaba,
Suna zaune ta'dan matse hannunta ko zata samu karfin gwuiwan jin abunda ke tafe dasu,

Tarin tilin magungunan(medicines) da Hamza yaturo gabanta yasa tahangame baki,
Ta'dago kai atsorace tace "wannan fa?",
Mama dake kefenta ta'dan matso tace "Ushna ciwon zuciya ba karamin ciwo bane kema kinsani, danhaka dan Allah karkiyi wasa da maganinki kuma kishasu akan lokaci dan lafiyarki dana abunda ke cikinki",
Jin maganar Mama tayi yana ansakuwa akunnanta,
Tasake mamaimaitawa atsorace tace "abunda ke cikina?"
"Eh kwananmu biyu dake a asibiti bakya cikin hayyacinki,
Daga baya likita yagano kina dauke da juna biyu kinga dole kirage damuwa",
Kasa furta ko kalma tayi, tahau bin idanun kowannnan su dakallo hawaye nazarye afuskarta,
Take tadun'kule hannu tuncin karfinta tahau naushin mararta kamar zautacciya tana fadin "kafita, wallahi saika fita natsaneka, natsaneka",

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now