WASIYAR AURE😭❤️❤️
Mallakin; Najaatu Shehu Naira
Wattpad: Najaatu_NairaFKD PROD FANS WRITERS ((((51)))
Dasauri Mama ta'dago kai tace "Alhj karka yanke danyan hukunci" baibata amsaba yasakai yajuya zaifita tataso dasauri tabi bayansa, fitowan da zasui suka tsinci Hamza bakin 'kofa, jiki ba'kawari ya'dago kai yakallah Mama yace "dama jakarta tamance amota,"
"Toh" kawai Mama tace tabi bayan Alhj dayafita afusace,Ganin sun 'kule yashiga yasameta tana zuban hawaye, ahankali yazauna kusa da ita yakira sunanta cikin sanyin rai,
Bata 'dago kai takalleshiba sai kuka datake tana dukan Pillow,
Hakanan yatsinci kansa cikin tsananin yaga yarungumeta shikansa yarasa dalilin duk sanda zuciyarsa tatsinci Ushna kusa saita kasa bashi hadin kai, shin tausayin rayuwar Ushnan yake kokuwa tausayin shi kansa,
mamakin sanyin zuciyarsa adukkan lamarin Ushna,
Zaitashi tariko hannunsa tana hawaye tace "dan Allah karka tafi",
Kasa magana yayi dan kallon fararen kwayan idonta dake cike da kwallah,
Ahankali yasa yatsa yafara goge mata yace "ke bakyajin magana ko? Kinsan kwanannan akaimaki aiki amma bakya kiyaye sharuda, gaki da hawan jini ga uwa uban ciwon zuciyarki duk baki damuba baki da aiki sai kuka da rigima",
Tana hawaye tace "bakaji abunda Baba yaceba?"
Rasss yaji gabanshi yafadi ya'dan cize lebe yadake ya'kurama kwayar idonta ido yana kokarin tantance halin da take ciki, ganin tayi kass dakai yasa yace "toh ni banga wani abun kukaba tunda tunfarko su suka hadamu, nibanga abun kukaba tunda ke bakima sona gashi yanzun nima aure zanyi, ga ra'ayinki akan kishiya, kince bazaki zauna da mai mataba toh meye abun damuwa?",
Tana kuka tariko hannunsa bibbiyu tace "Yaya wlh sharrin shedanne, kuma aida kanasona",
"Nima aida kingujeni" yafada batare da yakallah fuskartaba yace "Ni zantafi yanzun gobe zandawo",
Yafita dasauri yabata waje,Baitsaya ko'inaba sai gida, yana shiga baikula kowaba yafada dakinsa baisake ko fitowaba sai washegari yafito ido jajir yayi kicibus da Precious akofar dakinsa,
Da dukkan alama awajan takwana,
Dasauri yagirgiza gai ganin tafarka farat tana tambaya "hey are u ok, kana lafiya?",
Yana hamma yace "bana hanaki wannan halinba, meyesa bakije kinyi barciba?" Tana kallon kwayar idonsa tace "kadawo jiya da gajiya inatama magana kayimin banza nasan fushi dani kake shiyasa natsaya nan dan inkatashi kan katafi aiki natsaya nabaka hakuri", kasa magana yayi dan mamakin hali irinna Precious sainoke wuya yayi yace "toh fine kije bakimin laifiba," zaitafi tarike hannunsa tace "maizanyi kasoni kamar yadda kakeson Ushna?" "Ina sontane?" Yatambaya yana kallon kwayar idonta,
Cikin 'dar tace "tunda tadawo kacanzamin kadaina kulani sannan kaima kullun kana cikin damuwa",
Ahankali ya lumshe ido yadanne xuciyarsa don gaba daya maganar nata ba dadi yakemai ba, jinshi yake agajiye, zatai magana ya'dago kai yace "Precious nataba gayamaki ina sonki?" Nandanan idanunta yacika da kwallah, kasa mgn tayi tana tsaye tana kallonshi yagyada kai yace "kwarai, amma yau zangaya maki kina burgeni", cikin tsananin farinciki tai washar da hakora tana murmushi hawaye yasauka kan kuncinta zata rungumeshi yaja da baya yace "a'a nagayamaki munan bama wannan saidai ko munyi aure",
Cike da mamaki tazaro ido tace "zaka aureni?" Rasss yaji maganar tabigi zuciyarsa, yatsaya kallon yadda take farinciki tare da rike hannu biyu abaki yace "eh banda matsalar haka amma bazan auri ahalil kitab ba, balaifi bane amma banso nasama matsalar addini agidana nangaba, sannan matsalar Ushna kibarni dashi, Ushna koba mu'amular aure tsakaninmu, Qanwatace kuma tsohuwar Matana sannan Qanwar tsohuwar Matana ga 'Ya'yantanan kingani dan haka tanada matsayi sosai aguna, dole damuwarta tazama nawa kingane ko?" Dasauri tagyada kai tabar wajen cike da fara'a,.Ajiyar zuciya yayi ya girgiza kai azahiri yafurta "toh meye nafarincikin?",
Yaci gaba da ma'amilonshi,
Makon sati dazaran yashirya zaije ganin Ushna saiyaji gabansa nafadi tare da fargaba aduk sanda yatuna zancen Alhj Shehu,
Wato abun bakaramin ki'dimame tunani yakeba sannan awani bangaren Precious kara gogewa take duk wani classes na koyan hausa da al'adun Hausawa tana shiga danganin taja hankalinsa, bata da'aiki sai jan lalle dayin kitso kanana da sa turare nau'i kala-kala dan ganin taja hankalinsa,.
Shikansa tun abun baitasiri awajansa har yafara yabawa sbd jajircewanta nason ganin lalle saita burgeshi, hakan najan hankalinsa,
![](https://img.wattpad.com/cover/227361078-288-k99320.jpg)
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...