Wasiyar Aure 13

610 182 1
                                    

Wasiyar Aure😭❤❤

By; Najaatu Naira

FKD Fans Writers 《《 13 》》

Ahankali Hamza yabude ido yana 'karema inda yake kallo,
Cikin 'yandabaru yasama guri yazauna, yakallah Dr Usain dake zaune agefenshi yazabga tagumi yace "haryanzun baka tafiba",
"Kafarka kenan" Dr Usain yafada yana ta'ba jikinsa yace "Masha Allah Fever din yasauka,"
Tsam Hamza yari'ke tsintsiyar hannunsa cikin 'dakushashshiyar murya yace "dan Allah Dr kayi hakuri katafi kaban guri dan Allah, inaso nakadaice",
Yanda Dr Usain yaga Hamza na godensa jikinsa yai la'asar yace "toh inna fita zankirama Kamal yazo yazauna dakai",
"A'a kakiramin Daddy ne pls",
Gudu-gudu Dr Usain nagyada kai yace "toh zanfadamai sannun narubutamai magungunan dayakamata kasha, daganan zanwuce".

*******
Lokaci daya Ushna ta tsinci kanta cike da zullumi hadi da fargaba tun bayan fitar Dr Ussain,
Maryam dake zaune agefenta tadafa kafadarta,
Afirgirce Ushna tajuyo, Maryam ta 'daga gira tace "lafiya Ushna mainene",
Bata bata amsaba takallar Wasikar dake hannunta ta mike takoma kan chestdrower tazauna,
Kamar mara gaskiya tabude takarda tana le'ke cikin zullumi tafara karantawa,
Assalamu'alaikum, Masoyiyata abar kaunata Ushna, nasan kinanan kinci kuka kinkoshi Allah sarki madadin kidungamin addu'ah, toh naji banson kukannan addu'arki gareni nake bukata,
Ina Munawwara ta da 'Dan Jaririna? Inafatan kinatare dasu gabadaya",
Shar Ushna tarufe takardar tana hahawaye tare da waiyayen inda zataga Madina, ganin hawaye nasintri kan fuskar Ushna, Maryam tataso dasauri tace "Ushna mainene wai dan Allah, kifadamin maike damunki?" Dasauri tasa hannu tagoge hawayen cikin dakushashshiyar murya tace "Madina nake nema",
"wajan Babanta take wuni",
Maryam tafada atakaice ,
Gyada kai tayi ta lumshe ido taci gaba da karanta wasikar,
"'Yar Qanwata dan Allah kirainanmun 'Ya'yana, karki bari suyi maraicin Uwa kinji Ushna nasan zaki iya ko?" Kamar tana gabanta tahau gyada kai azahiri tafurta "Eh Anty Insha Allah".
"Sannan Ushna kiyafemin alkawarin dana daukarmiki kan tsakaninki da Fidyan, Allah baibani ikon cikawaba inafatan zaki yafemin hadi da'yar Alfarma dazan ro'ke'ki, Ushna kima ma'aikin Allah Ushna ki Auri Hamza Mijina kurungumi maraicin 'Ya'Yana dan Allah, nasan zakice nafiya sonkaina dayawa, amma kiyi hakuri 'Yar kanwata bayan 'ya'yana danake ro'kan ki raina nasan duk macen datasama namiji kamar Hamza tayi babban rabo, inamiki kwadayin farinciki mai daurewa Ushna inafata zakiji kaina ki karbi bukatata gunki Masoyiyata, daga karshe Ushna zanmiki nasiha kirage rawankai kima iyayenmu biyayye, yanzun bananan bare nakare laifinki wajan Mama kuma ganauyin 'Ya'ya akanki kibasu Tarbiya Allah baku ikon daukan nauyin dana rataya awuyar ke da Hamza bisalam"
Gwalalo manyan idonta tayi da nandanan suka kada sukai jajir, dasauri tasa hannu tarufe baki da tafukan hannunta gudun karta 'burma iwu har wani yasan halinda take ciki,
Kuka take tuncin karfinta Maryam nararrashinta tana tambayar dalili,
Ganin Ushna taki sauraronta cikin rarrashi dajan hankali tace "haba Ushna kinsan illar kuka ga mamaci babu amfanu, kiyi hakuri kidaina kukannan addu'ah take bu'kata Ushna kinji kiyi hakuri"
Ganin babu sauki hakuri take bata kamar tana 'kara zigata tatashi a fusace tace "barinje inkira Mama tunda kinki hakura"
Maryam nafita Ushna tatashi dasauri tana girgiza kai ta cutsa Wasikar bayan wardrobe dinta,
Tasa tafukan hannunta tagoge hawaye tasaki ajiyar zuciya,
Azahiri tafurta "kiyi hakuri Anty gaskiya wannan bamai yuhwa bane, bazan iyamaki irin wannan alfarmarba",
Takoma kangado tana ajiyar zuciya daidai 'Dan Jaririn Rayhana dake kwance yafarka ta janyoshi tarungume,.

Mama nagaba Maryam nabinta abaya suka shigo, Ganinta sukai hankali kwance tanaba 'Dan Jaririn madara,
Bata 'dago kai takallesuba saida Mama ta'kari nazarinta tsaye kan tace "Ushna inafata kinrage yawan koke-koken nanko?"
Ahankali ta'dago kai suka hada ido kan tace "eh Mama", tamaida hankalinta kan Feeder,
Mama takallah Maryam datai sarairai tasaki ajiyar zuciya tace "toh Alhamdulillah",
Tafice,

Cigaba da hidimominta Ushna tayi tsja bakinta tai shiru ko Maryam bata 'kin'kitsa mata Wasiyar dake dauke a Wasikar Rayhana ba.
************

Karfe tara nadare,
Ranar addu'an bakwai, Ushna nazaune da Jariri ahannunta, Hamza, Mama, Alhaji Bello da Alhaji Shehu azaune cikin katafaren Parlour Margayya Rayhana,

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now