Wasiyar Aure 12

634 133 0
                                    

Wasiyar Aure❤😭😭

By; Najaatu Naira

FKD Fans Writers 《《 12 》》

Tunda suka dawo kai margayya Rayhana makwancinta, Hamza yakoma kamar zautacce, bin mutane kawai yake da ido ko gaisuwa bai'iya amsawa,
Duk inda yacire 'kafa nan Madina zatasa, yana rike da hannunta kusa dashi baibari tamotsa konan dacan ,

Lamarin Hamza basauki kullun 'kara cigaba yake tun Daddy nabashi baki harya gaji ganin wani lokaci shikadai yaita sambatu yana kiran sunan Rayhana yana girgiza kai yana hawaye Madina dake gefenshi nasharemai da tafukan hannunta.

☆☆☆☆☆☆☆☆
Karfe biyar Ushna tatashi yin sallah subhi, nafila tayi tai sallah tareda alqunut tayi azzikar sosai dan ita dakanta tana iya jinta badaidaiba, jitake kamar ana kwankwasa kanta da guduma,
Cikin kwana uku ta rame takwanjale tana jinkanta kamar za'a hure tafadi,
Tana idar dasallah tananna'de sallaya tatashi tahado madarar Jariri takada tasa a feeder sa tafito,
Dakin Mama tawuce kaitsaye, cikin azzama tajiyo kukansa kanta 'karasa,
Hakan yasa ta'karasa dakin da gudu hartana tuntu'be da Door stairs din dakin Mama,
Ahannun Mama tasameshi tana jijjigashi,
Ushna tamiko hannu cikin dakushashshiyar muryarta data toshe dan kuka tace "Mama kawoshi",
Mama tagirgiza kai bata 'dago kai takalletaba tace "tsaya barin bashi ruwan dumi"
Dakyar yasha yana rigima Ushna tayi sauri ta karbeshi hadi da jijjigashi tana fadin ya'isa ya'isa tasamai feeder madarar abaki,

Karfe shabiyun rana Daddy yasama Hamza kwace atakure jikin gado yahau lallabashi yafito amsan gaisuwa,
Dakyar yatashi yana tsaye jiwa ta'debeshi yafada saman gado,
ganin haka Daddy ya'dagoshi, Hamza yarataua hannu saman kafadar Daddy yataimaka mai yafito tare da Madina ahannunsa,

Tundaga cikin gidan yake karban gaisuwa har zuwa wajan zaman makoki gefensu Baba kusa da parking Lodge dinsa,
Agefe yasama guri yazauna ba imm ba um-um sai idanu da yake zarewa yana kallon mutane 'kiruuuu,
Basai antambayaba kana ganin Hamza kasan akaima mutuwa,
Ganin shigowar Dr Usain gaisuwa gaban Hamza ya yanke yafadi nandanan yatsinci kanshi cikin fargaba dabugun zuciya mara musaltuwa,
Lokaci daya zuciyarsa tafaramai aiyane aiyane dafatan dama Dr Usain yacemai bata mutuba, langwabe kai yayi yalumshe idonsa da yanami hawaye sama ko'kasa sun'kafe yagirgiza kai shikadai aransa yace "ina wanda yamutu baya dawowa",
Azahiri yafurta Rayhanata tayi dogon zango, tatafi tabarni,
Bai'ankaraba yaji kwallah dayanema yarasa zirrr tanabin gefen fuskansa, dasauri yasa bayan hannu yagoge hawayen yana kallon Dr Usain yagama gaishe-gashensa baice uffan ba, sai danasanin fitowa dayayi,

Saida Dr Usain yashiga harcikin gida yaima su Mama gaisuwa kanya fito yazo gefen Hamza yazauna, cikin nutsuwa yakalleshi yaimai gaisuwa 'kasa 'kasa yakasa bare su hada ido,
Dr Usain ya sunkui dakai yatsinci kansa dafargaban haduwa da Hamza sanin ahannunsa matarsa tamutu,
A'aikin likitancin babu abunda Dr Ussain yatsana kamar kai sa'kon mutuwa, 'yan'uwan Mamatan basu ta'ba mance fuskanka barin Hamza dayake abokinsa.
Ufan Hamza bai'iya cewa sai kukan zuci hadi da goge hawaye tare da 'kan'kame hannun Madina da dayan hannunsa kamar za'a kwacemai ita,,

Dr Usain zaitafi yadafa kafadarsa yana magana kamar ra'da yace "Hamza tashi muje inason magana dakai"
Nandanan idon Hamza yai narai-narai jiki nakyarma yace "Dr wlh jikina rawa yake, wuni nake adaki yanzuma nafito nadansha iskane tunda jama'a sunragu muyi maganar anan"
Ganin dayaima Hamza agalabaice yasa baijaba ya jinjina kai yace "toh ba damuwa dama Matarka ne tabarma wasika(letter) kafin ta rasu, tabar letter biyu, daya na Ushna Qanwarta daya naka gashi",
Yakallah kwayar idon Hamza dakemai kallo kamar ba'kon duniyar wata yace "saida ta jaddadamin WASIYA ce, natabbatar nabaka hannu da hannu, ganin halin daka shiga ranan rasuwarta yasa na'adana banbakaba saiyau",
Jiki narawa Hamza yasa hannu ya karba, Allah Allah yake yaga maike ciki yasa hannu yayage envelop din yabude 'yar farar takadda A4 da zanen hannunta na rubutu (handwriting) 'buru'buru akai,
Take yasaki gawurtaccen ajiyar zuciya,
Yabude yafara karantawa,
Baifi 'yan mintina dafara karantawaba tsoro yabaiyana 'karara da zullumi afuskarshi;,

Sululu daga zaune ya 'bingire yafa'di"
Gaba daya mutan wajan hankali yadawo kansa dagudu Daddy ya 'karaso dasauri yana kwala kiran sunansa "Hamza Hamza",. Shiru ba'amsa,
Ganin yana numfashi sama-sama Dr Usain yasa hannu akan kirjinsa,
Zuciyarsa Bugu take kamar zata fasa kirjin tafito,
Jin haka Dr Usain agaggauce yace "kumatsa kubashi waje yasama iska,
Daddy yakallah Dr Usain yace "lafiya? Dr maike damunshi, maikai mishi?"
Dr Usaini yasa hannu 'kasa daidai inda wasi'kar take ya dauko karkashin 'kafar Hamza yamikama Daddy yace "gashi Matarsa tace inbashi",
Daddy yasa hannu yakarba wasikar jiki asanyaye, yafara karantatawa kamar haka "

"Assalamu Alaikum My Diamond,
Nasan idan takardannan ta'isa gareka mai afkuwa ta afku,
Allah yadau kwanana nabar duniya, nabar rayuwa Dakai da 'Yata Munauwara tare da abun kaunata Ushna nabar Mama da Baba da sauran dangi.
Uhmm idankuwa hakane nasan kana cikin ba'kinciki mara musaltuwa amma Diamond dan Allah hakan karyasa kaji kayi hannun riga da farin ciki, karka manta kamin alkawari zaka kula da amanata Munawwara tare da 'Dan Jaririnmu da zaiyi maraicin Mahaifiya saidai bata Uwa ba,
Duk duniya ba abunda nafiso irin Dangina, Iyalina dakuma 'Ya'Yana, Hamza dan Allah ka tabbatar 'Ya'yana sun rayu ahannun Ushna domin nasan babu wacce zata iyarikesu susama tarbiya da kauna tamancesu kalmar maraici sai Ita,
Nasan zaka girgiza kai kace zaka rainaisu da kanka toh Diamond banyardaba banso kokadan suyi rashin Uwa,
Kuma nasan tunda nake dakai Hamza bantaba ro'kanka alfarma kayiminba indai akan Ushna ne, amma yaudai so daya bayan raina albarkacin soyayyar da kakemin,
Dan Allah ka Auri Ushna kuzauna ku rungumi maraicin dana barku ciki, ku rikemin 'ya'yana kusamarma kanku farinciki, farin ciki maidaurewa,
Diamond karikemin Ushna Amana dan Allah Hamza wannan shine barar Matarka gareka,
Ka auri 'Yar'uwata Ushna ku rungumi kaddarar rayuwa hannu bibbiyu, Allahsa Mijina abun alfaharina zai'iya biyamin wannan 'yar bu'katar tawa, nagode............"
Zufar dake shararoma Alhj Bello yasa yatsa yasharce, gumi kawai yake hadawa dukda iskan dake wajan, yakallah Kamal 'Dansa dayasameshi da zancen auran Ushna kwana biyu kafin rasuwar Rayhana, gakuma margayya Raynahana datata Wasiyar,
Alhj Bello yagirgiza kai hadi da kallon inda Hamza yake kwance cikin confuse yace "toh maiya ta'bashi haka, ko Kamal yasanar dashi soyayyarsa da Ushna ne?"
Shikadai yake jefama kanshi tambayoyin dayakasa samar da amsansu yana kallon Hamza dake kwance ana taimakamai da Artificial breathe baiko motsi yana kallon Wasikar yana girgiza kai.

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now