Wasiyar Aure😭❤️❤️
By: Najaatu Shehu Naira
Watpadd: Najaatu_NairaFKD Fans Writers 《《29》》
Washe gari da sassafe yafito yin breakfast yaci karo da Ushna gaban Fridge tatasa Nutella agaba tana ci tana lumshe ido,
Chak yatsaya yana 'karemata kallo cikin nishadi yana murmusawa ganin yadda take ci da hadama kamar wani zai 'kwace mata.Harzai wuce ganin bata lura dashiba yace "Madam lafiya?",
Dasauri ta'boye robar nutella dake hannunta ta tsuramai ido.
Aboye yai danmurmushi yamazaye yace "lafiya maikikeyi anan",.
Yatsina fuska tayi tace "Akwai dokar data hana tsayuwa anan ne?",
Dasauri ya girgiza kai yace "a'a, amma tunda kintashi dawuri maizai hana muyi breakfast tare?",
Wani irin kalloh taimai zatai musu ya'daga yatsarsa manuniyarsa yana karkadawa yace "we're now a partners, yanzun ina rayuwane danganin nahadaki da masoyinki, babu tsana babu kyara ko tsangwama tsakaninmu sabida lafiyarki,",
Yanda yake maganar cikin walwala taji tsananin tsanar zama dashi na'kara mata katutu arai, ta'dan yatsina fuska tace "nifa inza'a shekara dubu bazan ta'ba sabawa dakaiba",
Murmushi yayi awasan dare yace "ashe kuwa kema aikin da kikaban zai dade bai kammalu ba",
Dasauri taware dara-daran manyan idanunta tana kallonsa yano'ke wuya yace "yaba kyauta tukuici",
Kasa magana tayi dan takaici,
Tabuga 'kafa tabar gurin.Tana shiga yashiga kitchen yabude wancan yaja wance yafito da kayan kumallo,
Lafiyaryan chips and plantain yahada masu tare da egg sauce dayaji kayan masarufi na zamani.
Baitsaya nanba ya'dauko kayan 'kamshi yahada lipton harda ganyen na'ana.
Yakammala tsab yajerasu kan Table.Dakin Madina yashiga yasameta tayi 'dai'dai da 'kafa tana barci ya cicci'beta yadireta a bathroom yayi mata brush yafito da'ita yin kummalo.
*****
Ushna tafito zata kitchen 'kamshin abincinsa yabigi hancinta, lokaci daya muyaunta ya tsinke dan kwadayi irinna masu ciki,
Ta'dan saci kallonsa zasu hada ido tayi saurin kauda kai,
Takallah Madina dake cin abinci tace "Sweetheart inkingama kisa Uwani tashiryaki zamu gidan Mama",
"Toh" kawai tace batare data kalletaba hankalinta nakan abinci.Duk yadda taso tajanye ido kan abincin takoma 'daki takasa,
Sarai Hamza yalura da yanayinta ya'dago kai yanacin plantain din tayadda zaija hankalinta yace "zo kizauna musamman ke naima breakfast dinnan amma bansan tayadda zankiraki ba",
Duk yadda ranta yabiya hakannan ta zumbura baki tace "na'koshi" badan ranta yasoba,
Tai narai-narai da ido cike da fuskar tausayi zata juya yataso dasauri yarike kafadarta yaturata kiiii harkan Dinning table din yace "inkinci inbai makiba saina dafa maki wani",Zatai magana yadauko plantain da chip yatura mata baki,
Babu yadda ta'iya yanda taji harkunnanta na ka'dawa talumshe ido ta tacinye.
Ba baka sai kunne tatasa abincin gaba ta lamushesu tsab,Jin ta'koshi tajanyo kayan lipton dindake gabanta tana tunanin sha tana tunanin bari ya karba flask din hannunta yazuba mata a kofi yace "gashi kigwada sha",
Nandanan kamshin kayan yajin dayasa yaturara hancinta takarba batare data musaba takafa kai.Ajiyar zuciya tasaki azahiri tafurta "Alhamdulillah"
Madina takalleta cikin zumudi tace "My Mommy yayi dadi ko?",
Ta'be baki tayi cikin tsiwa tace "innnna Sweetheart wannan ai bashi ake kira dadiba, gobe zanmiki abinci anan zakisan banbancin jagwalgwalo da girki",
Cikin zolaya Hamza yace "Amma Ushna banta'ba ganin kinyi girkiba inba ko indomie ba"
"Zaka gani", ta fa'da cikin tsiwa takoma daki daidai Inna Saratu tagama shirya Fahad,
Ta karbeshi tabashi madara daga bisani tashige wanka..Tana zaune gaban madubi harzata tashi wata zuciyar taraya mata gwanma kiyi kwalliya wata 'kil Allah yasa kihadu da Fidyan ahanya.
Take zuciyarta tayi 'kal ta lumshe ido tace "Allah Amin",
Ta 'dauki kajol tazana a dara-daran idanunta dayai furu-furu kamar tatashi ciwo,
Ta barbada powder tare da janbaki tagoga kan 'dan 'karamin bakinta,
![](https://img.wattpad.com/cover/227361078-288-k99320.jpg)
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomansaAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...