Wasiyar Aure😭❤️❤️
By; Najaatu naira
FKD Fans Writers 《《22》》
Inna Saratune tsaye akansu tana kwada sallama yajuya dasauri, akunyace cikin ladabi tace "Lafiya Alhaji? Dama naji ana doka sallamah ne tundazu awaje"
Yana kakkebe jiki kamar wanda yai aikin 'kasa yace "ah inazuwa barin duba", yabar wajan yana'dan kameme Ushna nabinsa da ido.Dr Usain yagani tsaye yana jijjiga jaka yace "ah yazaka tsaya tsaye baka shigoba, shigo mana",
Suna tafe cikin hanzari Dr Usain yace "ai naita kiran wayarka ina ka'aje?",
Baibi takan wayarba yanuna inda yabar Ushna dayatsa zaice "Gata,,,,,," ganin bakowa awajan yace "ah toh ina taje",
Take zuciyarsa tarayamai kota gudu sbd abunda yafaru?
Kut yafurta azahiri yanufa 'dakinta da gudu yabude 'kofa bata ciki. Asukwane yashige, zai kwa'da mata kira yagata fito daga bayi,
Ja dabaya yayi yasauke ajiyar zuciya yace "likita yazo zaiduba ki",
Wani irin kallo taimai natuhuma kan tamurguda baki tace "kanama Allah karka sakemin magana, natsani naganka wlh natsaneka",
Cikin sanyin rai yace "Ushna kinsan kwatankwacin tsanar da kikemin shi nake maki danhaka baidameniba, kizo muje likita yaduba lafiyar jikinki zaifimiki"
"Bazaniba, kafitarmin daga daki" tafada cikin tsawa hawaye nabin kuncinta,
No'ke wuya yayi yace "fine, saidai kinsan nangida nane, inada ikon shiga duk inda nakeso, amma zanfita kekika sani lafiyarkice, sa'annan gobe kishirya dawuri karfe takwas nasafe jirginmu zaitashi, nabarki lafiya",
Baijira tacewartaba yaja 'kofa yabar 'dakin,
Dr Usain nazaune yana zaman jiran Ushna, Hamza yadawo rai 'bace yace "tace bazata fitoba akyaleta",
Cikin rashin fahimta Dr Usain yace "bangane baxata fitoba, tana nufin bazatazo aduba lafiyarta ba?",
Hamza ya'daga gira yace "Eh rabu da'ita, kayi hakuri natasoka akarin banza",
Dr Usain yagirgiza kai yace "toh bakomai ai naji dadin ganin kirarka awayana wlh, nagode"
Sarai Hamza yafahimci inda Dr Usain ya dosa, Allah mai'ko shikanshi baitaba tsanmanin zai 'kara ido hudu da Fuskar Dr Usain ba sai yau da Allah yanufa,Yaimai rakiya harbakin mota, zasu rabu Dr Usain yaga damuwa tabayyana 'karara a fuskar Hamza,
Yadafa kafa'darsa cikin rarrashi yace "Abokina kamar akwai abunda kedamunka ko?"
Harzaice babu wata zuciyar tace "baridai nafada ko Allah zaisa da mafita ya taimakamin",
Yakallah Dr Usain cikin nutsuwa yace "Usaini wlh inacikin matsananci bu'kata ne, kaidai kasan yadda Allah yayini da matsanancin sha'awa, toh damuwa da rashin Matata yasa bantaba tunanin bu'kata zatazomin nankusa ba, gaskiya inacikin damuwa"
Baki bude Dr Usain ke kallonshi, yana mamakin furucin dake fita daga bakin Hamza,
Ganin irin kallon da Dr Usaini kemai yasa Hamza ya gyada kai yace "nasan zakai mamaki domin ni kaina nayi tunanin bayan rasuwar Rayhana bazan 'kara sha'awaba toh,,,,,,,,",
Dasauri Dr Usain yakatseshi yace "bahaka nake nufiba Hamza, dama kai namijine kuma kanada lafiya dole ko komai najikinka zaidaina aiki indai dasaurar lafiyar mazan takanka kaji matsanancin sha'awa, amma nibanga abun damuwaba tunda kanada mata ga Ushna nan mace har mace",
Guntun tsaki Hamza yayi nandanan ya'bata rai yace "wannan shashashan Yarinyar, kasanni bansan mace mai feleke kumama dama ni jinina baihadu da Yarinyar ba, atakaice dai ni bani kallonta amatsayin mata bare har innemi hakkina gunta, danhaka idan da'akwai maganin da zakabani kafindai Allah yahadani da 'ya mace inyi aure, ayanzun ina bu'katar taimakoka, kataimaka min",
Dr Usain nakallonsa cikin rashin amincewa ya girgiza kai yace "a'a maganin gaskiya cibiyar lafiya tayi hani dashansa domin daga karshe yana kashe sperm da kuma rage garkuwan Mazantakan 'Da namiji, dan cikin illolinshi yana hana haihuwa da kashe kwayoyin sha'awa",
Hamza nagyada kai cikin sambarka yace "Eh bani inaso, hakanma yafimin",
Cike da mamaki Dr Usain yazaro ido waje yana 'karema Hamza kallo, ganin dagaske yake yace "wlh Hamza bazan bakaba, sam bazai yuhba, nasan yanzun baka cikin haiyacinka amma dazaran komai yadawo daidai zaka gane ba'karamin kuskure kaso ka aikataba, ni zantafi yanzun dare yayi kuma ina fatan bazakaje wajan wani likitanba da wannan bu'katar, saida safe",
Baijira amsarsaba yawuce yabar Hamza tsaye cikin ba'kin ciki da rashin madafa.
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...