Wasiyar Aure 09

632 129 0
                                    

Wasiyar Aure😭❤❤
      
By: Najaatu Naira
                       
FKD Fans Writers 《《 09 》》

Tsayin daren Ushna na waya da Fidyan, banda lallashi babu abunda yake amma taki saurararsa,
Ganin yagaza fahimtar inda tadosa tafito fili tagayamai gaskiya 'karara zata bishi.
Shiru yabiyo baya na'dan mintina yana nazari akai,
Dukda yanaso saiyaji zuciyarsa taki amininta saima kwabarsa akan shawararta Ushna,
Chan yatsagaita shirun jin tana mita yace "Mine ni tsoro nakeji wlh dama kinga Mama daga gani bata sona karnaima laifi iyayenki laifi nangaba suhanani aurenki,
Kamar yana gabanta ta tazumbura baki tace "Ni wlh saidai ko kafasa tafiyarnan kokuma nabika daga baya mabasu hakuri, kasan inasonka koma maizaifaru saidai yafaru amma gaskiya Fid banso katafi kabarni anan kafi kowa sanin ba'akaunata,",
Yadda take maganar sallah-sallah kamar badaga bakinta yake fitaba yasa ya lumshe ido yana sauraranta,
Komai na Ushna birgeshi yake shagwaba, rigima hadi da matukar Son datake nunamai,
Dogon ajiyar zuciya yayi wanda tana iya jiyo numfashinsa yace "toh indai hakane gobe karki hada wani kaya mutafi yaso saikiyi siyayya inmunje chan, kiyi komai cikin dabara kamar zaki rakani saimu tafi, kinji kidaina daga hankalinki kina koke-koke banaso",
Ba'karamin dadi tajiba murna fal ciki, zuciyarta tayi fari'kal, hankalinta yakwanta tasaki ajiyar zuciya, duk wani damuwa takau, tadan gyara kwanciya cikin siririyar murya maidadin sauraro tace "toh My Fid Allah kaimu" taimai sallah takashe wayar tarungume 'kam akirjinta cikin murna har barawan barci ya sureta,

************

Washegari dasafe Ushna tashirya tsab,
Fuskanta tayi fayau babu wani kwalliya abunka da farin fata taji gyara sai kyalli take,
Madina tazo da gudu tafada jikinta tace "My Mummy",
Tayi 'dan murmushi ta rintse ido, idan dakwai abun da zatai kewa a Nigeria daga Madina sa Mamanta(Rayhana),
Burinta daya duniya shine tarayu da Anty Rayhana, Madina dakuma Fidyan amatsayin Mijinta,
Ta dauki Madina ta rungume kam ta 'karaso
Dining takallah Rayhana dakekan dining Table suna breakfast tace "Anty kinsan nagayamaki zankoma makaranta(school) zanje gida yanzun nahada kayana",
Gaban Rayhana yafadi tadan dake ta saci kallon Hamza suka hada ido, tama rasa yadda zata bulloma lamarin murya narawa tace "toh tam  indai hakane toh aisa Hamza yakaiki gida ya'ajeki ko",
Shiru Ushna tayi irin namarasa gaskiya tana 'kib'kibta ido tace "Aunty Fidyan fa zai ajiyeni agida yamazo yana waje yana jirana",
"Ke ba'inda zaki kikoma daki kikwanta", Hamza yafada ami'ke yana mata nuni dayatsa.
Hakan baifirgita Ushna ba kokadan, ta karkada ido tace "Malam ni badakai nayi maganata ba" tamurguda baki,
Baiji haushiba domin indasabo yafara sabo da rashin kunyar Ushna, yasaki ajiyar zuciya dansamun nutsuwa yakallah Rayhana yace "Beauty zanshiga ciki amma kisani banyarda Ushna tasa 'kafa tabar gidannan ba"
Yasakai yafita fuuuu kamar kububuwa yabasu waje,
Jikin Rayhana yayi sanyi, kallo daya zakamata kasan hankalinta atashe yake, dakyar tatashi tarike hannun Ushna cikin janhankali bakace maganar daga bakinta yake fitaba tace "Masoyiyata mekikeso kimaida rayuwarki iye, for God Sake maikika naima kikarasa dazakibi namiji 'kasar turai, balaifi bane idanshi yabiyoki amma ke kibishi Ushna laifine, dan Allah kimin wannan alfarman dan Allah naro'ke'ki da Allah karki bishi",
Mamaki ya kashe Ushna dake tsaye, wani irin kallo takema Rayhana kamar ba'kuwar duniyar wata (alien), tarasa ta'ina tasan mgnr tafiyarta, takuma kasa tambayarta,
Rayhana takatse tunanin dafadin "ranar da Fidyan yazo gayamin bakida lafiya yagayamin Babanshi ba lafiya zaikoma, abunda nakeso dake shine kiyi hakuri yaje, yaso saiya dawo da wuri kinji?",
Babu yadda Ushna ta'iya kamar zatayi kuka tace "toh Anty, zanrakashi kawai indawo",
"Toh nagode saikin dawo" Rayhana tace tana shafan bayanta.
Harta tafi takirata takallah fuskarta datayi rolling da 'karamin gyale tace "kinyi kyau Masoyiyata". Ta'danyi ya'ke tafice.
Ushna nafita takira Maryam Qawarta awaya tace "kitsaya a kofar gida zan biyo nadaukeki",
Bamusu Maryam tace "toh saikinzo dama nayi kwalliya narasa wajan zuwa",
Tace "toh" tayanke wayar tashige motar Fidyan tana ya'ke gudun karya gane halin datake ciki.
Tana shiga yaja mota,
Yajuyo ahankali yakalleta yace "maike damunki?",
Shiru tayi takasa magana sanin babu wani salo nata da Fidyan baisaniba,
Ta'dago kai idanuwa narai-narai tace "Fid Anty Rayhana tasan zanbika kuma tahanani",
Jiyayi kamar tasaukemai dutse kan zuciya,
Yakasa 'boye damuwarsa tunyana tuki haryagaji ya parker motar,
Tajuyo takalleshi sukayi ido hudu tace "am sorry", ta fashe dakuka,
'Kala baiceba yajanyota yasan kanta agefen kafadarsa yana maida ajiyar zuciya yana tapping bayanta da tafin hannunsa,
Sunfi munti biyar ahaka kanya dagota yasunbaci (kissing) saman goshinta yace "karki damu Mine, duk inda zanje kina raina kuma dazaran nagama zandawo gareki insha Allah",
Cikin hawaye tace "toh badamuwa nagode"
Yasaketa yafara tuki jiki asanyaye suna tafiya sunajin wakar Umar m Sharrif Sai Wata Rana,
Babu maicewa wani uffan acikinsu hannunsa nacikin nata yana wasa da yatsun idonshi nakan titi,
Suna isa Airport lokaci ya'kure dasauri sauri yace "idan munsauka Abuja zankiraki tunda sai karfe hudu flight dinmu zaitashi"
Kai kawai ta gyadamai dan kalma daya zata furta tafashe maida wani kukan,
Shima baimatsa saitayi maganaba yazare Naira Credit Card dinsa daga aljihu tare da Key din gidansa yace "gashi koda zaki bu'kaci kudi, gakuma Key dingida nan, motarnan nabarmaki kimin addu'ah kuma dan Allah kirikemin amana Ushna",
yanda yaimaganar muryarshi na sartsewa yasa tayi sauri ta rungumeshi tana hawaye tace
"Naji zanrikema amana Fid nima karikemin amana Allah dawomin dakai lfy, nagode"
Cikin kuka tayi maganar,
Ya'dagota yasa tafin hannunsa yahau sharemata hawaye, ya saketa yagoge nataccen hawayen dake gangaro mar gefen fuskarsa da handkie,
Yajanyo Jakarsa dake Sit din baya yatafi,
Baiko juyoba sanin yana juyowa zaiganta tana hawaye abunda kodawasa baya kaunar gani,
Kyam yaji anrungumeshi tabaya cikin kuka tace "dan Allah Fid karka dade kaji dan Allah",
Ahankali yajanyota gabanshi yana kallan kwayar idonta dasukai luhu-luhu yagoge mata hawaye yarungumeta cikin nutsuwa yace "insha Allah kikulanmin dakanki"
Ya sunbaci goshinta, ya wuce,
Gudu-gudu yagama duk wani process kan yashiga jirgi anagab da tashi minti goma yarage,....

Saida taga tashin jirgin kanta bargurin zuciyarta naturnu'ku'ki kamar zata fashe, gudu take saman titi kamar zata tashi sama,

Bata tsaya ko'inaba sai gidansu Maryam,
Abakin Gate din gidan tatarar da'ita tacika tayi makil da haushi,
Kala bataceba tayi Parking Maryam tashige,
Saida tazauna kanta juyo cikin fushi tace "mara mutunci tundazu nake tsaye inazaman jiranki",
"Kiyi hakuri" Ushna tajuyo tace tatada motar,
Yanda idonta yayi jaji yasa Maryam tasan balafiya saikuma bataji dadin hargowan dataimata ba,
Cikin sanyin rai tace "Ushna lafiya maike damunki",
Idonta nakan titi tace "Fid yakoma yau",
Kai kawai Maryam tagirgiza tace "Allah sarki kiyi hakuri aizai dawo",
Uhmm kawai Ushna tace,
Daidai isarsu gidan Rayhana,
Suka sauko Hamza natsaye yana jiranta yace "ke daga ina kike, bana hanaki fitaba",
Ko kallo bai'ishetaba bare tankashi sai Maryam data dur'kusa har 'kasa tagaisheshi ya amsa agaggace, yabi Ushna ciki dasauri yana zazzaga masifa,
Gaba daya sukayi Parlour tana fadin "idan kai Ubanane aisaika hanani fita",
Yadago zai shararamata mari sukaji ihun Madina tana kiran "Ummi Ummi",
Lokaci daya suka kallah dakin Rayhana suka rankaya aguje,

A'kasa suka tadda'ita jini nabin gefen 'kafarta tana salati tana cije le'be,
Dasauri Hamza ya'karasa gabanta yadur'kusa yace "Lafiya Beauty, yabaki kirani ba?",
Jiki narawa Ushna tace "Anty lafiya maike damunki"
Dakyar Rayhana tace "kabar wayarka agida kekuma inata kira baki daukaba, kudainamin tambayoyinna kukaini asibiti na'kudane",
Cikin hanzari Hamza yatashi ya cicci'bota yakallah Ushna data daburce banda hawaye ba abunda take yace "Muje asibiti Ushna jeki tada mota barinfito da'ita",
Asukwane tafito Maryam na Parlour tace "lafiya Ushna mainene?"
Bata sauraretaba tafice dasauri tajanyo mota hadi da reverse daidai kofar shiga ta ajiye",

Sunfito Hamza yakallah Maryam yace "dan Allah kikula dagida ga Madina nan kiri'keta", kai kawai tagyada tare da rike hannun Madina nafincikewa,
Hamza ya shinfidar da'ita sit din baya,
Yashiga nagaba Ushna taja,
Harsunkai bakin gate tahango Madina tafinciko tarugo aguje.
Chak taja burki tatsaya ta bude kofar ta dauketa tamikama Hamza.
Zaiyi fada yaji Rayhana nafadin "dan Allah kutawomin da Madina, Diamond ina Madina?,"
Ushna datadau hanya tana sharara gudu tace "Gatanan Anty karki damu",
Murya narawa Hamza yace "eh gatanan karki damu, sannu insha Allah lafiya zaki sauka Beauty",.

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now