WASIYAR AURE😭❤️❤️
By: Najaatu Shehu Naira
Wattpad: Najaatu_nairaFKD PRODUCTION FANS WRITERS
《《31》》Marubuciyar;
KAINE RAYUWATA
SOYAYYATA DA MAJNUN
MASARAUTA
WASIYAR AUREIrin sauyin da Hamza yagani gun Ushna yasa haryaji karfin gwuiwar fita Office,
Duk wani damuwarta na zama da Hamza ta tattarashi ta ajiye gefe,
Tana cike da wutar daukar fansa,
Abu daya ketsinka mata jiki yadda Madina taja baya da'ita, duk yadda taso taja Yarinyar jiki ta'ki,
Hakan yasa gaba daya jikinta yai sanyi da tunanin idan Madina namata kallo irin wannan toh wani irin kallo duniya kemata kenan?,Tana zaune a parlour ta tsunduma cikin tunani taji anshafa fuskarta da lallausan tafin hannu, batai mamakiba domin irin wannan 'dabi'ar ta Hamza tafara sabawa dashi,
Ta lumshe zara-zaran gashin idonta ahankali tabude tace "kadawo?" Agajiye yazauna gefenta yace "kinanan kinata tunani ko?",
Dasauri ta girgiza kai tana ya'ke tace "a'a naji kamar inajin barcine",
Gyada kai yayi yakira sunanta "Ushna" tajuyo batare data amsaba yace "Maganar Madina karki damu akanta, Yarinyace kuma nasan tana matukar 'kaunarki zata fahimta nangaba"
Kasa dauke idonta tayi akansa, cikin siririyar murya tace "bansan taya zansakama irin 'ko'karin da kake akainaba, wlh bani da bakin da zangodema"
"Kinaso ki sakaminne?"
Ta gyada kai
Yayi murmushi yace "toh kikasance cikin farin ciki",
Da mamaki ta zare dara-daran idonta hadi da 'daga gira tace "aidama zanyi wannan kodan lafiyata",
"Toh ki dafamin abinci, yunwa nakeji",
Murmushi tayi tace "wannan kadai kakeso?",
Yana kallon cikin kwayar idonta ya gyada kai yace "eh, zansamu?"
"Yanzun kuwa?" Tamike dasauri tatafi Kitchen,
Yabita da ido yana mamakin shagaltuwar dayake akwanakinnan inyana tare da ita,
Wani irin shiga ransa Yarinyar take tana 'kara kwarjini da bashi sha'awa akoda yaushe inya sauke idanunsa akanta,
Nantake ya hadiye maitarsa tare da sakin ajiyar zuciya ya kishingi'da,.Baifarkaba sai gabannin sallah La'asar yayi mi'ka jin duk yagaji dan kwanciyar dayayi kan kujera,
Dasauri yakallah agogo yaga karfe hudu saura(3:36) ya lumshe ido tarw da hamma azuciyarsa yace "toh ina wannan tashiga",
Jin 'bunruntu a kitchen yatashi dasauri yana aiyana kardai tazauna tana wani abu na musamman ne,
Yana shiga yaci karo da kwalin indomie da tarin dafarfun indomie a sink,
Gaba-daya kitchen din yahautsine da zafi da tarkace,
"Subhanallah" yafurta tare dakallon Ushna data fukace kamar tayi aikin shekara yace "lafiya? Maike faruwa?"
Cikin shagwaba ta gwalalo ido kamar zatayi kuka tace "Indomie nakeso dafama tunda naji kace kanajin yunwa",
Zaro manyan idanunsa waje yayi cike da mamaki yace "Ushna Indomie awa uku?"
"Toh ni duk wacce nadafa sainaji tana 'karni, shiyasa ya'dan dau lokaci, amma katsaya yanzun wannan zatayi",
"Uhm" kawai yace yana kallon ikon Allah.Yana tsaye tabude tukunyar ta'dan 'dan'dana nandanan ta'bata rai takalleshi tana yatsina fuska tace "kash, wallahi shima yayi gishiri, zo ka 'dan'dana",
Ba musu yaje, yakar'ba ya 'dan'dana yakalleta dasauri yace "kinmasa magi kuwa?"
Ahankali ta girgiza fuska tana 'bata rai tace "a'a nalura indominma yanzun gishiri suke samata aciki, ko kawai nadafama taliya jellof ne?"
Dasauri yagirgiza kai yace "ah a'a wannanma tayi, Ni gishirin yamin haka"
Zatai musu yace "dan Allah, kibarshi hakama ni zanci"
Badan ranta yasoba tace "toh, amma gaskiya karma kacema wani nina dafa domin girkina yafi gabannan,"
"Bazan ceba" yafada yana sunkui dakai sabida tsananin dariyar dakeson kubcemai.A kwano (plate) takwasota kamar taliyar hausar data ji'ke, fuskarnan bayabo ba fallasa tami'kamai tace "gashi kaje kafaraci zanhadama juice",
Dasauri yace "dan Allah kibarshi aini nafisanma na kwali, bani 5alive indakwai",
Cike da mamaki tace "bakaso kuma kake ha'damana kullum",
"Eh sabida naga kamar ke kinaso shiyasa nakeyi", yafada adaburce yabar wajan ganin tana kokwanto.Yana zama Madina taxo dagudu tazauna tace "Abba namu fa?",
Jeki dauko cokali muci tare", kan kibta ido da bismillah ta'dauko tasa.
Ci daya tatashi dagudu ta tozar, ta'dago kai dasauri tace "Abba ba magi, kona maganine?"
"Haka nakeson ci, inbazakiciba kisa Uwani ta dafamaki wani abu kici",
Ushna na kitchen tana jinsu taji gaba daya ranta ya'kara 'baci,
Jiki asanyaye tafito ta ajiyemai juice batare datace uffanba tawuce 'daki..
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...