Wasiyar Aure 18

688 167 1
                                    

Wasiyar Aure😭❤❤

By; Najaatu Naira

FKD Fans Writers 《《 18 》》

Iwun Madina ya dakatar dashi, yatsuguna dasauri yana hakki yace "lafiya mainene, mai akaimaki?",
Bata bashi amsaba tana kuka cincin karfinta tano'ke wuya,
Ganin tana 'ka'kame jiki tayi matukar  razana,
Yasaki ajiyar zuciya yasa hannu yasharce zufar dake kan goshinsa,
Daidai kiran wayar Mama yashigo wayarsa,
Yazaro wayar daga aljihu yakallah Screen hadi dakallan Ushna dake jan zuciya kamar zata shi'da yace "kishiga ciki inazuwa zanyi magana da ,,,,,"
Kanyakai aya ta'bace awajan tare da Madina dake bin bayanta,
Cikin nutsuwa yakoma daga gefe yayi 'yar gyaran murya yana 'ko'karin saisaita muryarsa, yadauka wayar yakarata akunne yai sallama,
Bata amsaba cikin fada kamar zata ari baki tace "Kaganta tadawo gidan kobata dawo ba?"
"Eh tadawo ashe makwabta tashiga Ni bansaniba"
Dajin zancensa tasan karyane, 'ko'kari yake ya katange laifin Ushna,
Bata jaba tayi ajiyar zuciya tace "kace mata gobe inanan tafe",
Cikin ladabi dasanyin murya yace "toh Mama saida safe",
Ta yanke kirar yasaki ajiyar zuciya yari'ke kai,
Azahiri lamarin ba'karamin tsorata yayiba, ganin idonsa Ushna zata gudunmai da Yara,
Wani 'kululun ba'kinciki ya sar'kafeshi,
Ido jajir yanufi cikin gidan, tundaga waje yake kwada mata kira ba kakkautawa har dakinta,
Yasa hannu zaibude yaji tarufeshi 'kam da makulli, yayi kwafa yatafi dakinsa yadauko extra key dinsu yadawo yasa,
Da mamaki yaji tasa sakata,
Yatokari 'kofar yabigi kirji yace "'karya kike Ushna, baki'isa kigudu kokije yawan barikinki da 'Ya'yana ba, indai zakiyi iskanci kiyi kekadai karkisa zuri'ata aciki",
Zazzaga masifa yake kamar zai ari baki kan yakoma 'dakinshi yakwanta cikin 'dar da zullumin kar Ushna tagudu cikin dare,

Karfe biyu yasamu barawon barci yakwasheshi, bayan yagama tunane-tunanen nadamar auren Ushna mara adadi,.
Cancikin barci yaji 'burum din 'kofa yatashi agigice yafita,
Ushna yagani daga ita sai riga shimi 'yar fara sleeveless garment low-cut neck batakai gwuiwa ba,
Tari'ko ruwa ahannu tana jijiga Fahad daya tashi,
Bakuka yakeba yakuma 'ki barci adole sai sunzauna sunyi hira,
Tana zaune tana rikedashi tana 'korafi tace "Fid wallahi kana ganinsa, Mahaukaci madokine, yau inbaccin Allah yataimake ni wlh daya kasheni,"
Ta'kara marairaice murya tace "nidai wlh Fid kayi 'ko'kari kasamar mana VISAn Fahad akan lokaci dan Allah ko,,,,",
'Dago kan dazatayi tasaki feeder ruwan hannunta atsorace ganin Hamza tsaye yanamata kallo wani irin kallo,
Azahiri inbaccin tamai mugun sani, dasanin zalunci irin na Hamza zatace atsorace yake, saidai mugunta da 'bakar zuciyar Hamza tasan yau babu maicetonta kashinta yabushe sai waninta,
Dasauri tamike tasunkuci Fahad Tana ja dabaya tana kallonsa atsorace yana takowa gunta,
"Bani wayar" yafada cikin tsawa dahar Fahad dake hannunta yarazana,
Jiki narawa tano'ke wuya cikin i'ina tace "ah toh Ni inaruwanka dani",
Bata ankaraba taji tahade da pillars din dinning,
Yamatso dasauri yasa hannu hadi damatse hannunta, tasaki 'yar 'kara, yakar'be wayar yasa akunne,
Jin Fidyan yayi yana fadin "lafiya Mine? Maike faruwa",
Hankalin Hamza ya'kara tashi, wani 'kululun ba'kinciki ya tokaremai ama'koshi yakasa bude baki ya furta ko kalma daya,
Nandanan idanunshi suka kada sukayi jajir, cikin zafin rai yace "bakasan matar aure bace kake kiranta awannan lokacin?",
"Bansani ba," Fidyan yafada, yakashe wayar,
Ba'karamin takaicin ganinta Hamza keyi agabansa ba, jiyake kamar yasa hannu yasha'kureta yakashe, koya huta",
Yasa hannu yakarbi Fahad,
Yajanyota 'kiiiiiiii suna tafe har Parlour yadankwafar da'ita tazauna tana shashshe'ka,
Cikin tsana yakalleta yace "Ke nasan ni bazan hanaki barikinkiba kuma ban'isa insaki tsoron Allahba tunda dama chan batsoransa kikeba bare tsoran haduwa dashi,
Abunda nakeso kisani shine duk wani tunanin rashin mutunci dazakiyi bazan hanakiba, ke nifa dakike gani banzafafaba, zaki iya tafiya barikinki kibar gidannan inkinaso, kitafi bazan hanaki yin duk abunda kikesoba amma banda wayar dare agidana, sannan kuma inkina ra'ayin gudu nikaina zan'iya taimaka miki inkin gadama kihaura sama dan gudu amma Ushna karki yarda kiyi kuskuren gudu da 'Ya'Yana, bakida wannan hurumin Ushna dan duk duniyar da zaki shiga wallahi saina biki nanemoki na tozartaki,,"
Ya nuna mata yatsa yace "sannan kisani dankina kula da Fahad bashi kenufin kinzama Uwarsaba,
Nakawo masa Mairaino tundaga gidan Marayu naro'ki alfarman akawomin wacce tasan aiki,
Gobe zatazo, kidan'kashi ahannunta, hakan zaibani damar ganin 'Dana duksanda nakeso sannan kema zakisama damar tafiya yawanki duksanda kike ra'ayi batare dakin daukarmin 'Ya'yaba, kuma kisani inabinki ahankaline sabida darajar Iyayenki dana Matata, inbaccin haka dayau nahadaki da hukuma,"
Yatsagaita yana 'karemata kallo kamar bazai maganaba yace
"Wlh ki kiyayeni Ushna sannan irin wannan 'yan'iskan kayan na tallan tsaraice, kibari inkinje chan waje kisa bandanan",

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now