Wasiyar Aure😭❤️❤️
By; Najaatu Shehu Naira
Wattpad; Najaatu_NairaFKD Fans Writers 《《 27 》》
Arude yabar dakin yahau sintiri tsakiyar Parlour.
Yana kai dakomowa tafito tana cije le'be cikin tsananin azaba ta yafitoshi da hannu,
Ya'karasa gunta dagudu.
Idanunta na 'kakkafewa yatareta tana nishi sama-sama, murya narawa tace "dan Allah ka taimakamin",
"Toh-toh" yace batare da 'bata lokaciba kai tsaye yakaita asibitin VICAS,********
Baba nagaban Yayarsa Hajara suna zaune ta'inda take shiga banan take fitaba tace "aiwannan rainin arzikine, dan kaganmu talakawa shiyasa baka naiman shawararmu,
Yau Shehu dakasan zanbada gudun mawan wallahi bazaka dunga zantar da hukunci kaitsaye batare da kaji tabakina ba, amma rayuwace ai arziki kashine idan Ni bantakaba insha Allah ban cire raiba wataran zanci arzikin 'Ya'yana",
Hannu yasa akai, kansa nasarawa yana kallon yadda take babbalin bala'i yarasa ta'inda zai bullomata yace "Yaya nace maki kiyi hakuri, wallahi gaba daya kanmu yakulle Yaya, ita kanta Mahaifiyar tasu babu wanda tasanarma kuma bama mu muka zantar da hukuncinba, Wasiyar margayya Rayhana ce dan Allah kifahimce ni kiyi hakuri",
Dan mayafinta dake gefe ta dauka ta yafa akai, takalleshi tawatsar batace uffan ba zata fita yace "Yaya dan Allah kiyi hakuri kinsan duk abunda zanyi inaneman shawararki wannan karon kimin uziri",
Hannu ta'daga tayi kini-kini da fuska tace "Shehu tunda Allah yasa ka'auro wannan bushashshiyar Matar taka gaba daya kajuyama dangi baya, dama nikadai yarage baka watsarba amma yanzu nafahimci nacine dasan shiga hidimarka yasa Nima baka watsar daniba, danhaka nima nabarka da Matarka da 'Ya'yanka Shehu",
Tana maganar tana kuka Mama tashigo dauke da kwanon abinci tace "Yaya ga abinci nakawo maki kiyi hakuri",
Harara ta gallamata tace "wani sakon munafurcin kikeson isarwa Kulu? Bayan kin farra'ka tsakaninmuba kinji dadi, kuci abincinku Ni ba mayunwaciya bace, kunga tafiyata",
Baba na kwada mata kira "Yaya Yaya" bata tankashiba tai tafiyarta,.Ganin haka Mama ta'ajiye kwanon abinci zatabi bayanta Baba ya girgiza kai yace "rabu da'ita yanzun tayi fushi insha Allah zamuje hargida mubata hakuri",
Tace "Toh amma?"
"Rabu da'ita tayi fushine inta sauko komai zaiwuce",
Uhmm kawai Mama tace "tawuce dakinta cikin dacin rai.**************
Ushna nakwance bisa kan gadonta samfarin Royal, tabude idanu ahankali,
Ganin Hamza zaune agefenta taji yam kanta yadau sarawa,
Ta yunkura zata matsa taji jikinta yayi nauyi,
Take tatuna duk abunda yafaru daren jiya,
Takalleshi araunace kamar zatayi magana tayi shiru,
Chan tayamutsa fuska zata juya kai yamike dasauri cike da danasani murya 'kasa-'kasa yace "karki kauda kai Ushna, nasan nacancanci duk wani hukunci daga gareki",
Shiru tayi tana kallonsa cikin rashin fahimta ta kauda kai daga kansa, kamar bazatayi maganaba can tarintse ido tace "dukda ninaso faruwar haka amma baka cancanta cinfuska ba, kayi hakura banyi tunanin zai kasance agidanka ba",
Wani irin tausayinta yaimai bargo, yatsaya cike da mamaki yatsura mata ido,.
Zatayi magana yace "daren jiya",
"Eh kayi hakuri nasani banyi daniya ba kuma nagode da dawainiyar asibiti",tafada atakaice
Dasauri ya girgiza kai murya narawa yace "bakya cikin hayyacinki Ushna bakisan abunda yafaru ba",Wani irin siriri hawaye ya gangaro mata tace "Ni dai dan Allah karka gayama su Mama abunda yafaru, zasui bakinciki suyi tur da lamarina suga gazawarsu kan tarbiyata, wannan alfarmar kawai zakaimin dan Allah",
"Toh" kawai yace ya gyada kai yafita dasauri dan tsananin tausayi da furgicin halin datake ciki,Adaki yakifa kai da filo yayi kukan zuci ma'ishi,
Lokaci daya yatsani kansa da zatonsa akan mutane musamman ita Ushna, bakomai ke 'daga masa hankaliba saiyadda lamarin Ushna yakoma ayanzun, dadukkan alama batasan shiyai mata wannan aika-aikanba, ayanzun tabbas ya tsira toh amma maizai faru intagano gaskiyar lamari?,
Take gabanshi yafadi, lokaci daya yatsinci kansa cikin tsananin tashin hankali,
Zufa naketo mai yasa hannu bibbiyu ya cakuda gashin kansa,
Yana mai jaddada Lallai zargi aikin shedan ne,
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...