Wasiyar Aure😭❤❤
By; Najaatu Naira
FKD Fans Writer 《《20》》
Baifi munti goma da fitar Ushnaba, Fahad ya'karema Inna Saratu kallo tsab yakyakyace da ihu, yi yake kamar zai shika dan kuka tana jijjigashi,
Tundaga bayan gida Hamza yajiyo kukan ba kakkautawa yashigo bin ba'asi,
Dakin Ushna yafara nufa yaji 'kofar a gar'kame yatsaya yasa kunne yabi sautin kukan yanabi yatsinci kanshi gaban Inna Saratu,
Dasauri yami'ka hannu yakarbeshi yana fadin "ina Ushna tashiga"
"Eh tabani shi tace bazata dadeba zata dawo", Inna Saratu tafada.
Yaja guntun tsaki yakallah Madina dake biye dashi yace "kinsan inda Ushna taje",
Dasauri ta girgiza kai tana ta'be fuska tace "Abba My Mommy batananne?",
Ganin yadda tai narai-narai dafuska yace "tana 'daki tana barci, muje waje",Sunfito yana jijjiga Fahad da muryarshi takusan dashewa dan kuka ya tadda ba'ki a parlour,
Hajiya Sadiya da 'ya'yanta yagani ciki harda Kamal azaune kan kujeru., turus yaja yatsaya yayi sankwarakawai dan mamaki,
Yakallah Kamal dayafi gwanda-gwanda a yaran yace "kai taya kuka shigo babu knocking?",
Kanya bashi amsa yatuna gigicewar dayayi jin kukan Fahad yasa baisama damar rufe 'kofar gidanba dazai shigo,
Hajiya Sadiya takalleshi tana yatsine tace "Toh Hamza ko mukomane tunda bason ganina kakeba",
Kokallo bata isheshiba yana jijjiga Fahad yayi kamar baijitaba,
Tai zundai da baki tace "toh ina Matar gidan da akaima kanne kwace, kohar tafara fita yawone?",
Kallan Kamal yayi sanin yafi uwar hankali yace "kagayama Mahaifiyarka ta'iya bakinta, idan naiman magana yakawoku kutashi kutafi dama Rayhana keson ganinku cikin gidannan kuma tarasu",Kamal yajuya zaimata magana, cikin zafin rai tace "inkace min wani abu sainaci uwarka, yimin shiru saina jira dawowar ayawon naga kamarta kan nawuce",
Kamal yaja baki yayi gum, takaici yasa Hamza yaja hannun 'Yarsa da Fahad daya cikamai kunne da ihuh yafice,
Yazo fita yaci karo da Uwani zata shigo yadakatar da'ita yanuna mata ba'ki yace "karki bari 'daya daga cikinsu yabar parlour, kizauna kimin gadinsu".
Yafice, yabarta tsaye cike da mamaki, baitsaya ko'inaba sai Garden,
**********Ushna nakwance bata iya motsa gaban jikinta, Fidyan ya'dago fuskarta jiki narawa zaitambayi amincewarta yaganta sharkaf cikin hawaye,
Kai yarike dahannu bibbiyu yana girgizawa yace "ooooh God damn, Mine Pls dont do dis to me, ki amince dan Allah kizama mallakina",
Batabi takanshiba tayun'kura ahankali jiki ba'kwari tasauko,
Tana hawaye takallah madubi, gaba dayanta tsirara take batada wani sauran mayafi jikinta,
Tadur'kusa tana kukan bakin ciki tuncin karfinta tace "mainake shirin aikatawa rayuwata haka, nashiga uku",
Ganin tana kuka Fidyan yashiga damuwa yaji bazai iya daurewaba yataso jiki ba karfi yadau mayafi ya yafa mata, yakauda kai yana 'kunci yace "am sorry, kiyi hakuri namiki badaidai ba",
Dasauri tajuyo fuskarshi da tafin hannunta yana kwallah ta girgiza kai tace "a'a balaifinka bane Fid ni keda laifi, sanadiyata rayuwarmu gaba daya ta tarwatse, kayi hakuri"
"Toh amma Ushna maiyasa bazamuji dadin rayuwarmu ba, tun amakaranta kike azabtar dani gashi yanzun kiri-kiri kinhanani jikinki baccin kinsan ni bazan taba zama mallakinki ba",
Cikin rarrashi da sanyin rai tace "Fid kamanta alkawarin da mukaima Anty Rayhana?"
"Namanta, ni namance komai Ushna" yafada cikin tsawa yana wurga hannu,
Ta'dan ja dabaya afurgice jiki narawa tace "zaifa sakeni dazaran yayi aure saimuyi aure",
Hawaye na zirya akumatunsa zuciyarsa namai 'kuna yace "Karyane Mine, wallahi bazai sakeki ba, babu 'Da-namijin dazai mallakeki yarabu dake Ushna, kima daina wannan tunanin",
Kauda kai tayi gefe tana neman inda tawatsar da kayanta ganin inzata kwana dubu tanama Fidyan bayani baganewa zaiba,
Yakoma kan sofa yazauna yana kallonta tana shiri harya kammala tsab,
Zata fita tawuce yasha gabanta,
Cikin zafin rai yace "ina zaki?"
Ido jijir ta'dago kai tace "kabani hanya Fid gida zani",
Hannu yasa yahada danata yarike gam yana kallon kwayar idonta data razana yace "kimin alkawari yanda kika hanani jikinki, bazaki taba yarda kimallaka mashi kanki ba",
Lokaci daya tsananin tausayinsa yakamata, tarungumeshi ta lumshe ido tace "nama alkawari bazan taba bari wani 'Danamiji ya mallakeniba face kai Fidyan",
"Toh muje muyi shopping kan kitafi" yafada yana maida ajiyar zuciya,
Bata bashi amsaba tadauko wayarta cikin jaka taduba, karfe takwas nadare tazare manyan zara-zaran idonta tace "a'a dole inkoma gida Fid nabar Fahad da Madina, saidai muyi magana kawai innaje zankiraka yaso gobe sai muwuni tare",
Sam maganar baimai dadin jiba, amma gudun 'bacin ranta ya danne tashi maitar yayi 'yar ya'ken dole yace "inkinje kikirani i love u"
"I love u Fid" tafada
Sukai kissing din kumatun juna tafice, dasauri tashiga mota taja tawuce.

YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...