WASIYAR AURE 48

560 115 5
                                    

WASIYAR AURE😭❤️❤️

By; Najaatu Shehu Naira
Wattpad: Najaatu_Naira

FKD PRODUCTION FANS WRITERS (((48)))

*With so much memory to remember, how do you expect me to live a perfect life without you?

                      ~Najaatu Naira~*

Not edited.
Bayan kwana biyu Hamza nazaune yayi zugun ya tsunduma cikin tunani Alhj Bello yazo tabaya ya dafashi,
Firgit yajuyo yaga Mahaifinnashi tsaye kallo daya zakaimai kaga  damuwar dake dauke afuskarshi karara,
Dan gyaran murya yayi cikin nutsuwa yakira sunanshi yace "Daddy" shiru Alhji Bello yayi na'yan dakiku kan yayi ajiyar zuciya yace "Hamza nasan gaba dayanmu muna cikin damuwa barinkai daka tsinci kanka cikin tsaka maiwuya amma abunda nakeso kagane shine karage kadaici",
Azuciya Hamza yace "Daddy yanayin yanayi kamar bazai wuceba, abun ciwo yakemin yanamin ra'da'di, gaba daya rayuwata namance rabona da samun farinciki nawa nakaina" kamar yasan abunda 'Dan nashi ke aiyanawa yace "zomuje kaga gari, nasan zakaji dadi" ba musu Hamza yabisa suka  fita suka shiga manyan motocinsu Jeep ta gwamnati tare da motocin jami'an tsaro nabimasu baya,

Suna daukan hanya zuciyar Hamza tafara dukan Uku uku, hakanan yatsinci kansa cikin 'kaguwa dasan sanin inda suka dosa, kamar bazaiyi maganaba yakasa ya'dago kai yakallah Mahaifinnasa dake karanta jarida yace "Daddy ina zamu?",
Dan yatsine fuska yayi yace "gidan Alhj Shehu, kasan namasu laifi wlh inna tuna duk abunda yafarunnan nikadai sainaji kunya ta kamani, Alhj Shehu Aminin kwaraine, duk abunnan da ake ko yunkurin karekansa baiyiba, inbaccin Allah yabayyana ka,,,," chak yayi shiru tare da girgaza kai yace "kai da abu baiyi dadiba Allah shikyauta,"
"Toh hakuri zamuje mubashi ko dakwai wani abu daban"
Da mamaki Alhj Bello ya'dago kai yakalleshi yace "eh toh duk wannan abun da ake ita Mama bata gidan, ta tattara inata-inata takoma gida, toh da muke waya dashi ya gayamin nacemai bazaije biko shikadaiba, dole muje dashi nabata hakurin kama mata miji danasa akayi, nasan kuma inmunje taredakai taganka zataji dadi,"
Harya gama maganar idon Hamza nanan 'kiru akanshi, cikin sanyin murya yace "shikenan?" Rasa tacewa Alhj Bello yayi ya'daga gira yanoke wuya yace "shikenan mana, ko dakwai wani abu da kakeson sanine",
"Eh, Daddy ko anji labarin Ushna da 'Yayana baka bincika bane, dasufa tatafi", nandanan Alhj Bello ya'bata rai yace "ni banmason jin labarin yarinyarnan, saidai nasan shi Yusuf Mahaifiyar taturashi waje tunda yai yunkurin kiran lauya", nan hirar tasu tatsaya har suka isa gidan,
Da zuwansu suka tarda Mama da Alhj Shehu nazaman jiran isowarsu,
Cike da mamaki Alhj Bello yasauko yana dariya irin tasu ta manyan mutane yace "ah yahaka, keda nadauka saimunbada cigiyarki," murmushi kawai tayi tace "ni matsamin naje gun 'Dana, daidai Hamza nasaukowa ta karasa tana hamdala tana fadin "kuma lafiyanka kalau babu inda sukaima lahani?" Murmushi yayi yace "sunmin harbin yadda bazai cutar daniba, kuma inashan maganin kashe zafi tare da allura banjin zaiwani dameni",
"Mushiga ciki" Alhj Shehu yafada cike da fara'a dauke afuskarsa,
Nantake suka shiga komai nanan inda yake, gidan tsatsab, suna zaune suna hira Alhj Shehu yakallah Alhj Bello yace "ai bayan nakiraka nacema mushirya muje, toh dama bazata (surprise) naso namata Allah da ikonsa kuma kwatsam saigasu ni taimin,
Sosai Alhj Bello yabama Mama hakuri kan aikin shedanne tana fara'a tace "mugodema Allah tunda komai yawuce itakuma Hajiya Sadiya Allah shiryeta Allah kuma kiyaye gaba, takallah Hamza dake zaune yayi zugum baicikin hayyacinsa tace "Hamza yadai?" Firgit yayi yace "lafiya Mama, nace Mama ko kinkira Ushna kinji halinda take ciki kuwa?" Dasauri ta 'bata rai tace "maizanmata abunda tasa agaba shi takeyi, lokacin datatafi da Yaran na dauka zafinso ne irin na Uwa amma ganin ta'aikosu dagabaya nacirarai akan Ushna, nasan bazata taba hankali ba,"
Cikin yanayin rashin fahimta Hamza yace "Mama banganeba ta aiko da sakone?"
Ganin gaba daya hankali yadawo kanta ta takallesu tace "ranan dazanbar garinnan Mijin Ushna Fidyan yazo garinnan, nayi mamaki kwarai ganinsa da Hussaini da Hassana ahannu na tambayeshi ina Ushnan kada bakinshi yacemin ita ta'aikoshi da 'Ya'yanta yadawo dasu, nayi-nayi dashi yashigo dan insan halinda suke ciki, ya'ki,
Bayadda na'iya nakarbesu natambayeshi inda suke zaune kiri-kiri Yaronnan yasakai yawuce batare dayaban amsa koya kalleniba, toh ni banyi mamakiba saboda nasan Ushna bata nunamai darajarmu na Iyayentaba kokuma ta'iya yuhwa tazauna dashi tazagemu tas agabansa shiyasa baiganin kowa da gashi,"
Dasauri Hamza yace "a'a Mama Ushna bazatai hakaba, kiduba fa aganina da batasan rayuwa da 'Ya'yanta datun farko bazata gudu dasuba, tunda kinyi-kinyi da ita tabarsu anan amma ta'ki tatafi dasu dan kaunarsu, babu Mahaifiyar da zataki 'Ya'yanta barin Ushna da Allah yajarabceta da sonsu, Mama mudaiyi tunani ko tanacikin wani hali, ko Fidyan na cutar da 'ita dan margayya Maryam tamin gargadi akansa mugune", nandanan Mama tahau fargaba jikinta yai sanyi idanunta sukai zuru-zuru tarasa abun fada, aranta taji lalle maganar Hamza abun dubawane,
Zatai magana Alhj Shehu yakatseta cikin 'bacinrai yace "agidannan banso na'karaji anyi maganar Ushna inba hakaba zan tsine mata" dasauri Mama ta'dago kai takalleshi tarike baki ta zaro ido,
Ya gyada kai yace "kwarai kuwa, nacireta cikin 'Ya'yana, kuma banso nakarajin an ambaci sunanta" yakallah Hamza dakeji kamar yana tsalamai bulala mai ra'dadi yace "kacire maganar Ushna aranka, dama 'Ya'yane kuma tadawo mana dasu danhaka awajanmu matacciyace"
Dakyar Hamza yahadiye miyaun daya makalemai a makogoro cikin sanyin murya yace "ina yanbiyun suke Mama?"
Ita kanta mutuwar zaune tayi yanayinta ya canza idonta yai jawur da dukkan alama tana bude baki zatai kuka, jiki bakwari tatashi tafita,

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now