Wasiyar Aure😭❤❤
By; Najaatu naira
FKD Fans Writers 《《 17 》》
Tunda Hamza yafita sallah yaji bugun zuciyarsa ya'kara tsananta,
Lokaci daya yatsinci kansa cikin kewar Rayhana mara adadi,
Ana idar da sallah yakoma daga jikin bango yafara azzikar da neman tsari da shedanin dakemai kaikawo azuci.Daga nesa Abokinsa Aminu yahangoshi,
Abotarsu tasamo asaline da Aminu tunda Hamza yasamu aiki a FIRS,
Office dinsu nakallon juna,
Zuwan farko Hamza da Aminu suka hadu, yaba hankalin Aminu da Hamza yayi yasa lokaci daya suka 'kullah abota, yauda kullun irin kyautatawa dason mutane na Aminu haryaja Hamza suka saba.
Kafadarshi Aminu yasa hannu yadafa, Hamza yajuyo arazane ganin Aminu ya lumshe ido yana shafa fuskansa yasaukar da ajiyar zuciya yace "Amin yakake",
Zama Amin yayi kusa dashi ya'kuramai ido kan yace "Hamza nasan amma mutuwa, amma abunda nakeso dakai Hamza dole kazo kayi ya'ki da damuwa kasa hakuri da salama aranka tunda kanada ilimi kasan duk mairai mamacine, su basuyi gaggawaba mukuma bamuyi jinkiriba, kasa dangana aranka"
'Dago kai Hamza yayi yana girgizawa cikin damuwa yace "Amin bazaka ganebane, abubuwa sunmin yawa bangama fita daga rashin Matanaba andauko wata damuwar an dauramin, gani nake kamar ba'aimin adalciba Amin",
Cikin nutsuwa da sanyin murya Amin yace "kaidai kayi addu'ar Allahsa hakan yafizama alkhairy, kuma kasan za'bin iyaye kabi tunfarko kadace, Ni aganina ka'kara hakuri kawai wannanma zakaga Alkhairinta",
Gyada kai kawai Hamza yayi dan tunanin Ushna kawai dagamai hankali yake, yacije le'be yace "Amin kenan, muje"
Atare suka fito Amin nabashi baki sukayi Sallahma Hamza yagangaro yashige gida,.***********
Ushna na'isa Airport tayi Parking,
Fidyan yataso dasauri zai rungumeta ganin Madina da Fahad ahannunta yaja yatsaya turus,.
Ta'karaso takalleshi tana zazzare ido kamar mara gaskiya tana waige.
Cike da mamaki Fidyan yakalleta yace "lafiya Mine naganki da wa'dannan?"
Tayi ajiyar zuciya takallah Madina dake kallonsu tayi jugun tace "Eh nadaukosune Fid bazan iya barin Yarannan ahannun azzalimun Ubansu ba",
"Kamarya banganeba, sunada Ubanda yafishine" Fidyan yafada yana mata kallon tuhuma,
Dukda maganar baimata dadi ba tadaure tace "a'a saidai kasan nangaba auro wata matar zaiyi idan ba'aci sa'aba ta azabtar dasu"
Nandanan yahada rai, yayi kini-kini da fuska yace "toh ina ruwanki, kinfi Mahaifinsu sonsu ne?"
"Eh nafishi, kuma tare dasu zantafi inhakan yamaka toh inkuma baimaba saika kyalemu"
Yanda tayi maganar cikin tsawa yasa yagane kato'barar da yayi, ya rintsa ido yabude yace "ohhh Ushna kitsaya ki fahimceni",
Zatai magana Fahad yafara rigima, tahau jijjigashi tana waige kozataga wajan zama kusa,
Daga gefe taga bench taja hannun Madina taje tazauna, taduba jakar hannunta dasauri tadauko feeder tasamai madararsa abaki tana sunbatar goshinsa tana bashi baki, tana Allah-Allah yayi shiru suci gaba da magana.,
Ba'karamin takaici hakan yaba Fidyan ba, kiri-kiri Ushnarsa yar 'kwalisa tazama Uwa,
Lokaci daya jikinshi yayi la'asar, matsanancin kishi yataso mai yasama guri kusa da'ita yatsuguna kamar maineman gafara yazabga tagumi,
Kamar mainazari yamike zumbur yana kallonta, kamar bazaiyi maganaba chan yace "yanzu Mine bazaki yarda kibini batare dasu ba?"
Shiru tayi ta lumshe idonta da suka cika tam dakwallah, ahankali tagyada kai tagasgata masa,
Yasaki gawurtaccen ajiyar zuciya da ita kanta tana iya jiyoshi, yace "toh sunada Visa bare Passport?"
Kallonshi take tana wiki-wiki da ido kamar ranan tafarajin kalmar, murya nasartsewa tace "itadai Madina tanadashi amma Fahad ko birth certificate hankali baikwanta anmaiba",
Yakallah kwayar idonta dake kallon nashi yace "toh kingani ko Mine, babu damar tafiya dasu kenan, kuma kinsan Ni bazan iya barinki inuwa daya da wani 'Da namijiba, hakan kasheni yake akowani da'ki'ki"
Yanda yayi maganar gwaninban tausayi kwallah yahau sintiri fuskarta tace "Fid kasan bazantaba cin amanarka ba, kuma yabani tabbacin dazaran yayi aure zai sakeni, sannan yace idan ina ra'ayin ganinka zan'iya zuwa muhadu duk sanda raina keso kan yasama wata macen yasakeni, kumani Fidyan ko sannu bata hadani dashi, ka kwantar da hankalinka",
"Haba! dan Allah" yafada cike da mamaki,
Ta gyada kai tace "kasan shima baya kaunata kamar yanda bana kaunarsa,"
Yayi dan jim dakai dukda hakan yamai dadinji amma hankalinsa baigama kwantama lamarin yaga Ushnarsa hannun wani 'danamiji,
Tamike tsaye tana kallon yadda yake nazari tace "trust me Fidyan bazantaba yarda naci amanarkaba, kayarda dani",
Dasauri yariko tafin hannunta yahada danashi yace "yanzu zansan yadda za'ai asamarma Fahad Visa da Passport yaso daganan saimu gudu ina..............."'Kugin da wayarta keyi yadakatar dashi, yakallah screen din wayar sabuwar number ce babu suna,
Ushna takashe 'karar hadi da tsaki tace "toh yanzu saiyaushe zanganka My Fid?"
Zaibata amsa wayar tasake 'kugi, kamar bazata kallahba ta'dago wayar tana yatsina fuska,
'Buru'buru taga number Mama akan screen,
Kallon Fidyan tayi atsorace jikina kyarma tafara yarfi da hannun cikin i'ina tace "Fid Ma Mama ce",
Da ido yaimata alamar ta dauka, tagyada kai ahankali tasa yatsa tadauka,
Kamar saukar aradu taji sautin muryan Mama "kina ina Ushna",
Tasa wayar a loud speaker cikin sanyin rai tace "na'am Mama ina wuni, banajinki network bakyau" Ushna tafada tana waige,
Mama ta'kara kausasa murya tace "Bakyajina"
Jiki narawa tace "eh Mama banajinki",
Dasauri Fidyan yasa hannu yakar'be wayar yakashe, yakalleta yace "tace bakyaji kince eh bakyaji, alamar kinajinta sarai kenan"
Ta'kara firgita ta gwalalo zara-zaran idanunta tace "Fid nashiga uku ko Mama tasan zamu gudu ne"
Yasa hannu yagoge mata hawayen dakebin fuskanta cikin hanyin murya yace "yaza'ai tasani, kikwantar da hankalinki kidaina kuka karki damu, sa'annan kibari karki dau wayar harsai kinkoma gida tukun",
Jiki narawa gudu-gudu ta rungume Fahad, Madina tabiyota tashige mota, Fidyan yaturo kanshi ta window yaimata sallama, ya'kara maimaita "Mine tunda kince yace muna iya haduwa, gobe kizo gidana ina jiranki da makulli",
Ta gyada kai tanasa giya tace "sai goben i Love u",
"I love u more" yasa hannu yanamata bye-bye harta 'bace,*****
Akofar gida tatarda Hamza yana sintiri jitayi kamar tabi takanshi, kantaje tayi parking,
Madina tabude motar dagudu taje dasauri yana tsaye ta rungumeshi,
Ushna dake rike da Fahad tafito da akwatin kayan Fahad ta gungaro,
Zata wuce Hamza yabugamata tsawa ido jajir yace "daga ina kike",
Dukda firgicin da take ciki batatsaya ta saurareshiba ta'dan 'kan'kame Fahad zata wuce,
Ya fincikota kamar zaki mai gurnani yace "Ushna tambayarki nake daga inakike, ina kika kaimin 'Ya'ya, zaki gudu da Yarana bakida hankaline,",
Rasa tacewa tayi yayin datake jiran saukar yatsunsa akan kumatunta, tafashe da kuka tasa fuskarta jikin Fahad,
Ya'daga hannu zaikai mata duka Madina tafashe da iwuh mai'kara ta rungeme Ushna,...
![](https://img.wattpad.com/cover/227361078-288-k99320.jpg)
YOU ARE READING
WASIYAR AURE😭❤❤complete
RomanceAtsorace yakira sunanta tana kwance kan kafadarsa ya'dago fuskarta idonta arufe 'kib, Nandanan yadaburce yakwantar da'ita flat yafada kitchen dagudu yadebo ruwa yawatsa mata shiru babu labari. Afirgice jiki narawa yasa waya yakira Dr Usaini abokinsa...