WASIYAR AURE 54

747 127 7
                                    

WASIYAR AURE😭❤️❤️

By: Najaatu Shehu Naira
Wattpad: Najaatu_Naira

FKD PROD FANS WRITERS (((54)))

Haleems Garden Unguwan Rimi yawuce kaitsaye,
Yana isa yabiya kudin Ticket yashige cinema can baya yazauna, 
Yana zaune yagaza samun sukuni sai tsaki duk bayan da'ki'ka,
Yana cikin wannan halin kiran wayar Daddy yashigo,
Baidagaba yana kallo harwayar tagama 'kugi,
Yana yankewa ta Precious tashigo nanma tsaki yayi yasa wayar a silent mode yasata a'aljihu,
Yana zaune yana kukan zuci yaji sallama kusa dashi,
Ahankali yajuyo ganin Ushna kusa dashi ya'dan razana tare da tunxura yace "maiyakawo ki nan?"
Kanya rufe baki tadur'kusa tace "dan Allah kayi hakuri"
Cikin rashin fahimta yace "hakurin mai" ganin tayi kas da kanta yagyara zama gabanshi na mummunan faduwa yace "look Ushna kigane nifa bawai zanhanaki komawa gidan mijinki bane inshi kikeso amma ina tsoran karya sake wahal dake"
Dasauri ta'dago kai tana kwallah tace "Ni bansonshi"
'Dib yayi yakasa magana dan mamaki idanunsa nakanta cikin sanyin rai yace "bakya sonshi",
Ahankali ta gyada kai,
Take yai ajiyar zuciya, sai alokacin yalura gabadaya hankalin mutanan wajan nakansu koke-kokenta yacika ko'ina,"
Cikin rarrashi yaja hannunta yace "muje daina kukan bawanda zaimaki dole",
Yana tafe tanabin bayanshi yakaita mota,
Yabude 'kofa zata shiga ta'tsaya, idanunta nakan nashi tana kallon yadda sukayi jajir tace "kuka kayi?" Dasauri yagyada kai yace "believe me i was afraid, i'm very scared I thought u'll choose him over me, i feel sad bcos i'm neva ur option nd will neva be ko?",
Dasauri tagirgiza kai,
Manyan dara-daran idanunsa ya'daga yace "toh i've done my best Ushna haryanzun kinajin haushina ko,,,,,,,,,?",
Jinta rungumeshi chak yakasa motsi, sai da cinbaki ya'karasa maganar,
Zuciyoyinsu nabugawa atare kamar wa'inda sukai gudun fanfalaki tace "i love you Yaya, i very very much love u inasanka inamasifar sonka wlh inasonka",
Chak yaji iskar dayake shaka tatsaya, kamar gunki yatsaya sai maganarta datake ringin akunnansa yanajin butterflies nayawo saman kansa, baice kalaba harta gaji ta'dago kai takalleshi,
Kamar mai sambatu taji yana fadin, "daga gidansu Baba shehu 'bacin rai yasani nai gida, nasan Ushna zata sasanta da Mijinta shiyasa naje nakwanta kozan tashi ace komai mafarkine, toh amma wannan yanayi adaidai wannan lokacin banso yakasance a mafarki, nadau tsawon lokaci ina dakon soyayyar Yarinyarnan, ya Allah kasa kunnena gaskiya suke jiyemin azahiri,"
Ganin yana magana kamar zautacce ta girgizashi tace "Yaya lafiyanka kalau kuwa?"
Dasauri yagirgiza kai yace "A'a Ushna, pls cijeni naji ko agaskene",
Batasan sanda murmushi yakwace mata taja hancinta tace "dagaskene mana, amma Yaya dagaske kana sona?"
Ido biyu yazaro yarike kafadarta yace "tsaya inazuwa bari nabinciki lafiyata,"
Numba Dr Aliyu Haydar bugu daya yadauka, kansu gaisa yace "Dr dan Allah kaimin uziri zankiraka mugaisa dagabaya amma yanzun inaso kagayamin soyayyar da nakema Ushna zaikai nadunga mafarkin gashi ta'amince da soyayyata har tana sona?"
Murmushi yayi yace "nagayama gwanma kafito fili kagayamata irin kaunar da kakemata yafi kadunga karyar ciwo, gayamatane zaisa kasan makomarka kan kodai kadage kokuma kai hakuri, amma naji kana zancen mafarki",
Dasauri Hamza yagyada kai yace "eh mafarki nake",
Jin sautin dariyar Dr Aliyu ya'kular da Hamza yaishiru,
"haba Hamza karka bari soyayya ta zautaka Be a man" baibashi amsaba yakashe wayar itadai Ushna tana tsaye tana kallonshi tana murmushi,
"Shiga mota muje" yafada,
Baitsaya ko'inaba sai gidansu, tundaga bakin Gate yake kwadama Daddy kira, baifitoba sai Precious,
Tsananin farincikin dayake ciki yasata murmushi tace "bairiga yadawoba, nayita kira baka daukaba yanzun nasan dalili",
Fuska dauke da fara'a yamatsa gab da'ita yaimata ra'da akunne yace "Ushna tayarda, tanasona bansan yadda zance kifahimta ba amma yau Ushna ta'ki Fidyan akaina, yau ni tazaba abun namin kamar amafarki, dan Allah dagaskene?"
Batabashi amsaba taje wajan Ushna dake tsaye kunya dukta baibayeta tace "congratulations, kullun cikin kukan rashinki yake, akullun idan magana tashafeki yarintarsa 'kara fitowa fili take, inatayaki murna, nabaki amanarshi",
Take tafara hawaye tuna lalurar  Precious,
Cikin nutsuwa Precious tarike hannunta tace "karki mance kinyi alkawari bazaki gayamaiba dan haka kidaina kukannan kanya tsanmaci wani abu, my days are numbers dan Allah kikula dashi dukda yara nakine amma zanso nace suma kikula dasu",
Ganin fuskar Ushna cikin bakinciki hawaye yaki tsayawa Hamza ya'karaso dasauri yace "lafiya mainene kuma?"
Dasauri tai ya'ken dole tagoge hawayen tace "bakomai,"
"muje gidanku ina tunanin Daddy nacan"
Ahankali talumshe ido suka nufi gida,

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now